ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Ta Samar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Da Za Su Ƙarfafa Kasuwanci Da Ƙasashen Duniya – Dantsoho

by Bello Hamza and Sulaiman
3 weeks ago
NPA

Muna gina tsarin tashoshin jiragen ruwa mai inganci wanda zai iya gogayya a matakin duniya, domin ƙarfafa sauƙaƙa harkokin kasuwanci, jawo jarin kai tsaye daga ƙasashen waje (FDI), da kuma ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin Nijeriya. Muna sa ran ci gaba da haɗin gwiwa domin cimma waɗannan manufofi.

Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) tana kuma aiwatar da wani dandali na zamani da ke haɗa dukkan masu ruwa da tsaki, bayanai, mu’amaloli da shirye-shirye domin inganta tsarin dijital na hukumar. An tabbatar da ingancin wannan dandali, wato Port Community System, a farkon zangon shekarar 2026.

Muna inganta hanyoyin sarrafa kaya ta hanyar ƙaddamar da tsarin tantance e-Tag, manhajar binciken haɗin gwiwa a jiragen ruwa, tsarin aika bayanai ta lantarki da sauran fasahohi, domin rage lokacin da kaya ke ɗauka a tashoshin jiragen ruwa da kuma saurin gudanar da ayyuka. Haka kuma, tsarinmu na dijital yana ba da damar gudanar da mu’amaloli ba tare da amfani da takardu ba, wanda ke rage barnar albarkatu.

ADVERTISEMENT

Shirin zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da sauye-sauyen da ake ci gaba da yi a harkokin gudanar da tashoshin ruwa na NPA sun yi la’akari da buƙatar ci gaba da samar da yanayin kasuwanci mai kyau, wanda ya taimaka wajen samun rarar cinikayya ta ƙasa a jere cikin shekaru.

Bayan habakar da aka samu a harkar jigilar kaya ta hanyar sauya kaya daga jirgi zuwa jirgi a Tashar Ruwa ta Lekki Deep Seaport, da kuma ƙaruwa a cinikayyar kayayyaki da Ƙungiyar Tattalin Arzikin Nijeriya (NESG) ta bayar da rahoto a kai, zuwan jirgin MƁ Ocean Dragon ya ƙara nuna cewa yanayin kasuwanci a Nijeriya na ci gaba da ingantuwa.

LABARAI MASU NASABA

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

Yayin da ake sa ran yawan zirga-zirgar jiragen ruwa da kayayyaki zai ƙaru, irin waɗannan zuba jari na hangen nesa da muka taru domin murnar ƙaddamar da su a yau za su yi tasiri mai girma a nan gaba.

Ina tabbatar wa al’ummar masu zuba jari na duniya cewa Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), ƙarƙashin kulawar Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, za ta ci gaba da haɗa kan masu ruwa da tsaki domin inganta sauƙin gudanar da kasuwanci, da nufin cin moriyar ɗimbin arzikin tattalin arzikin teku da Nijeriya take da shi.

Dangane da ababen more rayuwa na tashoshin jiragen ruwa, abin da muka yi jinkirin aiwatarwa shi ne gina sabbin tashoshin jiragen ruwa na zamani. Yanzu mun fara gyara wannan gibi ta hanyar fara aiki da Lekki Deep Sea Port, wanda ke da cikakken tsarin sarrafa kansa, kuma yana da zurfin ruwa na mita 17 a ɗabi’ance. Haka kuma muna ƙara zuba jari domin gina ƙarin tashoshin jiragen ruwa masu zurfin ruwa.

Manyan tashoshin jiragen ruwanmu kamar Apapa da Tin Can sun tsufa. An gina Tashar Ruwa ta Apapa kusan shekaru 100 da suka gabata. Duk da cewa tana da wuraren sauke jiragen ruwa guda 24, yawancinsu sun tsufa. Ƙarancin faɗaɗawa da zamanantar da su ya sa yake da wahala su karbi manyan jiragen ruwa na zamani.

Tashar ruwa ta biyu mafi girma a ƙasar, wato Tin Can, an gina ta kusan shekaru 50 da suka gabata. Sai dai girman jiragen ruwa, saurin tafiyarsu da fasahar da ake amfani da ita a yau sun canza sosai, wanda ya sa ya zama ƙalubale ga wasu manyan jiragen ruwa su shigo Nijeriya.

Bugu da ƙari, waɗannan tashoshin ruwa guda biyu na cikin koguna ne, don haka ba su da zurfi sosai. A gefe guda kuma, ƙasashe maƙwabta kamar Ghana (Tema), Côte d’Iboire (Abidjan), Togo (Lomé) da Benin (Cotonou) sun yi gaggawar ɗaukar matakan bunƙasa tashoshinsu, wanda ya sa yanzu suka zarce mu a wasu fannoni.

Tashoshin jiragen ruwansu sun fi zurfi kuma sun fi samun gyare-gyare da kayan aiki na zamani. Duk da haka, gaskiyar magana ita ce Nijeriya ta fi waɗannan ƙasashe yawan jama’a kuma tattalin arzikinta ya fi ƙarfi. Sai dai ana sauke kaya a tashoshinsu ne saboda sun tsara tashoshinsu cikin hikima ta yadda suka fi namu inganci ta fuskar ababen more rayuwa, kayan aiki da fasaha.

Saboda haka, muna kallon waɗannan matsaloli a matsayin ƙalubale, amma kuma dama ce ta ci gaba da bunƙasa, wadda muka shirya tsaf domin cin moriyarta.

Wannan yana da alaƙa da shirinmu na cike gibi, wanda muka gudanar shekaru kaɗan da suka gabata bayan ƙarshen annobar Korona, domin gano muhimman wuraren da ya kamata a zuba jari a yankuna daban-daban wajen inganta ababen more rayuwa na tashoshin jiragen ruwa, fasaha da tsarin haɗin gwiwar al’ummar tashoshin ruwa.

Tun daga lokacin, muna aiki tare da cibiyoyin yankuna, bankunan raya ƙasa da kuma Bankin Duniya domin ganin yadda za a samar da tallafin zuba jari, ta yadda a ƙarshe za mu samu tashoshin jiragen ruwa masu iya gogayya a dukkan yankunan ƙasar.

Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) tana da wani tsari na musamman saboda tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati da kuma hukumomin kula da harkokin teku. Wannan ya samar da kyakkyawar daidaituwa da Ƙungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa na Ƙasa da Ƙasa, fiye da yadda ake samu a ƙasashe da dama, kuma wannan babban abu ne mai ƙarfi a gare mu.

Muna da ƙalubale da dama, amma yana da muhimmanci a fahimci tarihin Nijeriya da kuma yadda tashoshin jiragen ruwanta suka samo asali. Don haka, idan ana son yin adalci wajen tantance yadda muke aiki, dole ne a yi la’akari da wannan tarihin. Ba za a iya kwatanta Nijeriya kai tsaye da ƙasashe kamar Belgium ko Netherlands ba tare da la’akari da waɗannan bambance-bambancen ba.

Mun tsara gyaran tsarin tashoshin jiragen ruwanmu bisa shawarwarin wani kamfanin ba da shawara na ƙasa da ƙasa, kuma a babban mataki mun yi koyi da tsarin tashar ruwa ta Port of Antwerp. Aiwtar da irin wannan babban tsari yana ɗaukar lokaci mai tsawo, amma wannan ita ce hanyar da muka zaba.

Ta yaya zamanantar da tashoshin ruwa zai taimaka wa ci gaban tattalin arzikin Afirka?

Afirka na da wani yanayi na musamman saboda ita ce nahiyar da ƙasarta mafi yawan jama’a kuma mafi ƙarfin tattalin arziki ba ita ce ke da mafi girman tashar jiragen ruwa ba. Yawan al’ummar Afirka ya kai kusan biliyan 1.5, don haka damar ci gabanta tana da matuƙar girma, kuma har yanzu akwai manyan damammakin bunƙasa tattalin arziki.

Dangane da ma’adanai kuwa, har yanzu muna da ɗimbin albarkatun ƙasa a ƙarƙashin ƙasa. Amma ƙarancin fasaha, dabarun tattalin arziki, tallafi da tsari idan aka kwatanta da ƙasashe kamar China, sun hana nahiyar cin cikakken moriyar waɗannan albarkatu.

Misali, tashar ruwa ta Port of Shanghai ta sarrafa kusan TEU miliyan 41 a bara, yayin da nahiyar Afirka baki ɗaya ta sarrafa TEU miliyan 34 kacal. Saboda wannan damar ce ma China ke ƙara zuba jari a Afirka, ciki har da aikin ma’adinan ƙarfe na Simandou Iron Ore Project mai darajar Dala biliyan 16 a Guinea.

Yaya batun Nijeriya da gudummawar tashoshin ruwa ga tattalin arziki?

Za mu ɗauki dabaru masu fannoni da dama ta hanyar ƙarfafa harkokin haƙar ma’adanai da noma. Hakan zai sa tashoshin jiragen ruwanmu su bunƙasa, ba wai don karbar kayayyakin da ake shigowa da su kawai ba, har ma da fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa kasuwannin duniya.

Haka kuma, za mu ci gaba da neman haɗin gwiwa da zai kai ga kafa wani sabon tashar jiragen ruwa mai zurfin ruwa a Nijeriya, wanda zai ƙara faɗaɗa damar kasuwanci, zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

A gaskiya ma, muna da lasisi ko izinin gudanar da ayyukan tashoshin ruwa masu zurfin ruwa guda shida. Sai dai ina fatan aƙalla ɗaya daga cikinsu za a aiwatar da shi cikin nasara. Muna kuma da niyyar yin koyi da aikin Tanger Med Port na ƙasar Morocco, ta hanyar gina sabuwar tashar ruwa mai amfani da sabbin fasahohi tare da haɗin gwiwar mafi kyawun abokan hulɗa a duniya.

Da zarar an samar da waɗannan abubuwa, masu zuba jari daga ƙasashen waje za su zo da kansu saboda za su ga cewa gwamnati ma ta himmatu kuma tana goyon bayan ayyukan.

Shin gaskiya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara gina sabbin tashoshin ruwa masu zurfin ruwa?

Eh, Gwamnatin Tarayya ta kammala dukkan amincewa, takardun shaida da matakan bin ƙa’idoji domin aiwatar da wasu sabbin ayyukan tashoshin ruwa masu zurfin ruwa guda biyar. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da ake yi domin Nijeriya ta dawo da sama da kashi 70 cikin 100 na kayan da ake jigilar su zuwa Afirka amma ba sa sauka a tashoshinta.

Ayyukan tashoshin ruwan da aka amince da su sun haɗa da: Badagry Deep Sea Port a Jihar Legas

Olokola Deep Sea Port a Jihar Ondo. Ibom Deep Sea Port a Jihar Akwa Ibom. Bakassi Deep Sea Port a Jihar Cross Riber. Bonny Deep Sea Port a Jihar Ribers.

Ko da yake har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da masu zuba jari saboda yawan kuɗaɗen da ake buƙata domin irin waɗannan manyan ayyuka, gwamnati ta riga ta kafa dukkan tubalan doka da tsarin gudanarwa da ake buƙata domin fara aiwatar da su.

Ana sa ran waɗannan tashoshin ruwa za su ƙara ƙarfin Nijeriya wajen karbar manyan jiragen ruwa masu ɗaukar kaya, faɗaɗa harkokin kasuwanci da kuma ƙarfafa hanyoyin sufuri da dabarun kasuwanci a yankin.

An kuma bayyana cewa yawan jama’ar Nijeriya da ke ƙaruwa, bunƙasar tattalin arzikinta da muhimmiyar rawar da take takawa wajen hidimtawa ƙasashe marasa bakin teku kamar Niger, Chad, Mali da Burkina Faso, sun sa zuba jari a tashoshin ruwa masu zurfin ruwa ya zama wajibi.

A halin yanzu, Nijeriya na ɗaukar sama da kashi 70 cikin 100 na zirga-zirgar kayan ruwa a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka, yayin da wasu daga cikin ƙasashen da ba su da bakin teku ke dogaro da tashoshin ruwanta domin shiga kasuwannin duniya.

Gwamnati na aiwatar da dabaru na gajeren lokaci, matsakaicin lokaci da kuma dogon lokaci domin inganta ayyukan tashoshin ruwa. Waɗannan sun haɗa da gyaran tsofaffin tashoshin ruwa, amfani da sabbin fasahohin zamani da kuma gina sababbin tashoshin ruwa masu zurfin ruwa.

NPA
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba
NPA
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Sulaiman
    Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin
  • Sulaiman
    Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni
  • Sulaiman
    ‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

MASU ALAKA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN
Tattalin Arziki

Rage Farashin Mai Na Ɗangote: Dillalan Man Fetur Sun Yi Burus Da Sauya Nasu Farashin

June 27, 2026
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani
Tattalin Arziki

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

June 26, 2026
Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
Tattalin Arziki

Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya

June 20, 2026
Next Post
2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa

2027:Yadda Kuɗi Da Siyasar Uban-gida Suka Daƙile Hanƙoron Matasa

LABARAI MASU NASABA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

“Mutunta Ƴancin Addinai Ita Ce Hanyar Wanzar Da Zaman Lafiya A Kaduna”

July 10, 2026
Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

July 10, 2026
Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu

Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu

July 10, 2026
Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Kan Gyaran Kudirin Dokar Shari’ar Manyan Laifuka

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Kan Gyaran Kudirin Dokar Shari’ar Manyan Laifuka

July 10, 2026
Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf

Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf

July 10, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

July 9, 2026
Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

July 9, 2026
‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

July 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.