ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaɓen 2027: ATM Gwarzo Zai Kalubalanci Sanata Barau A Mazaɓar Kano Ta Arewa

by Muhammad
3 months ago

Alamun rikicin siyasa na ƙara bayyana a Jihar Kano gabanin zaɓen 2027, yayin da rahotanni ke nuni da cewa tsohon Mataimakin Gwamnan jihar, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, na shirin kalubalantar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, a takarar Sanatan Kano ta Arewa.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan yunƙuri na iya haifar da gagarumin fafatawar siyasa a tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, musamman duba da muhimmancin Kano a siyasar ƙasa

Sanata Barau, wanda ke wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawa tun shekarar 2015, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar.

ADVERTISEMENT

A nasa ɓangaren, Gwarzo na da tasiri a siyasar Kano, musamman saboda alaƙarsa da manyan jagororin siyasa da kuma goyon bayan da yake samu a tsakanin al’umma.

Masu nazarin siyasa na ganin cewa wannan fafatawa na iya zama babbar gwagwarmaya tsakanin ɓangarorin siyasar jihar, wadda za ta iya sauya fasalin siyasar Kano kafin zaɓen 2027.

LABARAI MASU NASABA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Sun kuma jaddada cewa yadda jam’iyyun siyasa za su tsara kansu da kuma irin haɗin gwiwar da za a samu tsakanin ‘yan siyasa zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai yi nasara.

A halin yanzu, ana ci gaba da sa ido kan yadda al’amura za su gudana, yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100
  • Muhammad
    ‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
  • Muhammad
    Cikin Shekaru 28, Kudiri Ƙasa Da 10 Sanatocin Zamfara Ta Arewa Suka Gabatar A Majalisa – Shinkafi
  • Muhammad
    2027: NNPP Ta Yi Wa Korarrun Mambobinta Afuwa, Ta Yi Alƙawarin Basu Tikitin Kai-tsaye

MASU ALAKA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe
Manyan Labarai

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
Manyan Labarai

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Next Post
Wakilin Sin Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Shugaban Jamhuriyar Congo

Wakilin Sin Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Shugaban Jamhuriyar Congo

LABARAI MASU NASABA

Falalar Salatut Tasbihi

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

July 17, 2026
Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

July 17, 2026
Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

July 17, 2026
Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

July 17, 2026
Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

July 17, 2026
An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

July 17, 2026
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.