Aƙalla mutane 10 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari garin Tofa da ke Ƙaramar Hukumar Rabah ta Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka shiga garin tare da buɗe wa mutane wuta.
Sun kuma yi garkuwa da mutane da dama.
Majiyoyi a yankin sun ce ’yan bindigar sun tafi da mutane tsakanin 38 zuwa 40, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a tabbatar da ainihin adadin waɗanda aka sace ba.
Haka kuma, ’yan bindigar sun sace dabbobi masu yawa a garin tare da kwashe wasu kayayyaki.
Harin ya sake jawo damuwa kan matsalar tsaro a wasu sassan Ƙaramar Hukumar Rabah, musamman yadda ’yan bindiga ke iya shiga cikin al’umma, kai hare-hare sannan su fice da mutanen da suka yi garkuwa da su da kuma dabbobi.
Mazauna yankin sun kuma tambayi yadda ’yan bindigar suka samu damar kai harin, kashe mutane da yin garkuwa da wasu ba tare da jami’an tsaro sun daƙile su ba.
Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar harin lokacin da aka tuntube shi.
Sai dai ya ce rundunar za ta fitar da cikakken bayani bayan kammala tattara rahoton lamarin.
Ba a samu damar tabbatar da ainihin adadin mutanen da aka kashe, jikkata ko sace ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.














