ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Bankaɗo Hodar Ibilis Da Aka Ɓoye A Cikin Gwangwanin Kwakwar Manja A Legas

by Yusuf Shuaibu
5 months ago
NDLEA

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun yi nasarar tarwatsa wata babbar ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi bayan wani shiri na sirri da ya ɗauki tsawon makonni uku.

A yayin wannan aiki, an daƙile jigilar hodar ibilis da aka ɓoye cikin gwangwanin man ƙwarya da ake shirin tura wa zuwa ƙasar Birtaniya, tare da kai samame wurin da ake shirya kayan, lamarin da ya kai ga gano dukkan matakan ƙungiyar har zuwa kama jagoranta.

  • Kwastam Ta Kama Miyagun Ƙwayoyi Na Naira Miliyan 99.9, Ta Miƙa Su Ga NDLEA A Sakkwato
  • NDLEA Ta Kwace Kwayoyin Pregabalin 75,000 Da Hodar Iblis 556 A Kano

Nasaran ta fara ne tun a ranar da jami’an NDLEA da ke Ikeja a Jihar Legas suka gano kilo 3.10 na hodar ibilis a sashen fitar da kaya na filin jirgin sama. An ɓoye ƙwayar cikin gwangwanin kwakwar manja da aka shirya tura wa Birtaniya.

ADVERTISEMENT

Nan take aka kama masu kula da kayan guda biyu da suka haɗa da Idris Olayiwola Amoo da Akinlami Akinsoji Adedoyin. Domin gano wanda ya aika da kayan da kuma jagoran ƙungiyar, jami’an suka gudanar da wani aiki na musamman ranar Alhamis 2 ga Afrilu wanda ya kai ga kama Ezemuwo Joel, wanda ke amfani da sunan ƙarya na Ajayi.

Kamen nasa ya kai jami’an ga jagoran ƙungiyar, King Arinze mai shekaru 52, wanda aka cafke a maboyarsa a yankin Isolo a Legas. Daga nan aka kai shi rumbun ajiyarsa da ke 11, Ola Ifa Street, Bucknor, Isolo, inda aka gano gwangwani 886 na kwakwar manja da aka shirya don ɓoye miyagun ƙwayoyi, da kayan aiki irinsu na’urar rufe gwangwani, masu buɗe gwangwani, fenti, gram 52 na cannabis satiɓa da safar hannu. Ya amsa cewa shi ne ke zubar da man daga gwangwanin domin ɓoye hodar ibilis.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A wani aiki daban a Jihar Borno, jami’an NDLEA a ranar Laraba 1 ga Afrilu sun kama wata mata mai bai wa ƙungiyoyin ƴan bindiga miyagun ƙwayoyi, Aisha Adamu mai shekaru 28, a kan titin Gamboru Ngala, ɗauke da kilo 4.3 na Colorado, wani nau’in tabar wiwi ta roba mai ƙarfi.

A gefe guda kuma, jami’an NDLEA sun kama faston cocin Celestial Church of Christ da ke Agonɓi Sea Beach, yankin Sakpo a Seme, Badagry, Fasto Afolabi Hodonu mai shekaru 45, tare da matarsa, Mrs. Success Hodonu mai shekaru 35, ranar Alhamis 2 ga Afrilu a shingen bincike na Gbaji. Binciken motarsu ƙirar Honda Pilot ya kai ga gano kilo 11 na skunk da aka ɓoye a sassan motar.

Kamen ma’auratan ya biyo bayan cafke wani da ya yi ƙaryar zama jami’in tsaro, Sunday Samuel mai shekaru 35, a wannan shingen ranar Litinin 30 ga Maris, ɗauke da kilo 24.5 na skunk daga Seme zuwa Legas.

A Jihar Adamawa, jami’an NDLEA da ke sintiri a kan titin Namtari, Yola ta kudu, ranar Litinin 30 ga Maris sun tare wata mota mai lamba RUW 947 ƊA ɗauke da ƙwayoyi 48,000 na tramadol. An kama direban, Abdulaziz Ismail Korede, yayin da bincike ya kai ga kama mai karɓar kayan, Idris Adamu.

A Jihar Osun, an kama Idiatu Oladejo mai shekaru 60 da kilo 15 na skunk a Isale Osun, Osogbo, ranar Laraba 1 ga Afrilu. A Jihar Ondo kuma, jami’an NDLEA bisa sahihan bayanan sirri sun kai samame dajin Itaogbolu, Akure, inda suka ƙwato kilo 351 na skunk da tsabarsa. Haka kuma, an kama Aminu Usman Gembu mai shekaru 66 a Aliade, Jihar Benuwai tare da kapsul 28,600 na tramadol.

A Jihar Edo, jami’an NDLEA sun kama Roland Owie mai shekaru 37 bayan samamen da suka kai rumbun ajiyarsa a Egbanke a ƙaramar hukumar Orhionmwon ranar Litinin 30 ga Maris, inda aka ƙwato kilo 1,378 na skunk.

Haka zalika, an kama wata shahararriyar dillaliyar miyagun ƙwayoyi, Ayantola Omodunmomi (Iya Elle) mai shekaru 40, a yankin Eleta na Ibadan, Jihar Oyo, ranar Laraba 1 ga Afrilu. An kama ta ne bayan bayanan sirri sun nuna yadda take amfani da ‘yarta mai shekaru 11, Anjola, wajen kai miyagun ƙwayoyi ga kwastomominta. A lokacin kamanta, an ƙwato kilo 45.6 na skunk daga rumbunta.

A ɓangaren wayar da kai, rundunonin NDLEA a faɗin ƙasar nan sun ci gaba da shirye-shiryen wayar da kai da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi (WADA) a makarantun, wuraren ibada da al’umma. Daga ciki akwai laccoci a makarantar Okere Grammar School, Saki (Oyo) da Shasha Comprehensiɓe High School, Alimosho (Legas) da Ma’ahad Ahmad Turaki Islamiyya, Sabon Gari (Kano) da Ezi-Awka Community Secondary School, Awka (Anambra) da Madrasatul Ihsan, Tsafe (Zamfara), da sauransu.

Yayin da yake yaba wa jami’an hukumar kan nasarorin da suka samu, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya jinjina wa jami’an hukumar a faɗin ƙasa kan ƙoƙarinsu na daidaita yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da rage buƙatarsu.

NDLEA
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Cheng Li-Wun

Xi Jinping Ya Gana Da Cheng Li-Wun

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.