Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Kotun ta bayar da belin ne kan kuɗi Naira miliyan 100 tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa da makamancin wannan adadi.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta gindaya tsauraran sharuɗa kan belin, inda ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance mazaunin Maitama ko Asokoro a Abuja, sannan ya ajiye asalin takardar mallakar gida (Certificate of Occupancy) na wata kadara a gaban kotu.
Kotun ta kuma umurci wanda zai tsaya masa da ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na 17 ko sama da haka, tare da gabatar da shaidar albashi na aƙalla watanni uku.
Bugu da ƙari, dole ne wanda zai tsaya masa ya gabatar da takardar shaidar hali ta kuɗi, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar beli, sannan ya bayar da hoton fasfo na baya-bayan nan tare da wasiƙar tabbatarwa daga ma’aikatarsa da takardar biyan haraji ta watanni shida da suka gabata.
Kotun ta kuma umurci El-Rufai da ya miƙa dukkan ingantattun fasfo na ƙasashen waje da yake da su.
Mai shari’a Abdulmalik ta kuma umurce shi da ya riƙa zuwa hedikwatar DSS duk ranar Juma’a ta ƙarshe a kowane wata da ƙarfe 10 na safe domin sanya hannu a rajistar halarta har sai an kammala shari’ar.
Kotun ta yi gargaɗin cewa duk wani karya waɗannan sharuɗa zai janyo soke belin kai tsaye.
Jaridar Daily Trust ta rawaito yadda aka gurfanar da tsohon gwamnan bisa zargin saƙa na’urar sauraren wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.
An kawo tsohon gwamnan harabar kotun da misalin ƙarfe 8:55 na safe ranar Litinin tare da jami’an tsaron farin kaya masu tsaurin fuska, waɗanda suka killace harabar kotun.
An hana ƴan jarida, ma’aikata da sauran masu amfani da harabar kotun shiga nan take bayan kawo tsohon gwamnan, lamarin da ya haddasa ɗan zanga-zanga na ɗan lokaci.
Jagoran zanga-zangar, ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce kotu wuri ne na jama’a wanda bai kamata a hana duk wani ɗan Nijeriya mai sha’awar sauraren shari’a shiga ba.
Da yake magana da Daily Trust ba tare da bayyana sunansa ba, wani ma’aikacin ICPC ya bayyana cewa jami’an DSS sun isa ofishin hukumar tun ƙarfe 7:00 na safe domin ɗaukar wanda ake tuhuma zuwa kotu.
“Eh, shari’ar da ake yi yanzu ba tamu ba ce. Su jami’an DSS sun zo ɗaukar sa da misalin ƙarfe 7:00 na safe domin gurfanar da shi a kotu,” in ji majiyar.















Discussion about this post