Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kawo ƙarshen tattaunawar da yake yi da shugabancin jam’iyyar APC ta kasa kan yiwuwar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki. Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Pharm. Sama’ila Adamu Burga, ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Bauchi ranar Asabar.
- Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
- Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
- Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
- Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Burga ya ce gwamnan ya shiga tattaunawar ne bayan gayyata daga APC, wadda ta buƙace shi da sauran manyan ‘yan siyasa daga jihar Bauchi, ciki har da ‘yan majalisa, da ‘yan majalisar jiha da shugabannin ƙananan hukumomi, da su koma jam’iyyar gabanin zaɓen shekara mai zuwa. Ya ce an ɗauki matakin ne a matsayin wata hanya ta tattaunawa da haɗa kai, inda ɓangarorin biyu suka nuna aniyar yin aiki tare cikin gaskiya.
Sai dai ya bayyana cewa bayan dogon nazari, APC ba ta amince da shawarwarin da aka gabatar a lokacin tattaunawar ba. A cewarsa, rashin cimma matsaya ya kawo ƙarshen dukkanin shirin sauya sheƙar gaba ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa da zarar an dakatar da tattaunawar, hankula sun koma kan matakin da gwamnan zai dauka na gaba, inda ake ganin zai iya duba wasu hanyoyi daban-daban na siyasa, ciki har da ƙulla ƙawance ko sake fasalin matsayinsa. An kuma tuna cewa kimanin makonni uku da suka gabata, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yiltwada, da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun ziyarci gwamnan a Bauchi domin jawo hankalinsa ya shiga jam’iyyar.














