ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Naɗa Yari A Matsayin Darakta-Janar Na Yaƙin Neman Zaɓen 2027

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa sabon Kwamitin Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC gabanin zaɓen shekarar 2027, inda ya naɗa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin. Haka zalika, an naɗa Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin Sakataren kwamitin yaƙin neman zaben.

Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta nuna cewa Shugaba Tinubu ne zai kasance shugaban kwamitin (Chairman), yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda za su kasance mataimakan shugaban kwamitin. Shugaba Tinubu zai yi aiki kafa-da-kafa da wani rukunin masu ba da shawara da suka haɗa da Cif Bisi Akande, Cif Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha, Sanata Abdullahi Adamu, da kuma Sanata Florence Ita Giwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa an zabi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abass, da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, a matsayin Mataimakan Darakta-Janar domin gudanar da yaƙin neman zaɓen a shiyyoyin Kudu da kuma Arewa. Sanata Adams Oshiomhole zai yi aiki a matsayin mataimakin darakta-janar mai kula da tattaro kan jama’a (mobilisation), yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa (Chief of Staff) zai zama mataimakin darakta-janar mai kula da harkokin gudanarwa.

ADVERTISEMENT

Haka kuma an sake naɗa James Abiodun Faleke a matsayin mataimakin darakta-janar mai kula da tsare-tsare, sa-ido, da bin kadin zabe, inda zai yi aiki tare da daraktocin shiyyoyi na faɗin ƙasar nan.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris Malagi, shi ne aka dora wa alhakin zama daraktan tsare-tsare da yaɗa labarai.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya umarci ɗaukacin mambobin kwamitin da su tashi tsaye haikan domin ganin jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaɓen na watan Janairun 2027, inda ya buƙaci shugabannin ɓangarorin daban-daban da su jawo sauran mambobin jam’iyyar da ba a sanya sunayensu a cikin jerin sunayen kwamitin ba don su bada tasu gudunmawar.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post

Gwamnatin Katsina Za Ta Riƙa Biyan Malaman Addini 7,525 Duk Wata

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.