ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda El-Rufai Ya Ƙwace Filin Gowon A Abuja — Bishop Kukah

by Sadiq
4 months ago

Babban Limamin Cocin Katolika na Diocese da ke Sakkwato, Matthew Hassan Kukah, ya bayyana cewa tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nasir El-Rufai, ya taɓa ƙwace filin tsohon Shugaban Mulkin Soja na Nijeriya, Yakubu Gowon, da ke Abuja.

Kukah ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin bitar littafin tarihin rayuwar Gowon mai suna “My Life of Duty and Allegiance” a Abuja.

A cewarsa, bayan an yi wa Gowon juyin mulki a 1975 kuma ya dawo daga gudun hijira daga Birtaniya, bai mallaki ko da fili ɗaya a Abuja ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Babangida, tare da wasu manyan hafsoshin soja ne suka taimaka masa wajen samun filin.

Kukah ya ce Gowon ya fara gina gida a filin kafin daga bisani aka ƙwace shi a lokacin da El-Rufai yake ministan Abuja.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Sai dai ya bayyana cewa tsohon Janar, Theophilus Danjuma, da wasu manyan mutane sun shiga tsakani har aka mayar wa Gowon filin nasa.

Limamin ya kuma bayyana irin wahalhalun da Gowon da iyalansa suka sha yayin gudun hijira a Birtaniya.

Ya ce Gowon ya sha fama wajen samun aiki har ma da buɗe asusun banki, yayin da matarsa Victoria Gowon ke tallafa wa iyalin ta hanyar ɗinkin zanin gado da yin matasai tana sayarwa.

Kukah ya ƙara da cewa wani ma’aikacin gida da aka tura domin taimaka wa iyalin daga Nijeriya, daga baya an gano cewa leƙen asiri yake yi a kansu, amma bai samu wani abin kai rahoto ba.

Ya bayyana littafin tarihin Gowon mai kusan shafuka 900 a matsayin muhimmin tarihi da ya ƙunshi bayanai kan juyin mulki, gudun hijira, shugabanci da kuma rayuwar tsohon shugaban ƙasar.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 12, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Lalong Da Sauran ‘Yan Takarar APC Sun Lashe Zaben Fidda Gwani Na Majalisar Dokoki A Filato

Lalong Da Sauran 'Yan Takarar APC Sun Lashe Zaben Fidda Gwani Na Majalisar Dokoki A Filato

LABARAI MASU NASABA

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.