Rundunar ƴansanda ta Jihar Bauchi ta gurfanar da wani jami’in hukumar hana sha da fataucin ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Muhammad Mustapha Makama, gaban Kotun Majistare da ke Bauchi sakamakon zargin yi wa wata yarinya mai shekara 8 fyaɗe ta hanyar da yaudararta.
Wanda ake zargin mai shekaru 45, ya bayyana a gaban kotun ne sakamakon ƙorafin da mahaifiyar yarinyar, Salamatu Musa, ta shigar ta hanyar lauyanta na kare haƙƙin ɗan adam, Barrister Alkasim Mohammed.
Lauyan ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar 5 ga Yuli, 2026, a unguwar Dorawan Dillalai da ke jihar Bauchi, inda ake zargin ma’aikacin da amfani da damar aika yarinyar siyen ruwan leda wajen kaita cikin gidansa da yi mata fyade.
Kakakin rundunar ƴiansandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da cewa ‘yansanda sun kammala duk wani bincike na farko tare da tura ma’aikacin zuwa kotu domin fuskantar shari’a kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
Shari’ar ta ja hankali daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam a jihar Bauchi, waɗanda ke ci gaba da bin diddigin shari’ar a kotu domin tabbatar da an yi wa yarinyar da iyalanta adalci yadda doka ta tanada.














