ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDC:Kwankwaso Na Shan Sukar Jama’a Kan Naɗa Ɗansa A Matsayin Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan Kano

by Sulaiman
2 days ago
Kwankwaso

Naɗin Mustapha Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC ya haifar da ce-ce-ku-ce da kan mahaifinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda da dama ke ganin matakin kuskure ne na siyasa gabanin zaɓen 2027.

Mustapha Kwankwaso shi ne babban ɗan tsohon gwamnan Kano kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso.

Naɗin nasa a ranar Litinin a matsayin mataimakin Aminu Abdussalam Gwarzo ya biyo bayan murabus ɗin da ya yi a watan Janairu daga muƙaminsa na Kwamishinan Matasa da Wasanni a gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf.

ADVERTISEMENT

Masu sukar matakin sun zargi Kwankwaso da ƙoƙarin kafa siyasar gado ta iyali, suna masu cewa hakan ya saɓa wa akidar siyasar Kwankwasiyya da aka daɗe ana yabawa da tsayawa kan adalci da bai wa kowa dama.

Sun yi nuni da cewa an yi watsi da wasu manyan jiga-jigan Kwankwasiyya da suka daɗe suna hidima ga tafiyar siyasar, ciki har da Shehu Sagagi, Rufa’i Hanga, da Lamin Baffa, domin bai wa ɗansa wannan dama.

LABARAI MASU NASABA

Mutum 1,000 Daga Jam’iyyar ADC Sun Koma PDP A Jihar Katsina

Rashin Tsaro: CUPP Ta Goyi Bayan Kiran Da Aka Yi Wa Tinubu Na Jagoranci Ko Murabus

A cewarsu, matakin na iya janyo rashin jin daɗi a tsakanin magoya bayan NDC da Kwankwasiyya a matakin ƙasa, musamman a yankunan da suka kasance ginshiƙin goyon bayan tafiyar.

Haka kuma, wasu masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana haɗa gogaggen ɗan siyasa kamar Aminu Abdussalam da matashin Mustapha Kwankwaso a matsayin babban caca ta siyasa, wadda sakamakonta zai iya tasiri ga damar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Sai dai magoya bayan Kwankwaso suna ganin Mustapha yana da ƙwarewar siyasa da gogewar gwamnati da za su ba shi damar taka rawar gani a sabon muƙamin da aka ba shi.

Kwankwaso
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Manoman Citta Sun Soki Gwamnatin Delta Kan Mayar Da Su Saniyar Ware
  • Sulaiman
    Yadda Gwamnatin Kano Ta Samu Nasarar Kashi 80 A Fannin Aikin Noma
  • Sulaiman
    Jarin Waje Ya Inganta Hada-hadar Zuba Jari A Kasar Sin
  • Sulaiman
    Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

MASU ALAKA

Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin PDP Da ADC Yau
Siyasa

Mutum 1,000 Daga Jam’iyyar ADC Sun Koma PDP A Jihar Katsina

June 19, 2026
Tinubu
Siyasa

Rashin Tsaro: CUPP Ta Goyi Bayan Kiran Da Aka Yi Wa Tinubu Na Jagoranci Ko Murabus

June 18, 2026
2027: Tsohon Kakakin Majalisar Kaduna Abdulfatah Ya Zama Ɗan Takarar Gwamnan PRP
Siyasa

2027: Tsohon Kakakin Majalisar Kaduna Abdulfatah Ya Zama Ɗan Takarar Gwamnan PRP

June 18, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Shirin Sanya Haraji A Kan Man Fetur Da Kiran Waya

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Shirin Sanya Haraji A Kan Man Fetur Da Kiran Waya

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar Manoman Citta Ta Kasa Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Tallafin Da Take Ba Su

Manoman Citta Sun Soki Gwamnatin Delta Kan Mayar Da Su Saniyar Ware

June 19, 2026
Abinci

Yadda Gwamnatin Kano Ta Samu Nasarar Kashi 80 A Fannin Aikin Noma

June 19, 2026
Hakimi Zai Gurfana A Kotu Kan Zargin Aikata Fyaɗe A Faransa

Hakimi Zai Gurfana A Kotu Kan Zargin Aikata Fyaɗe A Faransa

June 19, 2026
Jarin Waje Ya Inganta Hada-hadar Zuba Jari A Kasar Sin

Jarin Waje Ya Inganta Hada-hadar Zuba Jari A Kasar Sin

June 19, 2026
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni

June 19, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Cimma Cikakkiyar Matsayar Kawo Karshen Fada A Gaza

Sin Ta Yi Kira Da A Cimma Cikakkiyar Matsayar Kawo Karshen Fada A Gaza

June 19, 2026
Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku

Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku

June 19, 2026
Sin Na Fatan Inganta Tuntuba Da Tsare-tsare Tsakaninta Da Membobin BRICS

Sin Na Fatan Inganta Tuntuba Da Tsare-tsare Tsakaninta Da Membobin BRICS

June 19, 2026
Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro

Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro

June 19, 2026
Sin Na Kira Da A Ingiza Matakan Siyasa A Kasar Libya

Sin Na Kira Da A Ingiza Matakan Siyasa A Kasar Libya

June 19, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.