Wani tsagi na jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Nafi’u Bala Gombe ya gargaɗi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya daina amfani da sunan jam’iyyar wajen sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tsagin Nafi’u Bala ya yi Allah-wadai da abin da ya bayyana a matsayin amfani da sunan ADC wajen yin abubuwan da bai dace ba.
A cikin wata sanarwa da Nafi’u Bala ya sanya wa hannu ranar 31 ga watan Agusta, tsagin ya ce ba zai amince a riƙa amfani da sunan jam’iyyar wajen abin da ya kira “cin mutuncin Nijeriya a idon duniya” ba.
Sanarwar ta ce irin wannan mataki na iya zama cin amanar ƙasa tare da rage darajar Nijeriya.
Ta kuma ce bai kamata a riƙa sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba tare da la’akari da dokokin ƙasar ba.
“Duk ɗan ƙasa yana da haƙƙin samun kariya a ƙarƙashin doka, amma ya kamata a bi hanyoyin da kundin tsarin mulkin Nijeriya da sauran dokoki suka tanada,” in ji sanarwar.
Kwamitin Amintattu na tsagin Nafi’u Bala ya kuma soki matakin Atiku na shigar da ƙara a wata ƙasa kan Shugaban Nijeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin kishin ƙasa kuma abin kunya.
Nafi’u Bala na kalubalantar shugabancin ADC da ke ƙarƙashin Sanata David Mark, wanda tsagin Atiku Abubakar ke goyon baya.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasar ne, na shirin neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.














