ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Babu Maganar Masalaha A APC Ta Nasarawa — Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda

by Muhammad
4 months ago

Tsohon Sufeto Janar na ‘Yansanda, Mohammed Adamu Abubakar, ya bayyana cewa babu maganar amfani da tsarin masalaha (consensus) wajen zaɓen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa.

Tsohon shugaban ‘yansandan, wanda yake daga cikin manyan masu neman tikitin jam’iyyar, ya ce babu abin da za su amince da shi face zaɓen fidda gwani kai tsaye.

Ya bayyana hakan ne a Lafia ta bakin Daraktan Hulɗa da Wayar da Kai na kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Hon. Isah Nathaniel, a ranar Asabar.

ADVERTISEMENT

Nathaniel ya ce matsayar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka cimma—ciki har da dukkan ‘yan takarar gwamna, ‘yan Majalisar Tarayya, tsofaffin gwamnoni biyu na jihar, da sauransu—a wani taro da aka yi a gidan gwamnatin jihar da ke Abuja, na nan daram.

Ya ƙara da cewa a wancan taro, an amince da zaɓen fidda gwani kai tsaye a matsayin hanya kaɗai ta zaɓen ɗan takara, wanda ya yi daidai da ra’ayin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na bai wa kowane ɗan jam’iyya damar bayyana ra’ayinsa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Nathaniel ya bayyana cewa a wannan taro, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabbatar cewa tsarin zai kasance a buɗe, mai gaskiya, kuma bisa dokokin jam’iyya da kundin dokar zaɓe, ta yadda ba za a samu ƙorafi ba.

Sai dai ya ce abin ya ba mutane da dama mamaki, ganin yadda bayan ‘yan kwanaki kaɗan aka fara maganar fifita wani ɗan takara.

A cewarsa, duk da cewa gwamnan na da ‘yancin goyon bayan duk wanda ya ga dama, hakan ba zai iya soke matsayar da masu ruwa da tsaki suka ɗauka ba, wadda ta amince da zaɓen fidda gwani kai tsaye bisa dokokin jam’iyya da na zaɓe.

“Yanzu fara neman wata tattaunawa ko yarjejeniya a wannan lokaci tamkar ƙoƙarin kauce wa gaskiya ne.

“Mun ce a’a ga duk wani nau’in tilastawa ko son rai; muna tsayawa kan bin doka da oda,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jagoransa ya riga ya sayi fom ɗin neman tsayawa takara da na nuna sha’awa kamar yadda doka ta tanada, yana mai cewa jama’a na jiran zaɓen fidda gwani ne kawai domin tabbatar da goyon bayansu gare shi.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Wadanne Kasashe Ne Ba Su Taba Zuwa Kofin Afirka Ba?

FIFA Ta Kara Yawan Kudaden Da Za Ta Bai Wa Kasashen Da Suke Buga Gasar Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.