Jam’iyyar hamayya ta NDC ta bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta APC ba ta da cancantar ci gaba da shugabancin Nijeriya wuce shekara ta 2027, sakamakon ƙaruwar matsalar tsaro, da tsada da halin ƙunci na rayuwa, gami da nisa da gwamnatin ta yi daga al’umma.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban Jam’iyyar NDC na Ƙasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, yayin ƙaddamar da Kwamitin sasanci mai mambobi 23 a Abuja, wanda aka sanya shi ƙarƙashin masanin tattalin arziki, Farfesa Pat Utomi jagoranci, tare da tsohon ɗan siyasa Alhaji Buba Galadima a matsayin mataimaki.
Sanata Zuwoghe ya jaddada cewa babbar manufar kafa kwamitin ita ce ɗinke ɓangarorin da suka ɓalle a cikin jam’iyyar sakamakon zaɓukan fitar da gwani na cikin gida, tare da sake gina amincewa juna da ƙarfafa tsarin jam’iyyar domin fuskantar zaɓen shekara ta 2027 da ke tafe.
Shugaban ya ci gaba da cewa halin da ƙasar ke ciki a ƙarkashin mulkin APC abin takaici ne, inda ya bayyana cewa rashin tsaro ya bazu zuwa yankuna daban-daban yayin da tattalin arziƙin ƙasa ke ci gaba da rugujewa, wanda hakan ke buƙatar haɗe kai domin sauya akalar shugabancin ƙasar.
A nasu ɓangaren, Farfesa Pat Utomi da Alhaji Buba Galadima sun yi kira ga dukkan mambobin jam’iyyar da su rungumi hanyoyin tattaunawa da fahimtar juna, suna masu nuna ƙwarin gwuiwar cewa haɗin kan ‘yan jam’iyya da goyon bayan al’umma ne kadai za su iya kawo sauyi na gaske a zaɓen 2027.














