ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ummul Kura Islamiyya Garki Abuja, Ta Gudanar Da Walimar Saukar Kur’anin Ɗalibai

by Sulaiman and Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago
Garki

Madarasatu Ummul Kura Islamiyya Garki Abuja, ta gabatar da walimar saukar Kur’ani daliban da suka samu saukar Alkur’ani Mai Girma karo na shida da makarantar ke yi a duk shekara, inda a wannan shekara dalibai 46 ne suka yi saukar maza bakwai Mata 39.

Da yake gabatar da jawabi a yayin taron Sarkin Garki Alhaji Dakta Usman, ya ja hankalin iyayen yara da su ba da himma wajen kula da karatun addinin ‘ya’yansu musamman ta wajen biya musu kudin makaranta, ya kuma roke su da su tallafa wa makarantar wanda ta haka ne ilimin ‘ya’yansu zai inganta.

Shi ma a nasa jawabin Sheikh Muhammad Nura Usman, ya yi kira ga iyayen yara ne da su kula da amanar da Allah ya danka a hannunsu, inda ya ce, kowa a ranar lahira sai an tambaye shi kiwon da aka bashi.

ADVERTISEMENT

Sannan ya yi kira ga yara masu shagalyuwa da kalle-kallen kwallon kafa da su koma makaranta domin samun abin da zai cece su duniya da lahirarsu.

Haka shi ma Asarkin Samarin Garki Hausa Shugaban Matasa na Garki Gana Daya, Alhaji Abdulwahhab Musa, ya yi nuni da cewa, ilimin addini abu da dake taimakawa wajen gyara tarbiyyar matasa da kuma yara ta yadda suke tasowa da kyakkyawar tarbiyya, inda ya ce rashin kyakkyawar tarbiyya ce ke haifar da aikata miyagun laifuka kamar su: Satar mutane, ta’addanci da sauran miyagun ayyuka.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ya ce hanyoyin dakile irin wadannan miyagun hala su ne a samu tarbiyya tun daga gida, inda ya ce ya kamata iyaye su rika sani abokan ‘ya’yansu, inda suka je da kuma ina za su je, ta haka ne za a samu ingantacciyar tarbiyya ga yara.

A nasa jawabin, Babban Limamin Juma’a na Garki Malam Abdullahi, addu’a ya yi gab akin da suka halarci taro da fatan alheri.Malam Mu’awiya Idris, shi ne shugaban wannan makanta ta Madarasau Ummul Kura Islamiyya Garki Abuja, ya yi LEADERSHIP bayanin farin cikin da yake yi, inda ya ce “Wannan rana ce ta farin ciki wanda ba zai misultu ba, saboda duk sanda aka ce ka karantar da dalibai har suka sauke Kur’ani a wurinka, wannan ba karamin abin farin ciki bane, domin duk sand aka koyar da wani akin alheri to duk sanda ya yi wannan aikin kana da lada.

”Ya yi kira ga iyayen yara da su bai wa ilimin addinin Musulunci muhimmanci ta hanyar kula da karatunsu.A cewarsa “Wannan ita ce hanya daya da rage wajen yi wa yara tarbiyya da kuma mayar da su masu kyakkyawar gobe, domin yana da kyau yadda iyaye ke ba wa bangaren Boko muhimmanci wannan shi ma a bashi hakan.

Taron dai ya samu halatar manyan baki irin su, Birgediya Janar Nura Muhammad, Sakin Garki Alhaji Usman, sai kuma Hakimin Hausawan Garki, Alhaji Umar Abubukar, da Iyan Misau Alhaji Sale Adamu, da Wamban Garki Alhaji Muhammad Rabiu, Santalin Garki Alhaji Isyaku Muhammad, da Sarikin Samarin Garki, Alhaji Abdulwahhab Musa, sai kuma zababben Kasilan Garki Hon. Alkasim Bala Sarki, da kuma Alhaji Muhammad Yunusa sarkin Fawan Garki da dai sauransu.

Garki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Garki
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Dangote Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Gaggauta Don Kawar Da Zazzabin Cizon Sauro

Dangote Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Gaggauta Don Kawar Da Zazzabin Cizon Sauro

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.