ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

PDP Ta Bankaɗo Shirin Tsige Gwamna Makinde Na Jihar Oyo

by Yusuf Shuaibu
5 months ago

Jam’iyyar PDP a Jihar Oyo ta nuna sabon damuwa kan wani zargin shirin siyasa da ake iƙirarin an tsara shi domin tsige Gwamna Seyi Makinde, wanda hakan na ci gaba da kawo ƙaruwar tashin hakali a cikin siyasar jihar.

A yayin wani hirar da ya yi, jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar PDP Jihar, Michael Ogunsina, ya bayyana cewa akwai ƙoƙarin da wasu shahararrun mutane ke yi da nufin dagula tsarin mulkin da ake yi a yanzu.

A cewarsa, an ce Olubadan ya gana da shugaban majalisar dokokin Jihar Oyo da buƙatar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

ADVERTISEMENT
  • Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Har ila yau, ya zargi Florence Ajimobi da ƙoƙarin gudanar da tsige gwamnan. Waɗannan zarge-zargen sun fito ne a lokacin da ake ci gaba da tashin hankali na siyasa a jihar, inda ƴan majalisa suka fara magance rahotannin wani shirin tsige gwamnan bayan wata muhimmin taro da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

Ganawar, wanda mambobin majalisar dokokin Jihar Oyo suka halarta, an shirya shi don jin ra’ayoyin ƴan majalisar da yin aiki a bayan fage don tattauna rashin jituwa tsakanin ɓagaren majalisar dokoki da na zartarwa. 

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Bayan taron, ƴan majalisa da dama sun fito fili sun bayyana matsayinsu. Yayin da wasu, ciki har da mataimakin shugaban majalisa, suka musanta kasancewarsu cikin irin wannan shiri, wasu kuma sun yi shiru, wanda hakan ya ƙara tayar da muhawara a tsakanin jama’a.

Ɗaya daga cikin amsoshin da suka fi fice ya fito ne daga babban mai tsawatarwa na majalisa, Hon. Gbenga Oyekola, wanda ya fitar da wata sanarwa mai cikakken bayani yana ware kansa daga duk wani aiki da zai iya kawo rashin zaman lafiya a jihar. Ya bayyana cewa bai san wani shirye-shiryen tsige gwamna daga muƙaminansa ba.

A cewar bayani da ya bayar, tattaunawar a taron sun haɗa da bayyana abubuwa daga shugaban majalisa, wanda aka ruwaito ya bayyana cewa wasu fitattun sarakuna da na siyasa sun tunkare shi game da makomar siyasarsa. Duk da haka, shugaban majalisar ya ƙi amincewa da irin waɗannan tayin, ciki har da zargin batun kuɗi.

Oyekola ya sake tabbatar da biyayyasa ga Gwamnan Seyi Makinde, yana mai jaddada sadaukarwarsa ga gwamnatin da kuma kiyaye haɗin kai da kwanciyar hankali a Jihar Oyo. Ya jaddada cewa ba zai kasance cikin wani mataki da zai iya raunana gwamnati ba.

A halin yanzu, tsohuwar uwargidan gwamnan Jihar Oyo, Dakta (Mrs.) Florence Ajimobi, ta musanta zarge-zargen da ke danganta ta da shi na kuɗaɗe da ake zaton za a bai wa ƴan majalisar dokokin Jihar Oyo don su tsige Gwamnan Seyi Makinde.

A wata sanarwa da ofishinta ya fitar, Ajimobi ta bayyana zarge-zargen a matsayin ba gaskiya ba ne kwata-kwata, kuma wani lamari ne na ƙage da aka yi da niyyar sanya ta a wani hali mara kyau da ruɗar da jama’a.

“Ban taɓa kiran taro ko halarta, ko shiga kowanne irin taro da wani mutum ko ƙungiya don yin magana kan tsige gwamnati ta Jihar Oyo ba,” in ji sanarwar. 

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Zaɓen 2027: ATM Gwarzo Zai Kalubalanci Sanata Barau A Mazaɓar Kano Ta Arewa

Zaɓen 2027: ATM Gwarzo Zai Kalubalanci Sanata Barau A Mazaɓar Kano Ta Arewa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.