ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaƙin Iran: Bankin Duniya Ya Yi Gargadin Tashin Farashin Takin Zamani

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
Iran

Farashin man fetur da takin zamani a duniya suna kan hanyar tashin goron zabi a cikin shekaru hudu, yayin da yakin Iran ke ci gaba da girgiza kasuwannin kayan masarufi, in ji Bankin Duniya a cikin sabuwar rahoton hasashen kasuwannin kayan masarufi.

Babban Bankin Duniya, a ranar Talata ya gargadin cewa farashin makamashi na iya tashi da kashi 24 cikin dari a wannan shekara, wanda zai zama mafi girma tun lokacin da rikicin ya barke da mamayar Rasha a Ukraine.

Ana hasashen cewa farashin kaya gaba daya zai karu da kashi 16 cikin dari a shekarar 2026, wanda mafi yawanci abin ya samo asali ne daga tsananin karuwa a farashin makamashi da taki, da matakan mafi girma da aka taba samu a wasu muhimman tashoshi.

ADVERTISEMENT

A cewar rahoton, girgizan da ke fitowa daga rikicin Gabas ta Tsakiya ya fara yaduwa a cikin hanyoyin samar da kayayyaki na duniya, tare da manyan tasiri ga ci gaban tattalin arziki, samar da ayyuka da ci gaba, musamman a kasuwanni masu tasowa.

A tsakiyar wannan tashin hankali akwai mashigin Hormuz, wata muhimmin hanyar sufuri ta ruwa da ke daukar kusan kashi 35 cikin dari na kasuwancin mai na duniya ta teku. Hare-hare kan abubuwan more rayuwa na makamashi da cunkoson sufuri a wannan hanya sun haddasa abin da Babban Bankin Duniya ya bayyana a matsayin mafi girman girgizar samar da mai a tarihi, inda aka rage samar da mai a duniya da kusan ganga miliyan 10 a rana a lokaci mafi tsananin tashin hankali.

LABARAI MASU NASABA

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ko da yake farashin ya ragu kadan daga mafi girman matakan da aka samu kwanan nan, farashin danyan mai ya kasance sama da kashi 50 cikin dari fiye da matakan da aka samu a farkon shekara a tsakiyar Afrilu.

Bankin ya yi hasashen cewa dayan mai zai kai matsakaicin na dala 86 a kowace ganga a shekarar 2026, daga dala 69 a shekarar 2025, idan aka dauka cewa manyan tangarda sun ragu a cikin watanni masu zuwa kuma hanyoyin ruwa suna dawowa daidaito a hankali.

Babban masanin tattalin arziki na Bankin Duniya, Indermit Gill, ya yi gargadin cewa rikicin na bayyana a matakai daban-daban, tare da tasiri mai girma.

“Yakin na shafar tattalin arzikin duniya a cikin hanyoyi daban-daban, farko ta hanyar hauhawar farashin makamashi, sannan hauhawar farashin abinci, da kuma hauhawar farashin kayayyakin abinci, wanda zai kara kudin ruwa na bashi kuma ya sanya bashi ya fi tsada.

“Mutanen da suka fi talauci wadanda ke kashe mafi yawan kudaden shigarsu kan abinci da man fetur, za su fi shiga matsala, kamar yadda kasashe masu tasowa ke fama da matsalolin bashi. Duk wannan tunatarwa ce game da koma-bayan da yakin ya haddasa “, in ji shi.

Ana sa ran farashin taki zai tashi da kashi 31 cikin dari a shekarar 2026, wanda hakan zai faruwa ne saboda tashin farashin urea da kashi 60 cikin dari. Ana hasashen wannan zai sa samun taki a ya kai mafi rauni tun daga shekarar 2022, yana matsa lamba ga ribar manoma kuma yana barazanar ga samar da amfanin gona.

Rahoton ya yi gargadin cewa idan rikicin ya yi tsawo na iya kara tsananta rashin abinci a duniya, inda Shirin samar da abinci na duniya ke kiyasta cewa mutane miliyan 45 za su shiga cikin yunwa mai tsanani idan matsin lamba na samar da abinci ya ci gaba.

Babban Bankin Duniya ya kara cewa tashin farashin kayan masarufi zai karfafa matsin lamba na hauhawar farashin kayayyaki kuma ya raunana ci gaban tattalin arzikin duniya.

Hawan farashin kayayyaki a kasuwannin da ke tasowa yanzu an kiyasta zai kai kashi 5.1 a cikin dari a shekarar 2026, daga kashi 4.7 a cikin dari. Ana sa ran ci gaban tattalin arziki a wadannan kasuwanni zai ragu zuwa kashi 3.6 a cikin dari, wani sauyi ne zuwa kasa daga hasashen da aka yi a baya.

Mataimakin babban masanin tattalin arziki na Bankin Duniya, Ayhan Kose, ya yi kira ga masu tsara manufofi da su yi taka tsantsan wajen mayar da martani ga rikicin da ke faruwa.

“Tashin hankali da ya biyo baya cikin shekara goma ya rage tsarin kudi da ake da shi don mayar da martani kan rikicin samar da makamashi na tarihi da ake ciki yanzu.

“Dole ne gwamnatoci su ki yin amfani da manyan matakan tallafin kudi marasa ma’ana wadanda za su iya lalata kasuwanni kuma su rage ajiyar kudi na gwamnati. Maimakon haka, su mayar da hankali kan tallafi cikin sauri da na dan lokaci wanda aka tsara musamman ga gidajen da suka fi rauni,” in ji shi.

Iran
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

MASU ALAKA

Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Next Post
2027:Atiku Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Ya Janye Takararsa Ya Mara Wa Obi Da Kwankwaso Baya

2027:Atiku Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Ya Janye Takararsa Ya Mara Wa Obi Da Kwankwaso Baya

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.