ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaba Tinubu Ya Umarci A Samar Da Sabuwar Kwalejin ‘Yansanda A Kudancin Nijeriya

by Sani Anwar
4 months ago
Tinubu

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin kafa harabar makarantar koyar da ‘yansanda ta kudancin Nijeriya a Abeokuta, Jihar Ogun.

Hakan, na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin, mai dauke da sa hannun mai bai wa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa shawara ta musamman, kan harkokin yada labarai da sadarwa, Ikharo Attah.

A cewarsa, ministan ya ce; Shugaba Tinubu, ya ci gaba da jajircewa, wajen kawo sauyi da sauya fasalin ‘yansandan Nijeriya, ta fannin ilimi da hanyar inganta makarantar ‘yansanda da sauran cibiyoyin ‘yansanda a fadin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Alausa ya bayyana haka ne, a lokacin da babban sifeton ‘yansanda (IGP), Tunji Disu, ya jagoranci magabacinsa na ‘yansandan, Kayode Egbetokun, da wasu manyan jami’an ‘yansanda zuwa ofishinsa, domin wani taro kan makarantar da nufin kafa harabarta ta yankin kudu.

Ministan ya yi nuni da cewa, ‘yansanda na yi wa kasa hidima sosai, don haka; ya kamata kowa ya ba shi kwarin guiwa, domin yin aiki tare da samun nasara gwargwadon karfinsa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

“Wannan taro na ci gaba ne da ajandar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na sake mayar da ‘yansanda, don gudanar da ayyukansu da inganta tsaro a fadin kasar nan.”

Attah ya kara da cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne a kan tsarin samar da ababen more rayuwa nan take da kuma tsare-tsare na zahiri na sabuwar harabar makarantar ‘yansanda da ke Erije, Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Haka kuma a wajen taron, Ministan ya umarci Hukumar Jami’o’in Nijeriya (NUC), da ta gaggauta gudanar da aikin tantance kayan aiki, inda ya bayyana cewa; Shugaban kasar, yana son a tashi harabar jami’ar tare da karbar dalibai na farko tsakanin watan Satumba da Nuwamban 2026.

An tattauna batun kwalejojin ‘yansanda sama da 42 da ke fadin kasar nan da nufin mayar da su na zamani.

Ministan ya yi nuni da cewa, “ana ci gaba da tattaunawa da ‘yansanda kan bukatar amincewa da kusan biyar zuwa shida daga cikin wadancan bukatu, don yin kwasa-kwasan da suka dace da masana’antu da ‘yansanda ke bukatar kara karfinsu.

“Na gana da sufeto-janar na ‘yansanda da tsohon IG da dukkan manyan ma’aikatan, BIG na horarwa da kuma AIG na horarwa da kuma AIG na makarantar ‘yansandan.

Sun kammala tattaunawa kan yadda za a kafa harabar makarantar ‘yansanda ta kudu, sannan an tattauna gaba-daya manufofin da sauran abubuwan da ake bukata.

“Aiki na biyu na NUC, yana tafiya cikin sauri don tabbatar da albarkatun, saboda manufar shugaban kasa na kwasa-kwasan ita ce, jami’ar ta tashi a wannan shekara tare da karbar dalibai na farko a tsakanin watan Satumba da Nuwamban 2026.”

Har ila yau, ministan ya kafa kwamitoci uku wadanda babban sakataren hukumar NUC da AIG da kuma kwalejin ‘yansanda za su jagoranta.

Tinubu
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
Gwamnan Kano Abba Yusuf Ya Miƙa Fom A Matsayin Ɗan Takarar APC

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Tinubu

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Tinubu

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.