ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
3 weeks ago
Adawa

A daidai lokacin da guguwar siyasar Nijeriya ke ƙara tashi a sararin samaniya gabanin zaben 2027; jam’iyyun adawa na fuskantar jerin ƙalubalen da za su iya yi masu tarnaƙin karon battar- ƙarfe da jam’iyyar APC da ke mulkin ƙasa.Baƙin hazo a farfajiyar siyasar Nijeriya ya yamutse ne a yayin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar babbar jam’iyyar adawa ta ADC da wasu jam’iyyu huɗu a bisa ga abin da ta kira kasa cika sharuɗɗan samun nasara a zaben 2023 da kuma zabukan cike gurbi da aka gudanar daga baya.

Rikice- rikicen cikin gida, shari’u a mabambantan kotuna, sauya sheƙar jiga-jigan ƴan siyasa da binciken hukumomin yaƙi da cin hanci na EFCC da ICPC na daga cikin abubuwan da suka haddasa tambayar ko jam’iyyun adawa na iya fuskantar jam’iyya mai mulki a babban zaben da ke tafe? Hukuncin ya kasance ba-zata ga jam’iyyar ADC kasancewar akwai umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya dakatar da ci- gaba da sauraron shari’ar domin kuwa a Ranar 22 ga Mayu, 2026, Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta amince da buƙatar dakatar da duk wani ci- gaba a shari’ar hayagagar har sai an kammala sauraron asalin ƙarar da ke gabanta.Sauran jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da Action Peoples Party, Action Alliance, Accord Party da kuma Zenith Labour Party waɗanda duka kotun ta ce ba su kai matsayin da ake buƙata ba a matsayin jam’iyyun siyasa.Jam’iyyar adawa ta ADC ita ce kan gaba wajen fuskantar ƙalubale musamman a bisa ga zartas da hukuncin kotun wanda ya janyo cece-kuce a tsakanin ƴan siyasa magoya baya, lauyoyi da masana harkokin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Tuni dai jam’iyyar ADC ta yi watsi da hukuncin gabaɗaya tana mai cewa za ta ɗaukaka ƙara domin kare matsayinta tare da jaddada cewar siyasa ce ƙashin bayan ɗaukar matakin wanda ke buƙatar adalci a kotu.

ADVERTISEMENT

Gabanin wannan rikita- rikitar, jam’iyyar ADC ta shiga matsalolin cikin gida da suka shafi shugabanci da ya kai ga shari’u kan halaccin zabukan cikin gida wanda ya rage mata ƙarfi da ma canza sheƙar wasu jigogi tare da fuskantar rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobinta.

Haka kuma yunƙurin haɗa kan ƴan adawa a ƙarƙashin wata babbar jam’iyyar haɗaka ya fuskanci cikas sakamakon sabani a tsakanin manyan ƴan siyasa wanda ya hana samar da cikakkiyar ƙwarƙƙwarar jam’iyyar da za ta zama babbar barazana ga APC a akwatin zabe.A gefe guda, jam’iyyar PDP wadda a baya ita ce ke jan zaren mulki gabanin ta koma jam’iyyar adawa, a yanzu haka ta na fama da zazzafan rikicin shugabancin da ya kassara ta tare da raba kan jam’iyyar gida biyu ta yadda kowanne bangare ke iƙirarin shi ne sahihin bangare.

LABARAI MASU NASABA

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

Rikicin jam’iyyar PDP ya zama silar mabambantan shari’u a kotuna daban- daban tare da kafa kwamitoci masu cin karo da juna wanda hakan ya sa jam’iyyar ke fama da rashin tabbas a matakin ƙasa bakiɗaya.Ita kuwa Jam’iyyar NDC wadda ta tsayar da Peter Obi takarar Shugaban Ƙasa da Rabi’u Kwankwaso a matsayin mataimaki na ƙoƙarin kafa kanta a matsayin sabuwar jam’iyyar adawa da za ta ƙalubalanci APC, amma ta na fuskantar ƙalubalen goyon baya da kuma matsalar haɗin kai a tsakanin shugabanni.

Masu fashin baƙin harkokin siyasa na ganin rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa na iya baiwa jam’iyyar APC cikakkiyar dama a zabe mai zuwa, musamman idan har ƴan adawa suka kasa haɗa kai gabanin zabe.Tuni dai jam’iyyun adawa suka zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunƙurin yi masu kisan mummuƙe da manufar mayar da siyasar Nijeriya a tsarin jam’iyya ɗaya tilo, zargin da wasu suka ce akwai ƙamshin gaskiya bisa ga wutar da ke ci-gaba da ruruwa a jam’iyyun adawa.

Masu wannan ra’ayin sun danganta hakan ne da yadda manyan jiga-jigan ƴan siyasa ciki har da gwamnoni da ƴan majalisun tarayya suka riƙa rububin komawa APC, abin da suke ganin zai rage ƙarfin fafatawar zaben da ke tafe.Rashin baiwa jam’iyyun adawa cikakkiyar damar auna tsawon su da jam’iyyar APC da ke mulkin ƙasa, babbar barazana ce ga mulkin dimokuraɗiyyar Nijeriya kamar yadda masu ruwa da tsaki a siyasar ƙasar suka bayyana tare da kakkausan gargaɗi a kai.

Bugu da ƙari, jam’iyyun adawa sun zargi hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da amfani da bincike wajen matsa masu lamba kan su shiga jam’iyya ma mulki ko kuma su jingine duk wata tafiya ta adawa, zargin da jam’iyyar APC ta yi watsi da shi.Sai dai jagororin adawa sun bayyana cewar binciken da ake yi wa tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon Ministan Shari’a kuma ɗan takarar Gwamnan ADC a jihar Kebbi, Abubakar Malami da tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da sauransu a matsayin misalai na abin da suke zargi.

Sai dai hukumomin sun musanta zargin, suna cewar suna aiki ne bisa doka ba tare da la’akari da kowace irin jam’iyya ba a yaƙi da cin hanci da rashawa da suke yi, yayin da ita ma APC ta ce ko kaɗan ba ta da hannu a binciken da hukumomin ke yi.Tun a watannin baya dai wasu jam’iyyun adawa suka nuna rashin amincewa da shugabancin Farfesa Joash Amupitan wajen jagorantar zaben 2027 suna cewar shugaban hukumar zaben ya riga ya nuna inda bakinsa ya karkata don haka ba su yadda da sahihancin zaben da zai gudanar ba. Mummunan Hari Ne Ga Dimokuraɗiyya – AtikuA yayin da yake mayar da martani kan hukuncin, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da cewa babban hari ne kai tsaye ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

A wata sanarwa da kakakinsa Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya bayyana hukuncin a matsayin wani mataki na nuna salon mulkin kama-karya a gwamnatin Tinubu wanda ya bayyana a matsayin yunƙuri mai hatsari da ke barazana ga tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

A cewarsa hukuncin kotun alama ce da ke nuna cewa a na ƙoƙarin kare lagon jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027, lamarin da ya ce zai iya rage zafin gwabzawa a zaben da kuma hanawa jama’a zaben waɗanda suke ra’ayi.

Ya ce hukuncin abin mamaki ne kasancewar kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da sauraren shari’ar har sai an kammala shari’ar da ke gaban ta. A kan wannan ya ce ma’anar wannan umarni a bayyane take, domin dakatar da shari’a na nufin a tsayar da duk wani mataki gabaɗaya, ciki har da yanke hukunci.

Atiku ya bayyana cewar a fili yake gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali ne kacokam wajen kawar da manyan abokan hamayya gabanin zaben 2027 ta hanyar raunata su yana mai gargaɗin cewa hakan na iya zama barazana ga makomar dimokuraɗiyyar Nijeriya.Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku ya kuma soki yadda gwamnatin Tiinubu ke mayar da hankali kan durƙusar da ƴan adawa maimakon magance manyan matsalolin da ke addabar ƙasar kama daga kan tabarbarewar sha’anin tsaro, matsin tattalin arziki, talauci da rashin aikin yi yana cewar ko kaɗan hakan ba shugabanci ba ne.

Ya ce Ƴan Nijeriya na ganin abin da ke faruwa. A na kai hari ga jam’iyyun adawa. A na matsawa jam’iyyun siyasa lamba. A na amfani da ikon gwamnati ba don ci-gaban ƙasa ba, sai dai domin kare muradun siyasa.”A kan wannan ya yi gargaɗin cewar idan ba a gyara wannan gurbataccen yanayin ba, wannan matsalar za ta haifar da dawowar jama’a daga rakiyar mulkin dimokuraɗiyya domin an rage damar da ƴan ƙasa suke da ita na zaben jam’iyyu da ƴan takarar da suke ra’ayi a 2027. Za Mu Shiga Zaben 2027- Jam’iyyar ADCSai dai jam’iyyar adawa ta ADC ta tabbatarwa magoya bayanta da al’umma cewa ta riga ta ɗauki matakin ɗaukaka ƙara kan hukuncin ta na cewar duk da wannan hukunci, ba za a cire ta daga ƙuri’ar zaben 2027 ba.

A martanin da Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar ya zargi alƙalin da ya yanke hukuncin, Mai Shari’a Peter Lifu da cewar ya karanta wani tsararren abu ne da aka shirya a baya ta hannun wasu da ke da alaƙa da gwamnati domin share masu fagen ci-gaba da mulki.A kan wannan jam’iyyar ta yi kakkausan gargaɗin ɗaukar kowane irin mataki domin amfani da bangaren shari’a domin gurgunta dimokuraɗiyya wanda a cewar ta hakan zai haifar da gagarumar rikita- rikita a farfajiyar siyasar ƙasar nan.

Ya ce jam’iyyar ta yi matuƙar damuwa da hukuncin da kotun ta yanke tare da cewar hukuncin ya ci karo kai tsaye da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma dukkan ƙa’idojin shari’a da aka sani.

Jam’iyyar ta ce a cikin takardar martanin rantsuwa da ta gabatar a gaban kotu a watan Mayu, Hukumar Zabe wacce ita ce hukumar da ƙundin tsarin mulki ya baiwa alhakin rajista, tsarawa da kuma kula da jam’iyyun siyasa a Nijeriya, ta jaddada cewa jam’iyyar ADC ba ta karya wata ƙa’ida ta rajista ba, kuma ba ta gaza cika wani sharaɗi na ƙundin tsarin mulki da ya shafi nasarar zabe ba, tare da cewa babu wata hujja ta doka da za ta tabbatar da soke rajistar ta.A cewar jam’iyyar baya ga matsayar ƙarfafa mata da Hukumar Zabe ta yi na goyon bayan jam’iyyar, abin damuwa ne yadda alƙalin da ya zartas da shari’ar yana da masaniya kan umarnin da Kotun Ɗaukaka ta zartas a ranar 22 ga Mayu, 2026, a inda ta umarci a dakatar da ci-gaba da sauraron shari’ar.

ADC ta kuma bayyana hukuncin a matsayin wata hujja mafi ƙarfi da ke nuna abin da ta kira boyayyen shiri na gwamnatin Bola Tinubu na ƙoƙarin gina tsarin jam’iyya ɗaya a Nijeriya tare da cewar ta ɗauki wannan mataki a matsayin barazana kai tsaye ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Dakatar da Hukuncin Soke Rajistar ADCA yayin da ake tsaka da taƙaddama da cece- kuce kan hayagagar; Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta umarci Hukumar Zabe ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.Kotun a ranar Talata ta umarci hukumar zabe da kada ta ci- gaba da aiwatar da soke rajistar har sai an kammala sauraron ƙarar asali da jam’iyyun da abin ya shafa suka shigar, wadda ke ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

Alƙalan kotun ɗaukaka ƙara uku sun yi watsi da hukuncin tare da bayyana matakin da Mai Shari’a Lifu ya ɗauka a ranar Litinin a matsayin raini ga kotu mai girma da kuma rashin bin ƙa’idojin shari’a. Kotun ta ce babban kuskure ne alƙalin ya tafka na zartas da hukuncin shari’ar da kotun da ke gabansa ta bayar da umurnn dakatarwa.

Hukumar Zabe ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara ne domin neman a dakatar da aiwatar da hukuncin da ya umarci a soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu, saboda ba ta gamsu da hukuncin ba.

Adawa
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ posts Bio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Shekara 200 Bayan Shehu Ɗan Fodiyo: Hubbarensa Na Ci Gaba Zama Wajen Ziyara Da Neman Tabarruki
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma
Adawa
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Ya Raba Buhunan Taki 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara
  • Sulaiman
    Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B
  • Sulaiman
    CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

MASU ALAKA

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta
Manyan Labarai

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Manyan Labarai

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa
Da ɗumi-ɗuminsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Next Post
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira

Shekarar Musulunci: Tinubu Ya Yi Kira Da A Nuna Kyakkyawan Kishin Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Ya Raba Buhunan Taki 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara

Gwamna Dauda Ya Raba Buhunan Taki 72,000 Da Kayan Noma Kyauta Ga Manoman Zamfara

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello

July 11, 2026
Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar  Jamus

Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar Jamus

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 11, 2026
Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.