ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 months ago
Nijeriya

Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Ƙasa, Sola Enikanolaiye, zai karbi rukunin farko na ƴan Nijeriya 268 da ake kwaso wa daga Afirka ta Kudu bayan sake barkewar hare-haren ƙiyayya ga baƙi da ke kai hari kan ƴan ƙasashen waje a ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ana sa ran waɗanda aka dawo da su za su isa Filin Jirgin Saman Murtala Muhammed da ke Legas a safiyar Alhamis, cikin jirgin kwashe jama’a na kamfanin Air Peace, wanda ake sa ran zai sauka da misalin ƙarfe 5:00 na safe.

A cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasa, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, an bayyana cewa Ambasada Enikanolaiye zai tarbi waɗanda aka kwaso a madadin Gwamnatin Tarayya, domin nuna muhimmancin da Nijeriya ke bai wa walwala da kariyar ƴan ƙasarta da ke ƙasashen waje.

ADVERTISEMENT

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa Muƙaddashin Babban Jami’in Diflomasiyyar Nijeriya a Afirka ta Kudu, Aleɗander Ajayi, zai raka fasinjojin 268 daga Pretoria zuwa Nijeriya, sannan ya miƙa su ga ministan bayan isowarsu Legas.

Sanarwar ta ce tarbar waɗanda aka dawo da su na nuna irin muhimmancin da Gwamnatin Tarayya ke bai wa jin daɗin ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, kuma hakan ya yi daidai da manufofin harkokin wajen ƙasar da suka fi mayar da hankali kan kare muradun ƴan ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Domin nuna muhimmancin da ake bai wa walwalar ƴan Nijeriya a ƙasashen waje da kuma manufar gwamnatin tarayya mai mayar da hankali kan ƴan ƙasa, Mai Girma Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Ƙasa, Ambasada Sola Enikanolaiye, zai kasance a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas domin tarbar waɗanda aka dawo da su a madadin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya,” in ji sanarwar.

Har ila yau, ma’aikatar ta sanar da tsawaita aikin tantance ƴan Nijeriya da ke son komawa gida bisa raɗin kansu, wanda Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Pretoria ke gudanarwa.

A cewar sanarwar, aikin wanda da farko ake sa ran zai ƙare tun da wuri, yanzu an tsawaita shi zuwa ranar 14 ga Yuni, 2026, domin bai wa ƙarin mutanen da rikicin ya shafa damar yin rajista domin a kwaso su gida.

“An tsawaita aikin tantance ƴan Nijeriya da ke son dawowa gida saboda hare-haren ƙiyayya ga baƙi da ake yi a Afirka ta Kudu zuwa ranar Lahadi, 14 ga Yuni, 2026, domin ba wa ƙarin mutane damar shiga cikin shirin,” in ji ma’aikatar.

Ta kuma bayyana cewa an kammala shirye-shirye na musamman domin tarbar waɗanda za su dawo, ciki har da yin rajista, tattara bayanai da samar da tallafin da zai taimaka musu wajen sake shiga cikin al’umma da kuma haɗuwa da iyalansu.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa an haɗa kai da ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati daban-daban domin tabbatar da cewa tarbar ta gudana cikin tsari tare da samar da duk wata gudunmawar da ta dace ga waɗanda tashin hankalin ya shafa.

Wannan matakin ya biyo bayan sabon barkewar hare-haren ƙiyayya ga baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu, wanda ya sa ɗaruruwan ƴan Nijeriya suka nuna sha’awar komawa gida saboda fargabar tsaro.

A baya-bayan nan, hukumomin Nijeriya sun tabbatar da cewa sama da mutum 1,000 sun nemi a dawo da su gida bisa raɗin kansu saboda damuwa kan lafiyarsu da tsaronsu.

Wannan aiki ya sake tunatar da irin shirin da aka gudanar a shekarar 2019, lokacin da aka kwaso ɗaruruwan ƴan Nijeriya daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙiyayya ga baƙi da suka janyo matsala a dangantakar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu. A lokacin ma, kamfanin Air Peace ya taka muhimmiyar rawa wajen kwaso mutanen.

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada cewa kare rayuka da muradun ƴan Nijeriya da ke ƙasashen waje na daga cikin manyan ginshiƙan manufofinta na harkokin waje, tare da alƙawarin ci gaba da tallafa wa duk wani ɗan Nijeriya da ya fuskanci matsala a wata ƙasa.

Nijeriya
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas
Nijeriya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Tinubu Ya Gana da Gwamnan Kwara Bayan Harin Ta’addanci Da Ya Yi Ajalin Sama Da Mutane 160

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Tsaurara Tsaro A NIPSS Bayan Harin ’Yan Bindiga

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.