ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Gano Ƙasusuwan Dabba Mai Shekara Miliyan 100 A Nijar

by Rabi'u Ali Indabawa
8 months ago
Dabba

Wata tawagar masu bincike da ke aiki a yankin Sahara na Jamhuriyar Nijar sun sanar da gano ƙasusuwan dabbar Dinosaur wadda ta yi rayuwa sama da shekara miliyan 100 da suka shuɗe.

Wasu masu bincike 20 ne daga jami’ar jihar Chicago ƙarƙashin jagorancin Dr. Paul Sereno suka gano ƙasusuwan, kuma sun ce abu ne mai muhimmanci: zai zama ɗaya daga cikin hujjoji na ƙasusuwan wata dabba da aka gano a cikin sama da ƙarni.

  • Sojoji Sun Ƙwato Dabbobi 257 Da Aka Sace A Kano
  • Yunkurin Kasar Amurka Na “Neman Cin Nasara” Ya Sa Sauran Kasashe Yin Watsi Da Ita

A ƙarƙashin tsananin zafi da ake yi a yankin na Sahara, masu binciken suka gano sauran ƙasusuwan dabbar ta Dinosaur, wadda ake ɗauka a matsayin wata dabba ta daban a tsawon ƙarni.

ADVERTISEMENT

Tafiyar da masu binciken suka yi ƙarƙashin jagorancin masanin halittu Dr. Paul Sereno, na jami’ar Chicago, ya sake haifar da muhawara kan wanzuwar dabbar Dinosaur a Afirka kuma ya bayyana abin da ya daɗe a ɓoye a cikin Saharar.

 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano

Ana Zargin Jami’in Kwastam Da Kashe Kansa A Bauchi Saboda Damuwa

A tsakiyar Sahara da babu kowa…

Tawagar masu binciken sun shafe tsawon kwanaki suna yawo cikin Sahara ba tare da sun san inda za su nufa ba, ga ƙura da ƙishirwa – sai dai ba su sani ba a she akwai babban abin da za su gano a gaba.

A 2019, sun koma Jamhuriyar Nijar domin bincike a wani wuri da aka yi musu bayani a kai.

A lokacin ne wani abu da suka gamu da shi ya so kawo musu cikas.

“Wani mutun ne ya shiga sansaninmu. Ya yi kama da mutum-mutumin ƴan ƙabilar Tuareg. Yana ɗauke da adda a bayansa kuma yana zaune kusa da wata mota ƙirar Honda. Yana magan da yaruka daban-daban. Ya faɗa mana cewa zai kai mu wani wuri mai nisa,” a cewar Dr Paul.

Ba tare da wata-wata ba, tawagar ta aminta da shi. Sun yi ta keta sahara na tsawon kwana ɗaya da rabi har man ɗin su ya kusa ƙarewa. Daga ƙarshe, mutumin ya jagorance su zuwa wurin da ƙasusuwan suke a tsakiyar Sahara.

“Muna da sauran rabin sa’a kafin nan muka juya don tsira,” kamar yadda mai binciken ya bayyana. Masana kimiyyar sun yi aiki cikin matsi, inda suka yi ta kwan-gaba kwan-baya domin gano wasu ƙkasusuwa da kuma gane wurin da suke.

Bayan komawa ɗakin gwaje-gwaje, sun cika da mamaki: sun gano cewa ƙasusuwan dabbar Dinosaur ne wadda ta yi rayuwa sama da shekara miliyan 100 da suka shuɗe.

 

Gano sabon na’uin halittu

Lokacin da harkoki a duniya suka tsaya cik a 2019 sakamakon annobar Korona, hakan ya shafi binciken da Dr. Paul da tawagarsa ke yi inda suka dakata har na tsawon shekara biyu.

“Daga ƙarshe lokaci ya zo da muka sake haɗa kayanmu don komawa bincike,” in ji Paul. Ya ce a lokacin burinsu shi ne su koma don tattara waɗannan ƙasusuwa son ransu.

Ba su daɗe da komawa ba suka fara gano ƙasusuwan. “Cikin ƙasa da sa’a ɗaya da isar mu, wani ya zo yana gudu a gare ni yana cewa: ‘Ya kamata ku ga wannan abu!…kamar yadda Paul ya tuna.

Daga nan farin ciki ya fara rufe su. Sa’o’i biyu bayan haka, wani mai bincike ya gano wani ƙashi a cikin ƙasa. “Ya tambaye ni mene ne. Ƙashin dabbar ta Dinosaur ne. Mun yi matuƙar kaɗuwa a lokacin,”in ji shugaban masu binciken.

“Babu wanda ya taɓa ganin irin ƙashin,” in ji shi.

Masu binciken sun ɗauki hotunan ƙasusuwan ta kowane ɓangare domin kafa hujja kan bincikensu.

 

Tafiya zuwa cikin Sahara

Wannan sabon na’ui na dabbar Dinosaur da aka gano a saharar Nijar za ta taimaka wajen ƙara ilimi irin na’uin dabbobin da ake da su.

A cewar Paul, dabbar ta fi kama da wasu dabbobi maimakon waɗanda ke rayuwa a cikin ruwa. Tsawonsa ya kai mita 12u, kuma yana da damar afka wa cikin ruwa da kuma a fili,” in ji shi.

Dabbar ba ta iya ninƙaya sosai ba a cikin ruwa, ba kamar yadda wasu bincike suka nuna ba. “Ba ta iya yawo sosai a cikin ruwa ba kamar sauran dabbobi, tana bin koguna inda take cin kifaye a matsayin abincinta.

Binciken da aka gano a Nijar ɗin ya sha bamban da wanda aka yi a tarihi a arewacin Amurka.

Ga masu binciken, wannan farawa ne kaɗai. “Wannan shi ne na farko a cikin dogon bincike kan ɓacewar dabbar a duniya,” in ji shi.

 

Me ya sa binciken ke da muhimmanci?

Ga Dakta Paul Sereno, binciken ya wuce na ɓurbushin halittu kaɗai. Yana ba da labarin wata tafiyar binciken kimiyya mai muhimmanci, kuma ya buɗe sabon babi a tarihin dabbar Dinosaur.

Mai binciken ya bar Ingila tare da tawagarsa a cikin wata tsohuwar mota ƙirar Land Roɓers, inda suka nufi wani yanki mai haɗari a duniya. Sai dai balaguron da zai gano wani abu mai muhimmanci.

“Kamar yadda za ku iya gani a cikin hotunan da muka ɗauka, ina son motar sosai kuma na kasance ina lallaɓa ta tsawon shekara 30. Ita ma kamar Dinosaur suke,” ya faɗa cikin barkwanci. Motar ta kai mu zuwa cikin Sahara da kuma dawo da mu ba tare da an samu matsala ba

Sun fara tashi ne daga birnin Southampton da ke Ingila, inda suka isa saharar Nijar – wani wuri da yake ganin ba a yin bincike a cikinsa yadda ya kamata.

“A farkon rayuwata na gano wani abu ɗaya: yankin Sahara shi ne wuri ɗaya da ya rage da a ba yi bincike kan dabbobin Dinosaur da ke cikinsa ba,” in ji shi.

Yayin binciken, jami’an sun cire ƙasusuwa kusan tan 55 daga tsakiyar Sahara. Wanda kuma shi ne irinsa na farko a yankin da ba shi da ababen more rayuwa.

Amma ga Sereno, abu mafi mahimmanci shi ne. “Har yanzu akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi bincike a kai. Muna matakin farko na gano yadda dabbobin Dinosaur na Afirka suke,” ya faɗa cikin farin ciki.

Mu ciro muku daga BBC Hausa

Dabba
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Samar Da Kayayyakin Cikin Gida Na Da Muhimmanci Wajen Ƙarfafa Tattalin Arziki – Dangote
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dole Afirka Ta Samar Da Hanyoyin Magance Matsalolinta
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja

MASU ALAKA

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano
Al'ajabi

Yadda Ɗa Da Uwa Suka Ɗauki Hayar Wani Don Ya Kashe Mahaifinsa A Kano

August 14, 2026
Ana Zargin Jami’in Kwastam Da Kashe Kansa A Bauchi Saboda Damuwa
Al'ajabi

Ana Zargin Jami’in Kwastam Da Kashe Kansa A Bauchi Saboda Damuwa

June 9, 2026
EFCC Ta Cafke Lauyan Bogi Da Mallakar Hatimin Kungiyar Lauyoyi Ta Nijeriya Na Jabu A Legas
Al'ajabi

EFCC Ta Cafke Lauyan Bogi Da Mallakar Hatimin Kungiyar Lauyoyi Ta Nijeriya Na Jabu A Legas

April 21, 2026
Next Post
Yaƙin Iran: Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Matakan Tsaro A Yankin Gabas

Wane Ne Alireza Aarafi, Shugaban Kwamitin Zaɓen Sabon Ayatollah A Iran?

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.