ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wane Ne Alireza Aarafi, Shugaban Kwamitin Zaɓen Sabon Ayatollah A Iran?

by Abubakar Sulaiman
6 months ago
Alireza

Hukumomin Iran sun sanar da Alireza Aarafi, wanda wakili ne a Majalisar Magabatan ƙasar, domin ya jagoranci majalisar tafiyar da mulkin riƙon-ƙwarya na ƙasar.

Bayan tabbatar da rasuwar Ali Khamenei a ranar 29 ga watan Fabarairu, za a kafa majalisar riƙon ƙwarya ta ƙasar, bisa dogaro da sashe na 111 na kundin tsarin mulkin ƙasar, wadda za ta ƙunshi shugaban ƙasa da babban alƙalin alƙalai da kuma wani wakili daga Majalisar Magabatan ƙasar.

  • Yaƙin Iran: Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Matakan Tsaro A Yankin Gabas
  • Dalilin Da Ya Sa Muka Kai Wa Iran Hari — Donald Trump 

Bayan sanar da Mista Aarafi a matsayin mamban wannan majalisa, ana sa ran mutanen uku ne za su karɓi ragamar tafiyar da lamurran ƙasar har sai majalisar masana ta ƙasar ta sanar da sabon jagoran addinin ƙasar.

ADVERTISEMENT

Sashe na 111 na kundin tsarin mulki ya bayyana cewa, daga lokacin rasuwar jagoran addini zuwa lokacin da Majalisar Masana za ta sanar da sabon Jagora, Majalisar wasu mutane guda uku ne za su tafiyar da ayyukan ofishin Jagora.

Wakilan wannan majalisa su ne Shugaban ƙasa, da Babban alƙalin ƙasa da kuma wakilin Majalisar Magabata wanda Majalisar lura da buƙatun gaggawa ke zaɓa.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Sai dai, wannan Majalisa ta Mutane uku ba ta da cikakken iko, kuma tana buƙatar amincewar kashi uku cikin huɗu na Majalisar lura da buƙatun gaggawa kafin aiwatar da abubuwa kamar haka:

Kasancewar an kashe babban kwamandan rundunar juyin juya halin ƙasar, da shugaban rundunar tsaro ta ƙasar da kuma da dama daga cikin manyan hafsoshin sojin ƙasar, ana sa ran majalisar shugabancin ta riƙon ƙwarya za ta riƙa zartar da manufofi ne ta hanyar samun amincewar kashi uku bisa huɗu na wakilan majalisar ƙasar.

Wasu kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen ƙasar, ciki har da jaridar New York Times cewa an samar da “mataki huɗu na magadan jagororin” ƙasar, sai dai kafofin yaɗa labarai da ke kusa da gwamnatin ƙasar sun bayyana lamarin a matsayin “farfagandar yaƙi.”

Wane ne Alireza Aarafi?

Bayanai daga kafofin yaɗa labaran Iran sun ce an haifi Alireza Aarafi ne a shekara ta 1955 a birnin Meybod da ke lardin Yazd.

Mahaifinsa Mohammad Ebrahim Aarafi shahararren malami ne a lokacin rayuwarsa, wanda ya yi adawa da jagorancin sarki Pahlaɓi, kuma yana da alaƙa ta ƙut da ƙut da malaman da ke kusa da Ruhollah Khomeini.

Mahaifiyarsa ‘ya ce ga Sheikh Kazem Malek Afzal Ardakani.

Alireza Aarafi ya yi karatunsa na farko-farko ne, kamar ilimin Ƙur’ani da adabi da harkar shari’a a wurin mahaifinsa da kuma wasu malamai.

Ya koma birnin Ƙom a shekarar 1960, sannan bayan kammala karatun elemantare ya fara karatun koyon maluntan addini a shekarar 1977.

Bayan kammala matakin farko, sai ya fara tafiya wurin manyan malaman shi’a daban-daban ya yi karatun shari’a, ciki har da Morteza Haeri, da Mohammad Fazel Lankarani, da Hossein Ɓahid Khorasani, da Jaɓad Tabrizi, da Ali Meshkini, da kuma Hassan Hassanzadeh Amoli, sannan ya yi karatun falsafa a wurin Mohammad Taƙi Misbah Yazdi.

Ya kuma yi karatun harkokin addini a tsangayoyi da jami’o’i kamar Allameh Tabataba’i da Tarbiat Modarres.

Alireza Aarafi ya kasance cikin harkokin siyasa tun yana matashi, kuma ya bi sahun mahaifinsa wajen adawa da gwamnatin Pahlaɓi.

An kama shi tare da ɗaure shi a gidan yari tun yana da shekara 16.

A shekarar 1979, an kafa wata ƙungiyar mai lura da ɗalibai waɗanda ba ƴan asalin ƙasar Iran ba a cibiyar karatun addini ta Ƙom.

Wadda daga baya ƙungiyar ta zama ‘Cibiyar Kimiyyar Musulunci ta Duniya’, inda ta koma ƙarƙashin kulawar jagoran addini na Iran.

A shekara ta 2002 ne aka naɗa Alireza Aarafi a matsayin shugaban cibiyar bisa amincewar Ayatollah Ali Khamenei.

Yana daga cikin iyayen jami’ar Kimiyyar Ƙur’ani da ilimi.

Aarafi ya kasance limamin Juma’a na Meybod tun daga shekara ta 1992, kuma an naɗa shi limamin juma’a na Ƙom a 1994.

Shi mamba ne a ƙungiyar malaman cibiyar horar da malaman addini ta Ƙom.

Mista Aarafi ya yi takarar shiga majalisar ƙwararru ta Iran a zaɓen shekara ta 2015 domin wakiltar mazaɓar Tehran, sai dai bai samu nasara ba.

Ya sake gwada yin takara a zaɓukan tsakiyar zango, inda ya samu nasara, domin wakiltar Tehran.

Ya samu shiga majalisar ne karon farko daga Tehran a zaɓen da aka yi a watan Maris na 2023, inda ya samu ƙuri’a 888,618.

A ranar 14 ga watan Yulin 2019 aka naɗa Mista Aarafi zuwa Majalisar Magabata bisa amincewar Ali Khamenei.

Daga Majalisar Masana zuwa jagoran riƙo

A shekarun baya-bayan nan ne mutane suka fara sanin Alireza Aarafi, a baya idan za a ambace shi a labarai, akan kira shi da laƙabin “Hujjat al-Islam”, amma a yanzu za a riƙa masa laƙabi da “Ayatollah”.

Alireza na cikin mutanen da Ali Khamenei ya amince da su kuma yana cikin na kusa da shi. Wannan karɓuwa da ya samu a wurin jagoran addinin ta sanya darajarsa ta riƙa ɗagawa, har ya kai ga inda ake ambaton sunansa a matsayin wanda zai iya gadon Ali Khamenei.

Alireza
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Rundunar Ƴansandan Nijeriya Ta Naɗa Sabon Kakaki

Rundunar Ƴansandan Nijeriya Ta Naɗa Sabon Kakaki

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.