ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Jinjina Wa Jami’an Tsaro Kan Jajircewarsu Wajen Kawo Karshen Ta’addanci

by Sani Anwar
3 months ago
Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa jami’an soji da sauran jami’an tsaro, inda ya bayyana cewa; kasar na sane da irin gudunmawar da suke bayarwa, don kawo karshen ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Shugaban, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, ya kuma yi jawabi ga jami’an soji da sauran jami’an tsaro, inda ya yaba wa sojojin bisa sadaukarwar da suke yi, inda ya kwatanta su a matsayin garkuwar kare ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Yayin da yake bayyana yaki da rashin tsaro a matsayin aikin da sojoji suka sanya a gaba, shugaban kasar ya ce; aiki ne na kasa, inda ya bukaci ‘yan kasar da su tallafa wa jami’an tsaro “ta hanyar samar da bayanai masu amfani a kan lokaci, da zarar ka ga wani abu, sai ka yi maza ka sanar, haka nan idan ka san wani abu, sai ka yi gaggawar kai rahoto,” in ji shi.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, ya rubuta cewa; “Ina yaba wa dukkan sojojinmu da ke sahun gaba kan kishin kasa, wajen yaki da ta’addanci ta kowane fanni. Babau shakka, kun tsaya a matsayin garkuwa tsakanin ‘yan kasa, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, domin kawar da masu neman hana zaman lafiya, tsaro da martabar al’ummarmu.”

Kazalika, ya yaba wa sojojin da suka dauki nauyin kare ‘yan Nijeriya a wuraren da babu zaman lafiya, yana mai cewa; kasar ba za ta dauki wannan sadaukarwa da wasa ba ko kadan.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

“Wannan yakin, ba mai sauki ba ko kadan, domin kuwa ya zo da abubuwa na rashin jin dadi, matsi da kuma sadaukarwa, amma, kun tsaya tsayin daka wajen kokarin magance shi. Ana sane tare da amincewa da hidimarku da kuma sadaukarwar da kuka yi, wannan wannan kasa taku ba za ta taba dauka da wasa ba.”

“Ga duk wani jami’in soja, ‘yansanda, DSS, Cibil Defence, jami’an leken asiri, jami’an tsaro na cikin gida da duk wanda ke aiki dare da rana don tabbatar da tsaron Nijeriya, ina mai yi muku godiya, na gode kwarai da gaske.

“Ina kuma jinjina wa iyalan wadannan jami’ai na tsaro, wadanda yawa daga cikinku, wadannan jami’ai sun yi nisa da ku a dare da rana, don haka Nijeriya na sane da wannan sadaukarwa taku.

“Muna girmama wadanda suka biya mafi girman farashi don kare kasarmu. Sunayensu ba za su yi ta yawo a cikin al’umma ba, amma karfinsu da ayyukansu na ceton al’ummomi a kullum yana yawo a tsakanin al’ummar.”

Shugaban ya jaddada muhimmancin aikin soja, yana mai jaddada cewa; yaki da ta’addanci ba aikin soji ne kadai ba.

“Hakkin kasa ne, ‘yan kasa su tallafa wa jami’an tsaronmu ta hanyar samar da bayanai masu amfani a kan lokaci, idan ka ga wani abu sai ka sanar cikin gaggawa, ta hanyar bayar da rahoto.

“Nijeriya ba za ta mika wuya don tsoro ba, ba za mu bari ‘yan ta’adda da ‘yan fashi masu garkuwa da mutane ko masu tsattsauran ra’ayi su bayyana wa duniya wace al’umma ce mu ba, domin kuwa tashin hankalin ba shi ne asalinmu ba.

“Saboda haka, ga sojojinmu da duk sauran masu kishin kasa, na gode da jajircewarku matuka,” kamar yadda ya rubuta.

Tinubu
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Sabbin Ƴansanda 50,000 Da Karin Sojoji — Tinubu

Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Sabbin Ƴansanda 50,000 Da Karin Sojoji — Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.