A lokacin da mata da dama masu shekaru irin nata ke more ritaya tare da kula da jikokinsu, Furera Muhammad mai shekara 63 ta koma aji domin neman ilimin da ta rasa tun tana yarinya.
Furera, wadda ke karatu a wata makarantar Islamiyya tare da wasu daga cikin jikokinta a Rigafada da ke Jihar Kano, ta ce har yanzu tana nadamar rashin samun damar yin karatun boko tun tana ƙarama, saboda a zamaninta ba a cika ƙarfafar ƴaƴa mata su je makaranta ba.
Ta ce, “Da a ce na yi karatu tun ina yarinya, ba yanzu tare da jikokina zan zauna ba. Da an ba ni damar yin karatu, da wataƙila na zama malama.”
A cewarta, rashin ba ƴaƴa mata damar samun ilimi a lokacin ƙuruciyarau ya hana mata da dama cimma burinsu da kuma ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban al’umma.
Duk da tsufanta, Furera ta ce har yanzu tana da ƙwarin gwiwar neman ilimi, tana mai fatan abin da ta yi zai ƙarfafa iyaye su bai wa ƴaƴansu mata ilimi, tare da ƙarfafa waɗanda ke makaranta su ci gaba da jajircewa wajen karatu.
Furera ta bayyana hakan ne a wani shirin tattaunawa da al’umma da Cibiyar Bincike da Ayyukan Raya Al’umma (dRPC) ta shirya tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Ford, ƙarƙashin aikin Grannies Network for Change (G-NEC) a Rigafada.
Shirin ya haɗa kakanni mata 40 domin tattauna rawar da za su taka wajen inganta ilimin ƴaƴa mata da kuma hana cin zarafin mata ta fuskar jinsi, musamman cin zarafin baki.
Aikin G-NEC na da nufin amfani da tasirin kakanni mata a cikin iyalai masu zaman tare tsakanin tsararraki domin ƙarfafa kyawawan ɗabi’u, bunƙasa damar ƴaƴa mata ga ilimi da kuma rage cin zarafin mata ta hanyar tattaunawa da al’umma da kuma isar da saƙonni masu dacewa da al’adu.
Ana aiwatar da wannan shiri a wasu zaɓaɓɓun al’ummomi a jihohin Kano da Jigawa, domin ƙara wayar da kai game da muhimmancin ilimin ƴaƴa mata, rage cin zarafin baƙi a gidaje, da kuma ƙarfafa iyalai su samar da yanayi mai aminci da goyon baya ga mata da ƴaƴa mata.














