ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Yobe, Sun Kashe Ƴan Ta’adda 50

by Abubakar Sulaiman
4 months ago

Dakarun rundunar haɗin gwuiwa ta Operation HAƊIN KAI sun daƙile wani babban hari da mayaƙan ISWAP suka kai shalƙwatar bataliya ta 27 da ke Buni Gari da kuma shingen bincike na Buni Gari a jihar Yobe, inda aka kashe aƙalla ‘yan ta’adda 50.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana a wata sanarwa cewa harin ya fara ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Juma’a daga sassa daban-daban, amma dakarun sun mayar da Zafafan martani tare da hana maharan kutsawa cikin sansanin.

Ya ce mayaƙan ISWAP sun kai harin ne daga ɓangaren yamma kafin su ƙara turo mayaƙa daga kudu da kudu maso yamma domin kewaye sansanin, amma dakarun sun tsaya tsayin daka tare da amfani da manyan makamai da dabarun yaƙi wajen ragargazar maharan.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sama sun bayar da bayanan sirri da sa ido daga sama, lamarin da ya taimaka wajen kai hare-haren sama kan maharan yayin da suke tserewa. Rundunar ta ce an ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda takwas, bindigogin GPMG guda biyu, makaman RPG, harsasai da kuma wasu abubuwan fashewa na IED.

Sai dai rundunar ta bayyana cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin fafatawar, inda ta yaba da jarumtakar su tare da jaddada cewa ana ci gaba da farautar sauran ‘yan ta’addan domin hana su sake haɗuwa ko kai wani hari a yankin.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Hukumar Kula Da Abuja Ta Haramta Amfani Da Tayoyi Wajen Gasa Sassan Dabbobi

Hukumar Kula Da Abuja Ta Haramta Amfani Da Tayoyi Wajen Gasa Sassan Dabbobi

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.