ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

by Rabi'at Sidi Bala
4 months ago

Kamar kowane mako, a yau ma shafin na tafe da wata baƙuwar ta musamman, inda shafin yayi cozali da wata fitacciyar mawaƙiya wacce ake yi wa laƙabi da Gimbiyar Sha’iran Ƙasar Hausa, kana Jakadiyar Galadiman Kano wato,  FATIMA ILIYASU ABUBAKAR wacce aka fi sani da FATI UK. Inda ta bayyanawa masu karatu batutuwa da suka shafi sana’ar waƙar ta, tare da batutuwan da suka shafi rayuwarta.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki

ADVERTISEMENT

Sunana Fatima Iliyasu Abubakar, amma ana kira na da Fati UK

Ko za ki iya faɗawa masu karatu ɗan taƙaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

An haifeni a Kano, ƙaramar hukumar Tarauni, a wata unguwa da ake kira da Darmanawa, bayan asibitin Aminu Kano. Na yi ‘Primary School’ a Kano, na yi ‘secondary school’ a Kano. A lokacin da nake ‘Secondary school’ ne na samu wannan sunan na Fati UK.

Me ya ja hankalinki har ki ka fara waƙa?

To, Alhamdulillah duk wanda zai ce ya fara harkar waƙa ko waƙe, abin da yake jan hankalinshi na farko dai yana ji kamar yana da baiwar ta wannan abun. Na biyu kuma ƙaddarar shi tana cika abun, na uku kuma yana so ya yi.

Kamar wacce irin waƙa ki ke yi?

A lokacin da na fara waƙa, ni na fara waƙoƙi na yabon Annabi (S.a.w) ne. Asali ni rubuta ƙasida nake, daga baya kuma yanayi na idan za ka yabi Annabi (S.a.w), ba komai za ka kira shi da shi ba, sai na riƙa na jure, saboda idan zan yi yabo sai na kai wa malamai sun tantance min, daga ƙarshe kuma sai na koma mawaƙiya ta siyasa.

Za ki yi kamar shekara nawa kina waƙa?

A taƙaice dai zan iya samun kamar shekara 20 ina yi waƙa.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance a wancen lokacin?

Gaskiya inda na fara gwagwarmaya lokacin dana fara waƙoƙi kamar na siyasa, tunda daman na faɗa miki ‘da’ waƙoƙin yabo nake yi na Manzon Allah (S.a.w), dana koma waƙoƙin siyasa gaskiya ita tana cike da gwagwarmaya da ƙalubale. Shi kuwa waƙoƙin yabo, saboda Annabi (S.a.w) za a yi wa, ba a buƙatar komai, ana buƙatar dai son Annbi (S.a.w) da kalamai masu kyau, wanda za a  faɗa mishi, sannan idan mun yi muna iya kaiwa kasuwar Ƙofar Wambai a lokacin mu bawa masu yin harkar sidika (CD) da wannan kaset. Lokacin ana yin kaset sai mu basu su, su za su cigaba da tallata mana abubuwanmu. Yanzu kuwa idan muka yi waƙoƙin siyasa muna shan wahala, domin sai mun nemo wanda muka yi wa, ko kuma ya karɓa, da dai sauransu. Shi ne dalilin da ya sa za ki ga a wannan lokacin akwai gwagwarmaya gaskiya, saboda dole idan ka yi wa wani kana buƙatar ya ji ko ya gani.

Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu kina so ki fara waƙa, shin kin fuskanci wani ƙalubale daga gare su?

Lokacin da nake so na faɗawa iyayena batun waƙa, ba kai tsaye na samu goyon baya daga gare su ba, saboda a lokacin sun zata irin waƙar fim ce, amma daga ƙarshe dai iyayennawa suka fahimci cewar yadda dai ƙaddara ta zo, suka yi min addu’a.

Ya farkon fara waƙar ya kasance?

Farkon fara waƙa ban sha wahala ba, saboda ni na rubuta waƙata da kaina, sannan kuma na je ‘studio’, akwai wani ‘studio’ a lokacin a nan Zoo Road gurinsu wata Hannatu Sakatariyya, gurinsu Tijjani Kazaure, a nan na fara aiki.

Da wanne mawaƙi ko mawaƙiya ki ka fara yin waƙa?

A lokacin da na fara waƙa ban taɓa yi da wani mawaƙi ba, saboda ni da kaina nake rubuta waƙa ta, amma a yanzu da yake an samu cigaba ni ma idan zan yi waƙa ina ɗaukar mace kamar, Allah ya ƙara mata lafiya Hajiya Zuwaira Isma’il ta na yi min amshi.

Kin yi waƙoƙi sun kai kamar guda nawa?

To, yanzu dai gaskiya ba zan iya tantance ko sun kai nawa ba, Allah ka ɗai ya sani.

Ko za ki iya faɗowa masu karatu sunayen kaɗan daga cikin waƙoƙin da ki ka rera ko ki ka rubuta?

Akwai waƙar da na yi a wancan lokacin ta ‘Annabi sai ɗangatau’, sai kuma ta Almajiri, akwai waƙa ta ‘Na shiga Soyayya’, sai waƙoƙin siyasa na APC. Sannan idan aka shiga ‘page’ ɗina mai suna ‘Fati Uk Jakadiya’ a Tiktok da Audiomack.

A cikin waƙoƙin da ki ka rera ko ki ka rubuta wacce waƙa ce ta zamo bakandamiyyarki?

A yanzu waƙar da ta zamo bakandamiyata, ita ce wacce na yi a kan Almajiri, kuma idan Allah ya so ya yarda ba zan daina sonta ba. Sannan ina fatan Al’umma su yi amfani da abubuwan da na ce a cikin waƙar, saboda waƙa ce na yi ta akan faɗakarwa akan harkar Almajiri.

Me ya fi baki wahala wajen rera waƙa ko rubutawa?

Abin da yafi ba ni wahala a wancan lokacin wajen waƙa, ko rera ta, saboda rubuta waƙa baya bani wahala, gurin hawa da sauka, shi ne ya fi ba ni wahala.

Wane irin nasarori ki ka samu game da waƙa?

Na samu nasarori, dalilin waƙa an naɗa min sarautu guda uku a kaina, an yi min alkyabbar Hausawan Africa, an yi min Jakadiyar Galadiman Kano, an yi min Gimbiyar Sha’iran ƙasar Hausa. Ta dalilin waƙa na yi ziyarce-ziyarcen garuruwa da ƙasashe, na yi aikin hajji na sauke farali, na yi umara babu adadi, na yi abubuwa da yawa, dalilin waƙar nan na yi kasuwanci na.

Ko kina da ubangida a ɓangaren waƙa?

A’a, ba ni da ubangida a ɓangaren waƙa, amma ina da abokanen mu’amala, abokanan sana’a, wanda kuma sun zama kamar yayyena, Alhamdulillah suna ba ni shawarwari masu kyau, amma ba ni da tsayayye kai tsaye wanda zan kira, misali in ce miki wai mawaƙi ne shi ubangida na, Allah shi ne wanda yake tsaya min.

Mene ne burinki na gaba game da waƙa ko kuma mawaƙa?

Buri na na gaba dangane da harkar nan da nake yi, ina fatan ubangiji Allah ya sa mutane su fahimci me ma nake yi, kin san akwai abin da kake yi wasu ma basu gane me kake yi ba. Fata na Allah Ubangiji ya sa mutane su fahinci me nake yi. Kuma ina fatan Allah ya sa abin da muke yi ya zama alkhairi a cikin Al’umma, sannan kuma mu gama lafiya, shi ne babban burina.

Wacce shawara za ki bawa masu ƙoƙarin fara waƙa?

Shawarar da zan bawa masu ƙoƙarin fara waƙa, su yi haƙuri su dage su yi juriya, harkar nan akwai wahala, dan idan ba ka da haƙuri gaskiya ba za ka samu duk nasarorin da kake son samu a ciki ba, amma idan suka yi haƙuri inda basa zato ma za su je. Sannan kuma idan sun tashi shigowa kada su shigo da niyyar za su yi kuɗi ko arziƙi, su jira Allah.

Ko kina da wata shawara da za ki bawa sauran mawaƙa?

Shawarata ga sauran mawaƙa ƴan’uwana, dan Allah don Annabi mu haɗa kanmu, mu daina munafurci, mu zama ƴan’uwa tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya, dan Allah mu cire hassada mu so junanmu, arziƙi Allah ne mai bayarwa.

Me za ki ce da masoyanki, masu sauraron waƙoƙinki?

Masu saurarona ina godiya, ina mana fatan alkhairi  gabaɗaya, sannan a cigaba da taya mu da addu’a, sannan idan kun ga wajen da muka yi kuskure ku sanar da mu ta inda ya dace, kuma ta inda zamu fahimce ku. Ina ƙara godiya ubangiji Allah ya bar zumuncinmu da ku, Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi bakiɗaya. Allah ya zaunar mana da ƙasar mu da ma duniyar mu bakiɗaya lafiya.

Ko kina da waɗanda za ki gaisar?

Ina gaida iyayen gidana na siyasa kamar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ina gaishe da Distinguish Senator Barau Jibril Maliya. A cikin fim industry kuma ina gaishe da Hajiya Hauwa Editor da Daddy Hikima, da sauran jama’a musulmi. Allah ya sa mu gama lafiya.

Muna godiya ki huta lafiya.

Ni ma na gode, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ubangiji ya bar zumunci, ya sa mu gama lafiya.

Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

MASU ALAKA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
Nishadi

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

September 5, 2026
Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
Nishadi

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

August 29, 2026
Nishadi

Dalilan Da Suka Sa Ba Zan Iya Auren Ɗan Film Ba —Bilkisu Bishasha

August 23, 2026
Next Post
Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Nemi Tallafi Na Musamman Ga Alhazai Mata

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Nemi Tallafi Na Musamman Ga Alhazai Mata

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.