ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sanata Buba Ya Janye Daga Takarar Fidda Gwani Ta Gwamnan APC A Bauchi, Ya Zargi Cewa ‘Ɗauki Ɗaura Ake Yi Ba Zaɓe Ba”

by Sulaiman and Khalid Idris Doya
4 months ago
Buba

Sanata Shehu Buba Umar, mai wakiltar mazaɓar Sanatan Bauchi ta Kudu kuma mai neman zama ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya sanar da janyewarsa daga zaɓen fidda gwani na gwamna da aka shirya gudanarwa ranar 21 ga Mayu, 2026, inda ya zargi cewa ana tafka maguɗi da take kundin tsarin mulkin jam’iyyar, dokar zaɓe, da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyyar cikin gida.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da mai ba shi shawara na musamman kan harƙoƙin yaɗa labarai da sadarwa, Kwamared Sabo Muhammad, da ya fitar wa labarai a Bauchi ranar Laraba.

A cewar sanarwar, matakin da Sanata Buba ya ɗauka ya biyo bayan rashin adalci wajen zaɓukan shugabannin jam’iyyar a matakin jiha musamman kan kujerar sakataren jam’iyyar a matakin jihar da kuma sakataren tsare-tsare.Sabo ya bayyana cewa zaɓukan shugabannin jam’iyyar sun kasance cikin ruɗani da kauce wa ƙa’idoji wanda hakan ya sanya jam’iyyar ta ke tafiya a bai-bai.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da masu ruwa da tsaki suka yi domin sasanta matsalolin cikin lumana, ba a samu wata nasara ba, lamarin da ya haifar da rashin kyakkyawar tsari a cikin jam’iyyar matakin jihar.

Har ila yau, sanarwar ta tuna da umarnin da aka danganta ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya buƙaci shugabannin jam’iyya su tabbatar da adalci tare da bai wa dukkan ‘yan takara dama yayin zaɓen fidda gwani, tare da gargaɗi kan duk wani abu da zai iya raunana haɗin kan jam’iyya da tsarin dimokuraɗiyya.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Sai dai Sanata Buba ya yi zargin cewa yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na APC a matakai daban-daban a Jihar Bauchi bai nuna waɗannan ƙa’idoji ba.

Ya ce tsarin ya kasance cike da kura-kurai, rashin gaskiya da kuma rashin ingantattun hanyoyin gudanar da zaɓe.Ya kuma yi zargin cewa ba a ga jami’an zaɓe a wuraren da aka ware domin gudanar da zaɓukan ba, yayin da aka ce an riga an shirya sakamakon kuma aka sanar da su ba tare da gudanar da ingantaccen zaɓe ba.

A cewarsa, wannan lamari ya janyo babban rashin yarda da sahihancin dukkan tsarin zaɓen na fidda ‘yan takara. Inda ya yi zargin cewa wasu tsiraru ke ɗauki-ɗaura maimakon a bar jama’a su zaɓi waɗanda suka dace.

Sanatan ya kuma tayar da tambayoyi dangane da shirye-shiryen gudanar da zaɓen fidda gwani, ciki har da su waye jami’an zaɓen, ina cibiyoyin kaɗa ƙuri’a da tattara sakamako suke, da yadda aka rarraba kayan zaɓe, tambayoyin da ya ce har lokacin da ya janye daga takarar ba a ba su amsa ba.

Bayan tattaunawa mai zurfi da magoya bayansa, abokan siyasa, ‘yan uwa da masu ruwa da tsaki, Sanata Buba ya bayyana cewa bai da wani zaɓi face janyewa daga zaɓen fidda gwani na gwamna a matsayin nuna rashin amincewa da matakan da suke a cikin jam’iyyar.

Ya bayyana matakin a matsayin abin da ya shafi ƙa’ida da akida, yana mai jaddada cewa dole ne tsarin dimokuraɗiyya ya kasance ƙarƙashin doka, adalci da gaskiya, ba wai ƙarƙashin tasirin wasu tsirarun mutane ba.

Sanata Buba ya buƙaci magoya bayansa da masu yi masa fatan alheri su kasance cikin kwanciyar hankali da jajircewa, yana mai nuna ƙwarin gwiwa cewa adalci zai yi nasara a ƙarshe, tare da miƙa al’amarin ga ikon Allah.

Buba
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Buba
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Buba
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Fubara Ya Janye Daga Zaɓen Fidda Gwani Na Gwamnan Ribas A APC

Fubara Ya Janye Daga Zaɓen Fidda Gwani Na Gwamnan Ribas A APC

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.