ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakar Da Na Yi Wa Annabin Rahma (SAW) Ce Bakandamiyata – Maryam Sangandale (2)

by Rabi'at Sidi Bala
2 months ago
Wakar

Kamar dai yadda aka sani shafin RUMBUN NISHADI na zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana har ma da mawaka daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. A yau ma shafin ya yi cozali da wata fitacciyar mawakiyar da ta shafe tsahon shekaru tana waka a cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood wato, MARYAM ABDULKARIM SULAIMAN wacce aka fi sani da MARYAM SANGANDALE Inda ta bayyanawa masu karatu  irin gwagwarmayar da ta sha kafin fara waka da kuma kalubalen da ta fuskanta bayan fara waka, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi rayuwarta.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Kin juma kina yin wakokai lokacin baya da kuma yanzu, daga bisani sai aka ji labarin kin yi aure, shin har yanzu kina ci gaba da yin waka ne ko kuwa kin dakata da yi a yanzu?

ADVERTISEMENT

Har yanzu Ina waka saboda masoya murya ta sun ce suna so su ji nayi musu murya ta a wakar su, saboda haka na ci gaba saboda kuma asali ma sana’a ta kenan to, har yanzu dai ina waka gaskiya ban daina ba [Murmushi].

Me ya fi baki wahala wajen rera waka ko rubutawa?

LABARAI MASU NASABA

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

Abin da ya fi ba ni wahala shi ne, nazari wajan yadda zan rera ta ace a sama zan yi wakar hakan yana wahalar da ni, saboda ‘tune’ dina ni a tsaka-tsaki yake ko kasa, amma sama ba nawa bane yana harde ni sosai. A wajan rubutu kuma wajan saka kalaman maganganun da zan sa a wakar to, dole sai na je neman taimakon a taya ni da rubuta wakar nan, musamman karin da zan rera yayi dadin da nake so.

Ko kina da ubangida a fannin waka tun a wancen lokaci zuwa yanzu?

Sai dai abokan aiki, ba ni da Ubangida gaskiya. Ubangidan nawa wanda ya kawo ni harkar wakar ne cikin industry wato Marigayi Alh. AHMAD ALIYU TAGE Allah ya jaddada rahamar sa a gare shi.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta sanadiyyar waka?

Kalubalen shi ne, ace wai ‘yar iska ce, gata nan za ta wayon iskanci. Ba za ka raba ‘yan’unguwa masu zaman majalisa daman ba sa rabo da yin sharri da gutsri tsoma da gulma ba, sai dai su zagi duk macen da ta fita neman na kanta, sun yi kudin goro da wacce take iskancin ne ke fidda ta daga gidan su, kuma wacce ta je neman halak din ta, to, duk hukunci daya suke mana akan haka na sha wannan kalubalen na zagi sai dai Allah ya saka mana kawai.

Ya batun nasarori, kamar wadanne irin nasarori ki ka samu sanadiyyar waka?

Alhamdulillah nayi muhalli, na je na sauke farali a kasa mai tsarki, na kai mahaifina ya je yayi aikin Hajji, mahaifiyata mun je Umrah da ita nayi motocin Hawa da wadanda aka ba ni da wayanda na saya da kudi na, har 8 na sayi filaye, na je wasu kasashen duk a nasarorin waka na taimaki wadanda Allah ya ba ni damar na taimake su ta fannoni daban-daban. Da sauran su, Alhamdulillah

Idan aka ce ki bambantawa masu karatu bambancin wakokin baya da kuma na yanzu, tare da ma’anarsu me za ki ce?

Eh, to! wakokin yanzu ai na zamanin yanzu ne, kuma suna da dadi wasu, wasu kuma akwai ma’ana, sannan suna isar da sakon inda ake son su je. Wakokin baya su kuma wa’azi ne tare da fadakarwa da ilmantarwa, sannan za ka ji masu sauraron na da, da na yanzu suna cewa wallahi sun fi jin dadin na da saboda suna samun nutsuwa wajan sauraron wakokin saboda akwai dattako,. Da dai sauran su dai sai a wajan masu sauraron za ki fi samun cikakken bayani da kuma dalilansu.

A cikin wakokin da ki ka rera ko ki ka rubuta wacce waka ce ta zamo bakandamiyyarki, kuma me ya sa?

Waka ce wadda na yi wa Fiyayyen Halitta Annabin Rahma Annabin tsira. Allah ya kara masa wasila da fadila Allahumma Amin Ya Allah, ita ce nake cewa “Limamin Annabawa Mai mi’iraji da Isra’i ka zarce dukkan Halittu kukaiyi Munajati da Allah”. Wannan ita ce bakandamiyyata.

Ko akwai wani ci gaba ko rashin ci gaba a fannin waka wanda ki ke ganin ya wanzu a yanzu sabanin lokutan baya?

Aaaa! an samu ci gaba fa sosai a wannan harkar ta waka sosai, ma kuwa saboda an bi zamani an kara bunkasa harkar waka ta fannoni daban-daban wallahi Alhamdulillah ai ba wani nakasu da aka samu a harkar nan Idan ma an samu to, wanda bai tsaftace aikin wakar bane ta bangaren sa. Amma yanzu harkar waka idan akwai ma gyara to, wajan tsaftace harshe ne da gyara alkalamin rubutun fikirar ka da Allah yayi maka ka fadi kalamai tsarkakakku wanda babba da yaro za su amfana da abin da ka fada a wakar ka.

Mene ne burinki na gaba game da waka ko kuma mawaka?

Buri na shi ne, na ga mun yi waka gidauniya ta waka musamman mu mawaka mata mun yi sadaukarwa, ta yadda ‘ya’yan mu za su amfana da jikokin mu da sauran al’ummar inda muke wato Kawar mu bakidaya. Ace kuma wannan wakoain mu ruka bada su ga al’ummar musulmai da Musulunci [Murmushi]

Wace ce babbar kawarki a mawaka?

Gaskiya ba ni da babbar kawa dukkansu kawaye na ne kuma manya a waje na, indai kin iya to, ke kawata ce Babba.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga harkar waka?

Dan Allah ku shigo da zuciya daya da girmama na gaba da ku, da tsafta ta jiki, da harshe, sai kuma kusa hakuri a dukkan abin da za ku riska, wata rana sai labari, za ku ce na gaya muku. Wallahi sai kun kai ga burukanku na abin da ya sa kuka shiga Sana’ar Waka a shiga da balaga ‘yan’uwa na.

Ko kina da wata shawara da za ki bai wa sauran mawaka?

Mu so junan mu tsakanin mu da Allah, kuma mu ci gaba da hakuri da juna, dan Allah mu kara girmama junan mu a duk inda muka hadu, mu zama Uwa daya Uba ma guda daya, domin jin dadin rayuwar ta mu gabadaya kun ji.

Me za ki ce da masoyanki, masu sauraron wakokinki?

Wallahi ina kaunar ku kamar yadda kuke sona saboda wakoki na na burge ku, Dan Allah ku rika saka ni a addu’o’in ku na yau da kullum ko ba duka ba. Saboda addu’a tana da tasiri a kan masoyi, ina wannan barar a wajen ku masoya wakokina. Kuma ina yi muku fatan alkhairi.

Idan mutum yana so ki yi masa waka ta wacce hanya zai bi?

Ta hanyar lambar wayata a bi a same ni, sai mu yi magana a kan wacce waka yake so na yi masa, sai mu tattauna a nan wannan shi ne hanya mafi sauki ‘yar’uwa.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina gaishe da iyaye na farko akan irin tarbiyar da na samu a wajansu, Mahaifiya ta Allah ya kara mata lafiya da nisan kwana mai albarka, mahaifina Allah ya jaddada rahamar sa a gare shi, ya haskaka kushewar sa, ya kyauta makwancin sa, ya sa aljannar firdausi ta zam makoma. Ina gaishe da dukkan kanne na su 15 Allah ya bar mana zumuncin mu har aljanna.

Wakar
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Labarai

Daraktan Hollywood Carl Rinsch Zai Shafe Watanni 30 A Gidan Gyaran Hali

July 12, 2026
Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
Nishadi

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

June 14, 2026
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Nishadi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

June 14, 2026
Next Post
An Tsaurara Matakan Tsaro A Daura Gabanin Jana’izar Buhari A Gobe Talata

Sojoji Sun Hallaka Shugabannin ‘Yan Bindiga, Tare Da Kwato Makamai Da Kuɗi A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.