ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsanar Baki:’Yan Nijeriya Na Bukatar Daukin Gwamnatin Tarayya A Afirka Ta Kudu

by Yusuf Shuaibu
4 months ago
Tsanar

‘Yan Nijeriya da ke Afirka ta Kudu sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa wajen kare rayukansu da kasuwancinsu a kasar.

Shugaban kungiyar ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu (NICASA), Reb Frank Onyekwelu, shi ya yi wannan kira a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

A halin yanzu akwai karuwar zanga-zangar adawa da bakin haure a fadin Afirka ta Kudu, inda masu zanga-zangar suka mayar da hankali kan shagunan da baki suka mallaka, yayin da suke kiran a kori wadanda ba ‘yan kasa ba.

ADVERTISEMENT

A wata sanarwa a ranar Juma’a, wacce mai magana da yawun hukumar kula da ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje (NiDCOM), Abdur-Rahman Balogun, ya sanya hannu a kai, ta roki ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu da su rufe kasuwancinsu su kuma kasance cikin aminci.

Ya ce shawarar ta biyo ne bayan wata wasika daga ofishin jakadancin Nijeriya a Johannesburg a ranar Laraba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cewar hukumar, zanga-zanga a Gabashin Landan, Cape Town, Durban, da KwaZulu-Natal sun rikide zuwa tashin hankali, wanda ya haifar da satar kayayyaki, lalata kadarori, da jakkata mutane.

NiDCOM ta ce bayanai daga ofishin jakadanci sun nuna cewa an shirya sabbin zanga-zanga a lardin Gauteng tsakanin ranakun 27 da 29 ga Afrilu, inda masu zanga-zangar ke neman matsa lamba ga gwamnatin Afirka ta Kudu ta kori ‘yan kasashen waje.

NiDCOM ta kuma yi kira ga ‘yan kasuwa na Nijeriya da su rufe shagunansu a ranar 27 ga Afrilu, wacce aka kebe a matsayin ranar ‘yanci, sannan su yi la’akari da ci gaba da rufe su a ranar 28 da 29 ga Afrilu, saboda galibi ana kai wa kasuwancin mallakar baki hari a yayin zanga-zangar.

Duk da haka, yawancin ‘yan Nijeriya sun shiga kafafen sada zumunta don su soki rashin matakin gwamnatin tarayya wajen kare ‘yan kasarta a Afirka ta Kudu, sun kara da cewa neman ‘yan Nijeriya su rufe kasuwancinsu ba shi ne mafita ga matsalar ba.

A daya bangaren, Ghana ta mayar da martani ga wani bidiyo da ya bazu na wasu ‘yan kasa da ke fuskantar tsangwama a Afirka ta Kudu ta hanyar kira ga mukaddashin babban kwamishanan Afirka ta Kudu da ke Accra, Thando Dalamba.

Ma’aikatar harkokin waje ta Ghana ta ce abin da ke cikin bidiyon wanda ya faru ga ‘yan kasarta a Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da cin zarafin jama’arta.

Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Ablakwa, ya bayyana cewa gwamnati za ta mayar da wanda abin ya shafa, Emmanuel Asamoa, tare da ba shi kudade mai yawa bayan da ya fuskanci barazana da cin zarafi.

Gwamnatin Ghana ta kuma shiga tattaunawa kai tsaye da hukumomin Afirka ta Kudu, wanda ya kai ga bayar da hakuri na hukuma da tarurrukan diflomasiyya.

Tsanar
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
2027: Babu Maganar Masalaha A APC Ta Nasarawa — Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda

2027: Babu Maganar Masalaha A APC Ta Nasarawa — Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.