ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sama Da Mutane 100 Sun Mutu A Harin Sama Da Aka Kai Kasuwar Zamfara

by Sulaiman
4 months ago
Zamfara

Wani harin sama da sojoji suka kai kan kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 117 tare da jikkata wasu da dama. Mazauna yankin sun ce waɗanda suka mutu sun haɗa da ‘yan bindiga da mutanen yankin. In ji rahoton Daily Trust

An kai harin ne a ranar Lahadi, ranar da rundunar kuma ta kai makamancin wannan harin a Guradnayi, kusa da Kusasu a ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane mazauna yankin su 13.

Rahotannin harin da aka kai Tumfa sun bayyana ne a ƙarshen ranar Litinin saboda matsalar sadarwa a yankin.

ADVERTISEMENT

An ce Tumfa da wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da ita a ƙaramar hukumar Zurmi na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga, inda mazauna yankin ke rayuwa tare da su saboda su ne suke da iko da yankin kamar hukumomin gwamnati.

Wani jagoran al’umma, Garba Ibrahim Mashema, ya ce har yanzu yana da wahala a tantance ainihin yawan waɗanda suka mutu a harin saman da aka kai kasuwar ranar Lahadi.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

“A yanzu yana da wahala a tantance cikakken adadin waɗanda suka mutu. Kowa — mazauna gari da ‘yan bindiga — na zuwa kasuwar. Jama’a na rayuwa ne ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga, babu abin da za su iya yi,” in ji shi yayin tattaunawa da AFP.

Aliyu Musa, wani mazaunin garin Zurmi da ke kimanin kilomita bakwai daga Tumfa, ya ce da dama daga cikin waɗanda suka mutu ‘yan kasuwa ne da masu sayar da abinci, ciki har da ‘yan mata masu sayar da kunu da awara. Ya kiyasta yawan mace-macen zuwa 117.

“Gaskiya ne, kasuwar Tumfa na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga. Ita ce sansaninsu. Duk wanda ya je can ya san ya shiga yankinsu,” in ji Musa.

Wani ɗan uwan wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce jirgin yaƙin sojoji ya fara shawagi a saman kasuwar domin bincike kafin ya dawo bayan wasu sa’o’i ya kai harin bam.

Ya kuma ce wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar kamar Fakai, Mayasa da Mashema na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga saboda babu wata hukuma ta gwamnati a yankunan.

“Babu wata hukuma ta doka a ƙauyuka kamar Fakai, Mayasa da Mashema. ‘Yan bindiga ne suka zama alkalai da ‘yansanda,” in ji shi.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

MASU ALAKA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
Next Post
Ɗaliban Jami’ar Nasarawa da Aka Sace Sun Shaƙi Iskar ‘Yanci

Ɗaliban Jami’ar Nasarawa da Aka Sace Sun Shaƙi Iskar ‘Yanci

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Zamfara

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Zamfara

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.