ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin “Gadar Abota Tsakanin Sin Da Najeriya” Zai Kara “Hada Zukatan Al’ummun Sin Da Afirka

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Sin

Ofishin jakadancin Sin a Najeriya da gidan rediyon muryar Najeriya (VON) sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a ran 18 ga watan nan da muke ciki, inda suka kaddamar da shirin koyar da harshen Sinanci mai suna “gadar abota tsakanin Sin da Najeriya” a hukumance. Wannan shiri mai minti 15 na koyar da harshen Sinanci da ake watsawa a kowane mako, ya aike da wani sako a fili cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka yana tafiya daga “hadin gwiwar gina ababen more rayuwa” zuwa “hade zukatan al’ummun kasashen biyu”.

Najeriya ita ce babbar kasuwar samar da kwangilar ayyuka mafi girma ga Sin a Afirka, kuma ita ce kasa ta biyu mafi girma da Sin ke fitar da kayayyakinta. Daga layin dogo na cikin gari na birnin Abuja zuwa tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Lekki a Lagos, daga gadar Oboroma zuwa layin dogo na Kano-Kaduna, ana bukatar dubban ma’aikatan Najeriya dake da kwarewar fasaha da kuma harshen Sinanci. Kwarewa a harshen Sinanci yana zama daya daga muhimman abubuwan da matasan Najeriya ke bukata wajen samun aikin yi.

Gidan rediyon na VON ne zai watsa shirin “gadar abota tsakanin Sin da Najeriya” ga kasashen Afirka daban-daban, inda za a ba da labaran hadin gwiwar Sin da Afirka, ta hanyar koyar da harshen Sinanci, ta yadda karin al’ummar Afirka za su shiga cikin ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka. Babban daraktan VON Jibrin Ndace ya bayyana cewa, shirin zai samar da dandamali ga bangarorin biyu don kara fahimtar juna ta hanyar koyar da harshe da musayar al’adu.

ADVERTISEMENT

A hakika, ba wai mutanen Najeriya ne kadai suke son koyon Sinanci ba, har ma Sinawa da yawa a Najeriya suna kokarin koyon harsunan Najeriya, misali Hausa da sauransu. Mu yi tunanin lokacin da dan Najeriya ya ce “ni hao” da Sinanci, kuma ma’aikacin kamfanin Sin ya ce “na gode” da Hausa ko wani harshen kasar, to za a sami saukin tuntuba da zurfafa hadin gwiwa, kuma sakamakon hadin gwiwa zai amfanar da al’ummar wurin sosai.

Hadin gwiwar Sin da Afirka ba wai kawai yana dogara da kwarin gwiwar gwamnati da zuba jari na kamfanoni ba ne, yana kuma bukatar dinkewar zukatan jama’a. Da zarar an gina gadar harshe, kuma aka yi kyakkyawan dashen al’adu a tsakanin juna, za a gina wani dandamali mai karfi na musayar al’adu, kuma za a ci gajiyar cudanyar al’adu daga zuriya zuwa zuriya.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

“Gadar abota tsakanin Sin da Najeriya” ba shiri ba ne kawai, har ma wata mahada ce, wanda ya shaida mana cewa, mataki na gaba da za a dauka na hadin gwiwar Sin da Afirka shi ne, a bai wa kowane dan Afirka damar cin gajiyar hadin gwiwar kasashen biyu, kuma ya rika ba da labarin abotar Sin da Afirka da bakinsa.

Wannan, shi ne ainihin matakin da ake dauka don tabbatar da ka’idar “tattaunawa a tsakanin juna da samun bunkasa da kuma more damammaki tare”.(Mai zane da rubutu: MINA)

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Obi Ya Ziyarci Kwankwaso Bayan Tantance Shi A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Obi Ya Ziyarci Kwankwaso Bayan Tantance Shi A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Sin

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Sin

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.