ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gwamnatin Kano Ta Samu Nasarar Kashi 80 A Fannin Aikin Noma

by Abubakar Abba and Sulaiman
3 months ago
Abinci

A yayin da kakar noman 2026 ta fara kankama, Gwamnatin Jihar Kano, ta bullo da wasu sabbin samarwa fannin aikin noman jihar matakai.

Manufar ita ce, don ta ƙara ƙarfafa wa manoman jihar guiwa, musamman duba da hauhawar farashin kayan abinci da kuma tsadar kayan aikin noma.

Kazalika, gwamnatin ta kuma zuba jari a bangaren noman rani, ta hanyar samar da kayan aiki na zamani da ƙirƙiro da shirye-shiyen da za su taimaka wa manoman jihar, domin samar da gurbi mai yawa.

ADVERTISEMENT

Ya zuwa yanzu, gwamnatin ta samu nasarar kusan kashi 80 cikin ɗari, na burin da take son cimma a fannin.

Kano dai, ta dogara ne kacoka, kan aikin noma wajen ƙara bunƙasa tattalin arziƙinta, musamman domin samar da wadataccen abinci da yaƙar talauci da ƙara ƙarfafa tattalin arziƙin mazauna karkara.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Kwamishinan Ma’aiktar Aikin Noma da Kula da Albarkatun Ƙasa, Dakta Yakubu Ɗanjuma Mahmud, ya danganta wannan nasarar kan samar da kyawawan tsare-tsare a ƙarƙashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, tun bayan ɗare karagar shugabancin jihar a 2023.

A cewarsa, ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka, su ne; tattara bayanan manoman jihar, domin yin amfani da su wajen samar da tsarin inganta fannin.

Wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin ta samar a cewarsa, sun haɗa da sake farfaɗo da noman rani a ɗaukacin faɗin jihar.

“Mun maido tare da kuma gyara kadadar noma 1,230 da kuma ƙasar yin noma a jihar, tare da dawo da wajen yin noman rani da ke Kadawa,” a cewar Mahmud.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta ɗauki matakan daƙile yawan samun rikici a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya da ke jihar, musamman ta hanyar katange kimanin Buratalai masu tsawon kilo mita 1,300.

A cewarsa, yanzu haka, gwamnatin na shirin fara wani babban aiki na gina Dam a dajin Ɗantsoshiya, wanda ya kai mai kimanin, tsawon kilo mita biyu da za a iya tara ruwan da zai kai lita miliyan uku.

“Dam ɗin zai taimaka wajen samar da ruwa ga kimain kadada 1,250, idan aka kammala aikin,” in ji Kwamishinan.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin ta kuma gina ƙananan Dam 11 a yankunan Albasu, Shanono, Gari, Dawakin Kudu, Rogo, Ajingi da kuma Bichi.

Mahmud ya ce, waɗannan Dam-dam ɗin, za su iya wadata kadadar noma kimanin 1,200, waɗanda kuma ake sa ran za su karaɗe kimanin kadada 2,000.

“A yanzu haka, akwai kuma wasu sabbin kimanin kadadar noman rani 2,000 da aka tsara za a samar a wasu yankunan jihar,” in ji Mahmud.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta kuma samar da kayan aiki ga manoman jihar, inda ya ce; a shekaru uku na hawan gwamnatin, jihar ta samar da Tirelolin takin zamani sama da 623 ga manoman jihar.

Noma
Abubakar Abba
+ posts Bio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
Noma
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
Kungiyar Manoman Citta Ta Kasa Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Tallafin Da Take Ba Su

Manoman Citta Sun Soki Gwamnatin Delta Kan Mayar Da Su Saniyar Ware

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.