ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rukunin Farko Na Alhazan Nijeriya Za Su Fara Tashi Ranar 3 Ga Watan Mayu

by Yusuf Shuaibu
4 months ago
Alhazan

Jirgin farko na aikin jajji na 2026 daga Nijeriya zai tashi daga filin jirgin saman Gateway na Abeokuta, Babban Birnin Jihar Ogun, a ranar 3 ga Mayu, 2026, a jirgin FlyNas

An dai bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labarai ta hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya (NAHCON), Fatima Sanda Usara, ta fitar a jiya.

Wannan yana nuni da cewa a karon farko alhazan Jihar Ogun za su tashi daga babban birnin jihar bayan gyara filin jirgin sama.

ADVERTISEMENT

Sauran jiragen sama da za su tashi a ranar guda su ne Umza da Mad Air daga Abuja, tare da fasinjojin Jihar Kogi da Nasarawa, bi da bi, Air Peace daga Legas tare da fasinjojin Jihar Oyo, da wani jirgin FlyNas daga Birnin Kebbi.

Saboda haka, hukumar NAHCON, ciki har da mambobin wucin gadi na tawagar likitoci ta kasa, sun tashi jiya don shirya tarbar alhazan Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

NAHCON ta shawarci jirgin sama da za su yi jigilar alhazan cewa kowanne jigila zai gudana ne sau daya a yankin daya a lokaci daya. Da zarar an kammala jigilar jirgin daga yanki daya kuma za a koma na gaba, ba zai koma wannan yanki ba. Duk maniyyacin ya rasa jirgin da aka tsara a wannan yanki dole ya dauki sakamakon matsawa zuwa na gaba da ake da shi. Sauran matsaloli sun hada da jira har sai an sake hada su don tafiya.

“Na biyu, ku sani cewa alhazai dole ne su yi tafiya cikin kungiyarsu ta mutum 45, wadanda an riga an shirya katunan Nusuk dinsu lokacin da suka isa Saudiyya. Saboda haka, ana ba kowane mai yin aikin hajji shawarar ya tabbatar da sanin mambobin kungiyarsu kafin tafiyar.

“Haka kuma, ana shawartar masu aikin hajji su samo bayanan tuntubar shugabannin kungiyoyinsu da jami’in jiha ko jami’an jiha da za su raka taimaka musu wajen tafiya.”

Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya tabbatar wa alhazan ‘yan Nijeriya cewa hukumar ta gudanar da dukkan shirye-shirye da suka dace don tabbatar da aikin hajji na 2026 ya gudana cikin sauki kuma cikin nasara.

Alhazan
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Manufar Sin Ta Soke Harajin Kwastam Ga Kasashen Afirka Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Bangarorin Biyu

Manufar Sin Ta Soke Harajin Kwastam Ga Kasashen Afirka Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Bangarorin Biyu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.