ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sallar Bana: Yadda Tsadar Ragunan Layya Ke Neman Dusashe Armashinta

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago

A yayin da Babbar Sallah ke ƙara gabatowa, musulmi a faɗin duniya ke cike da murna da farin ciki domin ganin sun gudanar da wannan ibada mai muhimmaci, a gefe ɗaya kuma farashin raguna sun yi tashin gwaron zabi a faɗin Nijeriya, inda al’umma ke ci gaba kokawa, lamarin ya gagari talakawa da sauran marasa ƙarfi.

LEADERSHIP Hausa, ta yi tattaki zuwa kasuwanni wasu jihohi domin gane wa idanunsa yadda ake gudanar da hada-hadar cinikin raguna shanu da kuma raƙuma.

A binciken da wakilin na Jihar Kaduna ya gudanar, ya bayyana cewa; akwai tsadar rayuwa da talakawa ke ci gaba da fuskanta, waɗanda su ma a shekarun baya, su kan yi layyar wanda a yanzu wasu daga cikin lamarin ya gagari Kundila.

ADVERTISEMENT

A kasuwar Zango dake Tudun Wada Kaduna, wani mai sayar da raguna, Malam Umar Abubakar, ya alaƙanta tashin farashin ragunan da tsadar man fetur, inda ya ce, “Akasarin rugunan,  muna shigo da su ne, daga wasu ƙasashen da ke maƙwabta ta Nijeriya, kamar su Jamhiriyar Nijar, Kamaru Chadi, inda batun tsadar Fetur, da ake fama da ita a ɗaukacin faɗin duniya, saboda yaƙin da ake ci gaba da yi a tsakanin ƙasashen Amurka, Iran da kuma Isra’ila, a yanzu, ya shafi batun sufuri, kuma a gefe ɗaya dole ne mu ma mu ƙara kuɗin domin fitar da ribarmu, da kuma uwar kuɗin,”.

Ya ƙara da cewa, akwai kuma batun faɗuwar darajar Naira wanda hakan ya ƙara janyo tashin farashin Ragunan.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Shi ma wani Ɗanasabin Takwarar mai safarar Raguna daga ƙauyka zuwa kasuwar domin sayarwa, ya alaƙanta tashin farashin, kan ƙalubalen rashin tsaro, inda ya ce, “Muna sadaukar da rayukanmu ne, zuwa ƙauyaka, domin sayo ragunan mu kuma yi jigilarsu, ga kuma tsadar farashin kuɗin motar haya, na jigilarsu,”.

A kasuwar ta Zango, an dai kawo raguna da dama, amma  farashin ya fara daga Naira 150,000, Naira 200,000, Naira 800,000 har da Naira miliyan ɗaya.

A ɓangaren masu saye domin yin Layya kuwa, wani Malam Haruna ya ce, “A bara na yi Layya amma a bana, batun abincin da zan ciyar da iyalaina kawai nake yi domin ban da kuɗin da zan iya saye”.

Shi kuwa Malam Lawal Mai Fetur cewa, “A yanayin da ragunan Layya a 2026, sun yi matuƙar tsada, saɓanin yadda ake sayarwa, a baya, domin farashin a bana, sun ninka matuƙa kan farshin baya,”.

Sani Lawal kuwa cewa ya yi, “Na kan yi Layya a duk shekara amma a bana, abin ya fi ƙarfina, saboda ragunan sun yi tsada, saboda haka zai kawai yi ginsami ne.”

Abuja

A Abuja kuwa, tare da ragowar kusan mako guda kafin bikin Eid-el-Kabir na bana, farashin raguna ya ƙaru sosai a wurare daban-daban a cikin Babban Birnin Tarayya (FCT).

Wannan ya biyo bayan ƙorafin ƴan kasuwar raguna kan ƙarancin masu saye, duk da cewa su ma suna fuskantar matsin tattalin arziki a ƙasar.

Binciken da jaridar Abuja Metro ta gudanar ya nuna cewa farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi fiye da na shekarar da ta gabata, lamarin da ya sa da yawa daga cikin Musulmi ke nuna damuwa kan rashin iya sayen dabbar hadaya a wannan shekara.

A kasuwar shanu da ke kan hanyar Abaji zuwa Lokoja, ƙaramin rago da a bara ake sayarwa tsakanin Naira 130,000 zuwa Naira 150,000 yanzu yana tsakanin Naira 185,000 zuwa Naira 200,000.

Matsakaicin Ragon da a bara yake tsakanin Naira 220,000 zuwa Naira 250,000 yanzu yana tsakanin Naira 280,000 zuwa Naira 320,000, yayin da manyan raguna da a bara ake sayarwa tsakanin Naira 350,000 zuwa Naira 420,000 yanzu sun kai Naira 460,000 zuwa Naira 600,000. Mafi manyan raguna kuwa da a baya suke tsakanin Naira 630,000 zuwa Naira 700,000 yanzu sun kai Naira 950,000 zuwa Naira 1.2 miliyan.

A kasuwar Kwaita, wasu masu saye sun bayyana cewa suna fi sayen kai tsaye daga makiyaya saboda suna da sauƙin farashi fiye da ƴan kasuwa da ke kawo dabbobi daga arewa.

Wani mai saye, Ibrahim Suleiman, ya ce makiyaya kan sayar da raguna da rahusa saboda suna zuwa kai tsaye daga wurin kiwonsu, saɓanin ƴan kasuwa da ke ƙara farashi saboda kuɗin sufuri.

Haka kuma, bincike ya nuna cewa farashin raguna ya ƙaru a kasuwannin ƙauyuka daban-daban a yankin FCT. A wasu wurare, ragon matsakaici da a bara yake Naira 130,000 zuwa Naira 140,000 yanzu yana Naira 185,000 zuwa Naira 220,000, yayin da manya suka kai Naira 300,000 zuwa Naira 430,000.

A kasuwar Anagada da ke kan hanyar Giri-Zuba a Gwagwalada, ragon matsakaici da a bara yake Naira 165,000 zuwa Naira 180,000 yanzu yana Naira 260,000 zuwa Naira 285,000, yayin da manya suka kai Naira 470,000 zuwa Naira 650,000.

A kasuwar Zuba kuwa, farashi ya ƙaru sosai inda ragon matsakaici ya kai Naira 200,000 zuwa Naira 250,000, yayin da manya suka kai Naira 320,000 zuwa Naira 400,000.

A Kuje ma, ragon matsakaici da a bara yake Naira 200,000 zuwa Naira 230,000 yanzu yana Naira 300,000 zuwa Naira 420,000.

A gefe guda, ƴan kasuwar raguna sun koka kan ƙarancin masu saye duk da zuwan bukukuwan Eid-el-Kabir.

Wasu daga cikin ƴan kasuwar sun danganta tashin farashin da matsalar tsaro a Arewa da kuma tsadar sufuri zuwa Abuja.

Wani mai sayarwa, Garba Isyaku, ya ce ya sayo raguna 120 ne kawai daga Jihar Jigawa, kuma ya kashe kusan Naira 3,500 wajen jigilar kowane rago zuwa Abuja.

Shi ma Dahiru Alhassan ya ce rashin tsaro da tsadar sufuri sun rage yawan ragunan da ya kawo kasuwa.

A cewarsa, a bara ya kawo kusan raguna 250 ya sayar gaba ɗaya, amma a bana bai samu sayar da ko ɗaya ba.

Wasu ma’aikata da ma’aikatan gwamnati sun ce hauhawar farashin ya sa ba za su iya sayen rago ba a bana, inda wasu ke shirin neman rancen haɗin gwiwa ko kuma su koma wata hanya.

Wani ma’aikacin gwamnati, Zakari Yakubu, ya ce zai iya canza shawara saboda rashin kuɗi, yayin da wani malami, Labaran Danjuma, ya ce bashin banki da yake bi ya hana shi iya sayen rago a bana.

Kano

Malam Haruna Idris da ke Unguwar Gama A Birged, ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa, “Duk yadda ake tunanin lamarin ya wuce haka, inda ya ce “Sun je kasuwar Danbatta domin sayowa su sayar suka samu ƙaramin ragon da a bara da aka sayar da shi Naira 150,000, a yanzu kuɗinsa ya kai Naira 250,000 zuwa Naira 300,000. Sannan matsakaicin rago wanda aka sayar da shi Naira 300,000 a bara shi ne a yanzu ake sayar da shi Naira 400,000. Babban kuwa a yanzu ya kai Naira 650,000 zuwa Naira 700,000.”

Sai kuma ɓangaren shanu inda ya ce ƙaramin Sa ana iya samun sa a Naira 400,000 zuwa Naira 500,000, har ma 700,000 yana kai wa, wanda a bara duk kuɗinsa bai kai haka ba, za ka yi mamaki na gaya maka darajar Sa kamar ɗaya ce da darajar rago, saboda ka san shi rago a fannin layya ya fi sa daraja. Matsakaici Sa kuma ana samunsa a Naira 1,000,000 ɗaya zuwa miliyan ɗaya da rabi, idan kuma ƙasaitacce Sa ne ana sayar da shi Naira miliyan biyu zuwa miliyan biyu da rabi.”

Malam Haruna ya danganta wannan tsadar da tashin farashin man fetur, inda ya ce kuɗin dakon kayan da ka saya na daga cikin abin da yake laƙume kuɗaɗe, sannan shi kansa abincin da za ka ba wa dabbobin yayin da kake kiwon su yanzu kuɗinsu ya tashi sosai.

“Haka idan ka koma ɓangaren raƙuma su dama waɗannan idan ba jajiratattun mutane ko masu yin watanda baa bin ba a cewa komai. Wato Sallar bana dai sai dai a yi wa Allah godiya abin ya wuce tunanin mutum.”

Halin da aka jefa al’umma a ciki na matsin rayuwa, bincike ya nuna cewa, kashi 70 cikin ɗari na talakawa ba su da halin yin layya, kuma idan aka ajiye batun layya hatta Watanda da ake ganin itace mafi sauƙin abin da mutum zai yi domin a samar wa yara nama, to yanzu ita kanta kuɗinta yana farawa ne daga kan Naira dubu 50 zuwa dubu 100, hakan ma kaso mafi rinjaye na masu yin watanda ba su halin yi a wannan shekara.

A gefe guda kuma, wasu gidajen talakawan ma hatta abincin Sallah sai an yi da gaske ake yi, idan ma an yi za ka samu ko dai a yi abincin babu nama ko kuma ka samu ba irin abincin da aka saba yi da Sallah ba ne. 

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Ƙungiyar NUJ Ta Karrama Shugaba Da Babban Editan Kamfanin LEADERSHIP A Abuja

Ƙungiyar NUJ Ta Karrama Shugaba Da Babban Editan Kamfanin LEADERSHIP A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.