ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tattaunawar Gwamnatin Tarayya Da SSANU Da NASU Ta Tashi Baram-baran

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
NASU

Tattaunawar da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kwamitin Hadin Gwiwa (JAC) na kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i ta kare ba tare da cimma matsaya ba a ranar Litinin a Abuja, yayin da manyan batutuwa suka ci gaba da zama cikin rashin tabbas dangane da rashin warware su.

JAC ya kunshi Manyan Kungiyoyin Jami’o’in Nijeriya da kuma Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Da Ba Sa Koyarwa.

An dage taron, wanda Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya kira, zuwa ranar 5 ga Mayu domin ci gaba da tattaunawa.

ADVERTISEMENT

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya tunatar da cewa SSANU da NASU sun fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a ranar 30 ga Afrilu bayan cikar wa’adin wata guda da suka bai wa gwamnatin tarayya kan sake duba yarjejeniyar shekarar 2009.

Kungiyoyin na nuna adawa da shirin gwamnatin tarayya na kara albashi da kashi 30 cikin dari, inda suka nace a kan karin kashi 40 cikin dari ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Tun da farko, gwamnatin tarayya ta janye tayin karin kashi 30 cikin dari, matakin da kungiyoyin suka bayyana a matsayin na kai-tsaye ba tare da cikakkiyar tattaunawa ba.

Da yake magana kan yajin aikin, Shugaban Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya, Mista Mohammed Ibrahim, ya ce an bi umarnin yajin aikin bai-daya a fadin kasar, lamarin da ya gurgunta ayyukan gudanarwa da muhimman hidimomi a jami’o’i.

“Bukatunmu ba su canza ba. Kashi 40 cikin dari shi ne mafi kankantar matsayi da za mu amince da shi, kuma yajin aikin zai ci gaba har sai an samu gagarumin ci gaba,” in ji shi.

Ibrahim ya ce ofisoshin gudanarwa, asibitoci, dakunan kwanan dalibai da sassan kudi sun kulle a jami’o’i daban-daban sakamakon cikakken bin umarnin yajin aikin.

A wani bangaren kuma, Jami’ar of Maiduguri ta dage jarrabawar (e-edams) dinta saboda tangardar da yajin aikin ya haifar.

Haka kuma, yajin aikin ya nakasa harkokin karatu da gudanarwa a Ahmadu Bello Unibersity.

Binciken wakilinmu ya nuna cewa an rufe ginin majalisar jami’a (Senate), dakin karatu da kuma asibitin jami’ar.

Haka zalika, an rufe sassan ayyuka da kula da kadarori, lamarin da ya janyo tangarda ga samar da ruwa da wutar lantarki a jami’ar.

Da yake magana da manema labarai yayin wata zanga-zangar lumana a babban harabar jami’ar, shugaban SSANU reshen ABU, Shuaibu Ahmed Halilu, ya ce sun bi umarnin da kungiyar kasa ta bayar kan yajin aikin.

NASU
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
NASU
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Yobe, Sun Kashe Ƴan Ta’adda 50

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Yobe, Sun Kashe Ƴan Ta’adda 50

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.