Sojojin Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, ‘Operation FANSAN YAMMA’, sun tare kwale-kwale guda uku, wadanda ba a hada su ba, kuma ake zargin fitaccen shugaban ’yan ta’adda, Shehu Bagewaye ya samar domin taimaka wa mayakansa ƙetare yankunan da ke da koguna a Jihar Zamfara.
Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, inda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, wanda ya ce aikin ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri cewa shugaban ’yan ta’addan ya samo kwale-kwalen ne daga Karamar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi, domin kai su Jihar Zamfara.
Ya ce bayanan sirrin sun kuma nuna cewa an shirya amfani da kwale-kwalen ne wajen kai hare-hare da taimakawa zirga-zirgar ’yan ta’addan a yankunan dake zagaye da koguna. Sai dai sojojin, bayan samun bayanan, sun dauki matakin gaggawa inda a ranar 23 ga Agusta, 2026, suka gudanar da wani samame na sirri a wuraren da aka gano cewa suna da muhimmanci, tare da yin nasarar tare kwale-kwalen guda uku a kan hanyarsu ta zuwa inda aka nufa.
Ya ce mutanen da ke jigilar kayayyakin sun gudu bayan ganin sojojin, inda suka bar kwale-kwalen.
Danja ya kara da cewa an kwashe kayayyakin da aka kwato zuwa hannun sojoji, yayin da ake ci gaba da kokarin gano mutanen da ke da hannu wajen safarar kwale-kwalen zuwa inda aka nufa.














