ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Cikin Gida Na Jam’iyyun Siyasa Na Yin Mummunan Tasiri Ga Sahihancin Zaben Nijeriya – INEC

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
7 months ago
INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan ya ce rikici na cikin gida na jam’iyyun siyasa na shafar ingancin zaben Nijeriya.

A yayin da yake magana a taron tuntuba tsakanin hukumar da shugabannin jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista, shugaban INEC ya ce rikice-rikicen shugabanci da ake yawan samu a cikin jam’iyyun siyasa daban-daban a fadin kasar nan yana dawo da hannun agogo baya kan harkokin zabe.

  • Manoma Da Makiyaya Sun Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Filato
  • Karfafa Tsarin Kimiyyar Fintech A Nijeriya

Ya ce shari’u da dama wanda INEC ke yawan samu suna karkatar da hankalin hukumar daga muhimman aikin tabbatar da sahihin zabe mai cike da adalci a Nijeriya. Yana kara da cewa “a matsayinmu na masu samar da tsarin zabe, mun tilasta wa kanmu magance wadannan al’amurra ba don amfanin hukumarmu kawai ba, sai dai don amfanin dimokuradiyyarmu.

ADVERTISEMENT

“Dole ne mu hada kai tare don kare gaskiya cikin harkokin zabenmu, wanda ke fuskantar kalubale daga yawaitar rikicin shugabanci a cikin jam’iyyu daban-daban a fadin kasarmu mai daraja.

“Asalin dimokuradiyya yana cikin ikon jam’iyyun siyasa su bunkasa, yin muhawara, da fafata manufofi ta hanyar da ke girmama ka’idojin na adalci da mutunta juna.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

“A ko da yaushe, ina matukar damuwa idan na kalli yadda rikice-rikice ke faruwa a tsakanin shugabannin jam’iyyumu, wanda ba kawai yana rage ma’anar manyan manufofin wadannan kungiyoyin siyasa ba, har ma yana yin tasiri a tsarin bangaren shari’armu da kuma albarkatun kasarmu.

“Wadannan shari’u masu yawa wanda hukumar ta samu kanta a ciki suna karkatar da hankalinmu daga muhimman aikinmu na asali na tabbatar da sahihin zabe mai cike da gaskiya da zai samu amicewar ‘yan Nijeriya. A matsayinmu na masu kula da tsarin zabe, mun tilasta wa kanmu fuskanci wadannan matsaloli ba wai don amfanin hukumar kawai ba, don ci gaban dimokuradiyyarmu.

“Tasirin wadannan rikice-rikice yana da fadi sosai. Suna haifar da yanayi na rashin tabbas ga ‘yan jam’iyya da masu goyon bayansu, suna rage amincewar jama’a ga tsarin siyasa, kuma suna raunana tsarin dimokuradiyya da muke raino. Kowace kara ba wai kawai tana cin lokaci da dukiya ba, har ma tana karkatar da hankalinmu daga muhimmin aikinmu da hankalin masu jefa kuri’a da kuma muhimman batutuwan kasa.”

“A matsayin hukuma mai zaman kanta, INEC ta kasancewa mara son zuciya, amma muna so mu tunatar da dukkan jam’iyyun siyasa cewa jagoranci mai hadin kai da gaskiya yana da muhimmanci ga lafiyar dimokuradiyyarmu. Muna kira ga shugabannin jam’iyya da su bai wa tattaunawa mai amfani fifiko fiye da rigingimu masu raba kawuna, su karfafa hadin kai a cikin jam’iyyunsu, kuma su mayar da hankali kan kirkirar manufofin da za su bunkasa kasa da al’umma maimakon rikicin cikin gida.”

A yayin da yake magana kan rajistar sabbin jam’iyyun siyasa, shugaban INEC ya sanar da rajistar sabbin jam’iyyun siyasa biyu don kawo yawan jam’iyyun a kasar zuwa 21.

Ya tabbatar da cewa hukumar tana nan daram a kan kokarinta na gudanar da harkokin zaben kasa, wanda za ta fara da zaben kananan hukumomin Abuja a ranar 21 ga Fabrairu, 2026, har zuwa zaben gwamnonin na jihohin Ekiti da Osun.

Ya ce, “INEC a karkashin shugabancina zan ci gaba da aiki bisa ga tanadin tsarin dokar zabe da suka hada da kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya da dokar zabe da ka’idodi da tsare-tsarenmu da kuma umarnin shari’a daga kotuna.

“Yayin da muke kara fuskantar karatowar zaben 2027, yana da matukar muhimmanci mu kasance masu lura da kuma daukar mataki tun kafin lokaci. Dole ne mu shirya don gabatar da tsarin zabe mai inganci wanda ya kunshi ka’idodin dimokuradiyya, adalci, da hadin kai.”

Shugaban cibiyar hadakar jam’iyyu (IPAC), Dakta Yusuf Dantalle, ya ce nauyin da ke gabanmu yana da girma sosai. Abin da ‘yan Nijeriya ke tsammani na samun kasa mai dimbin arziki, karfi, da ci gaba a tsarin dimokuradiyya yana da matukar girma. A matsayinta ta mai kula da zabe, INEC na da babban nauyi na kundin tsarin mulki ya dora mata.

Shugaban IPAC ya ce dole hukumar zabe ta kasance mai ‘yanci, mai adalci, gaskiya, karfi, da tsayuwa wajen gudanar da sahihin zabe wanda ya kasance mai cike da adalci, kuma dole ne koyaushe ta samar da yanayi mai kyau ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara, tare da lura cewa sahihancinta tana gwada shi duk lokacin da ‘yan kasa suka je zabe.

Ya ce IPAC na sane da rikice-rikicen shugabanci a wasu jam’iyyun siyasa kuma ya bukaci INEC ta bi ka’idojin jam’iyyun wajen magance irin wadannan al’amura, musamman dangane da shugabancin da ta shiga tsakani kuma ta wallafa a shafinta na internet.

INEC
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
INEC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Sin Ta Nuna Karfinta Na Sarrafa Bayanai Bisa Amfani Da Fasahar AI A Sararin Samaniya

Sin Ta Nuna Karfinta Na Sarrafa Bayanai Bisa Amfani Da Fasahar AI A Sararin Samaniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.