A yau Juma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar adawar kasar Sin da kutsen da wani jirgin ruwan dakarun tsaron Japan ya yi a wani yanki na zirin Taiwan, wani mataki da ya ce ya yi matukar haifar da barazana ga ‘yancin kai da tsaron Sin, kuma Sin din na matukar nuna rashin amincewa da hakan, ta kuma gabatar da kakkarfan korafi ga Japan.
Guo, wanda ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai na rana-rana da aka saba gudanarwa, ya ce sojojin kasar Sin sun gudanar da aikin dakile wannan mataki na kutse bisa dokoki da ka’idoji tabbatattu.
Ya ce can a baya kalaman kuskuren firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da yankin Taiwan, sun haifar da mummunar barna a alakar Sin da Japan, yayin da kuma kutsen jirgin ruwa da dakarun tsaron na Japan suka yi a wannan karo, da nufin nuna karfin tuwo ya kara tsananta kuskuren kasar ta Japan.
Bugu da kari, Guo Jiakun ya ce a shekarun baya-bayan nan, ana ta samun kiki-kaka, da takalar wasu hukumomin diflomasiyyar Sin dake Japan, wadanda suka haifar da mummunan yanayi.
Ya ce, “Muna sake kira ga bangaren Japan da ya dubi kura-kuransa, ya gudanar da cikakken bincike, tare da aiwatar da gyararrakin da suka wajaba, da gabatar da bayanai masu gamsarwa ga bangaren kasar Sin. (Saminu Alhassan)















Discussion about this post