A ranar Asabar ta makon jiya ne ƙungiyar Sayarwa Market Place ta shiya wa matasa masu gudanar da harkokin kasuwaninsu ta kafafen sadarwa na zamani (Shoshiyal Mediya) taron ƙara wa juna ilimi. Editanmu Bello Hamza ya tattauna da Dakta Muhammad Ubale Kiru (Manajan Sadarwa na Kamfanin SINNTS) wanda yana ɗaya daga cikin masanan da suka gabatar da bayanai a yayin taron, inda ya yi ƙarin haske a kan wata sabwar manhaja da za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin al’ummar mu. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Wani bayani zaka yi mana a kan manhajar SINNTS?
Manhajar ta samu asali ne sakamakon giɓin da aka samu kuma muke kallo a sauran kafofin soshial mediya msamman yadda suka karkata ga sauran al’ummar wasu ɓangare na duniya sai muka ga ya dace mu ƙirƙiro wani abun da ta dace da yanayi da al’adunmu a matsayinmu na ƴan Afirka, wanda zai tafi a kan irin tsarin rayuwarmu ya kuma tafi a kan yadda muke so muga ya yi maganin abin da suka fi damun mu a matsayin mu na baƙaƙen fata kamar talauci, kuma sauran mahajojin da ake dasu ba a waklitarmu ƴan Afrika. A kan haka muka ƙirƙiro da SINNT domin ta aƙalla ta yi mana maganin wasu daga cikin waɗannan matsalolin.
A kan haka ita SINNTS ta samar da cewa, mutum miliyan 1 na farko da suka fara hawa (suka yi rajista) za su zama masu hannu jari a kamfanin kai tsaye, duka abin da kamfani yake samu da su za a raba a ƙarshen shekara, ba irin yadda muka saba gani na a yanzu kamfanonin su kaɗai ke amfana da duk abin da akasa mu daga abin da aka samu a mahajonjin da ake ake amfani da su. Haka kuma ta hanyar amfani da manhajar mutum zai kai ga samun ribar miliyan ɗaya ba tare da ya ankara ba. Wanda hakan zai canza rayuwar matasan mu.
Ta yaya matasa za su mayar da kafafen sadarwa na Soshiyal Mediya wurin samun arziƙi ba nishaɗi kaɗai ba?
A wannan yankin ne kawai matasa suka mayar da kafafen sadarwa wuri ne kawai na kallo da nishaɗi amma a wasu sassan yana zama wuri ne na bunƙasa tattalin arziƙi. Misali a shekarar da ta gabata an ƙiyarsata cews, kamfanin Facebook ya samu ribar aƙalla Dala biliyan Dubu. An kuma ƙiyarsa cewa, matashi na iya samun aƙalla daga Dala 50 zuwa sama a kowacce wata ta hanyar amfani da Facebook, amma matasan mu na Afrika basa amfana da wannan tsarin, a kan haka muka fito da tsarin SINNTS domin matasa masu fasaha za su amfana ta hanyar samun kuɗaɗe a kan dukkan abin da suka ɗora a manhajar.
Mene ne sharhinka a kan matasa masu amfani da kafafen sadarwa wajen cin zarafin mutane?
Lallai yadda wasu matasan ke amfani da kafafen sadarwa wajen yaɗa kalaman ɓatanci a cikin al’umma abin takaici ne. Za mu tabbatar da mun tsaftace wannan mahajar ta mu daga masu irin wannan halin. Ya kumata su gane cewa, wannan ba abin kirki ba ne domin addini ma ya haramta cin zarafin mutum ta kowacce hanya. Haka kuma doka ta haramta hakan, akwai kuma tanade tanade na dokokin Nijeriya da zai iya kaiwa ga an ɗaure duk wanda aka kama da irin wannan halin.
Ta yaya mutum zai samu hawa tare da amfani da wannan mahajar ta SINNTS?
Abu ne mai sauƙi, tana nan a google playstore da sauran wuraren sauke manhajoji, daga nan ne zaka bi matakan da za su biyo baya domin zama cikakken mai amfani manhajar SINNTS.
Mun gode ƙwarai da gaske
Nima na gode sosai














