ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashin Farashin Abinci Na Kara Lakume Kudaden Shiga Na Mazauna Abuja

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
Abinci

Wasu mazauna Babban Birnin Tarayya, ciki har da masu saye da ‘yan kasuwa, sun koka cewa hauhawar farashin abinci ta kara tsananta musu rayuwa.

Mazaunan sun bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Kamfanin Dillacin Labaran Nijeriya ta yi da su a ranar Lahadi a Abuja.

Wani bincike da NAN ta gudanar a kasuwannin FCT da dama, ciki har da Dei-Dei, Kubwa da Dutse, ya nuna karuwa mai yawa a farashin muhimman kayan abinci.

ADVERTISEMENT

Sakamakon binciken ya nuna cewa gidaje da dama suna sauya tsarin cin abincinsu, domin hauhawar farashi ya sa ya zama wahala a ci abinci sau uku a rana.

A cewar mazauna, halin da ake ciki ya tilasta musu rage yawan abinci da kuma komawa kan nau’ukan abinci masu araha.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

NAN ta kuma ruwaito cewa ‘yan kasuwa sun koka da raguwar ciniki, inda suka danganta hakan da karancin karfin sayen kayayyaki na kwastomomi.

Wani dillalin kayan lambu a kasuwar Dei-Dei, Malam Adamu Isah, ya ce ‘yan kasuwa na fuskantar manyan kalubale sakamakon tsananin tashin farashin abinci da kuma raguwar masu saya.

“Da farko, ana sayar da babban kwandon tumatir tsakanin Naira 18,000 zuwa Naira 25,000, amma yanzu ana sayar da shi tsakanin Naira 45,000 zuwa Naira 48,000.

“Buhun barkono wanda a da ake sayarwa tsakanin Naira 70,000 zuwa Naira 85,000, yanzu ya kai tsakanin Naira 80,000 zuwa Naira 96,000.”

Sai dai Adamu ya nuna damuwa kan asarar kudade sakamakon lalacewar kayan abinci kafin a sayar.

“Wasu lokuta, har kashi daya bisa hudu ko rabin kwandon tumatir na lalacewa kafin a sayar, lamarin da ke janyo asara,” in ji shi.

Ya danganta matsalar da hauhawar farashin man fetur, wanda ke janyo jinkiri wajen kai kayayyaki zuwa kasuwa.

“Jigilar kaya na da matukar muhimmanci a wannan sana’a. Muna sayo kayayyaki daga gonaki, amma muna fuskantar kalubale wajen kawo su kasuwa.

“Muna rokon gwamnati ta magance matsalar farashin mai, domin yana matukar shafar sana’o’inmu da rayuwarmu,” in ji shi.

Wata ‘yar kasuwa a kasuwar Kubwa, Hajiya Peace Dabid, ta kuma koka da raguwar ciniki, inda ta danganta hakan da halin tattalin arzikin kasar.

“A da, ina sayar da karamar robar tumatir tsakanin Naira 1,500 zuwa Naira 1,800, amma yanzu ya kai tsakanin Naira 4,000 zuwa Naira 4,500.

“Karamin kwandon barkono yanzu ya kai Naira 10,000, kusan ninki biyu daga tsohon farashinsa na Naira 5,500 zuwa Naira 6,000.”

Wani mai sayar da hatsi a kasuwar Dutse, Malam Ahmad, ya ce ‘yan kasuwa na kokarin ci gaba da kasuwancinsu duk da kalubalen.

“Muna dai jurewa ne don kada mu tsaya cak, amma sauyin farashi a kai a kai ba abin karfafawa ba ne.

“Mutum ba zai iya tsara gobe ba, domin ba ka san farashin kaya a lokaci mai zuwa ba,” in ji shi.

Ya ce buhun shinkafa mai kilo 50 yanzu ana sayar da shi tsakanin Naira 52,000 zuwa Naira 55,000, sabanin Naira 46,000 zuwa Naira 48,000 da aka samu kimanin watanni biyu da suka gabata.

Ya kara da cewa wake yanzu ya kai tsakanin Naira 80,000 zuwa Naira 82,000 kan buhun kilo 50, daga Naira 69,000 zuwa Naira 72,000 a baya, yayin da guga daya na garri ke sayarwa tsakanin Naira 2,000 zuwa Naira 2,500, daga tsohon farashi na Naira 1,200 zuwa Naira 1,500.

Malam Rabi’u Haruna, mai sayar da sukari a kasuwar Dutse, ya ce tsadar sufuri ta rage musu ribar kasuwanci.

“Yanzu ina sayen sukari a Naira 65,000 maimakon Naira 60,000. Wasu lokuta ma, ko mun sayar ba ma samun riba saboda kudin sufuri.”

Wani mazauni, Malam Paul Ugo, ya ce ci gaba da tashin farashi na shafar masu saya da masu sayarwa baki daya.

“A da, ina saye da yawa, amma yanzu sai kanana-kanana nake iya saya.”

Hajiya Safiya Muhammad, wata mazauniya, ta nuna damuwa kan yadda hauhawar farashin abinci ke shafar gidanta.

“Ciyar da iyalina ya zama da wahala sosai. Yanzu ina rage girki kuma ina mai da hankali kan abinci masu saukin araha domin mu iya jurewa.”

Ta bukaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa domin daidaita farashi da rage wahalar da jama’a ke ciki.

Bayanan Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna cewa hauhawar farashin abinci a Nijeriya ya kai kashi 14.31 cikin dari a watan Maris na 2026 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, abin da ke nuna ci gaba da matsin lamba kan farashin abinci a fadin kasar.

Binciken ya nuna karuwa da matsin tattalin arziki ga ‘yan kasuwa da masu saye, yayin da kudaden shiga ke nan daram amma farashin abinci ke ci gaba da tashi.

Abinci
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Abinci
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
Labarai

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ƙwato Makamai A Kwara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ƙwato Makamai A Kwara

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.