ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Majalisar Wakilai 50 Da Suka Rasa Tikitin Takara A Zaɓen Fid Da Gwani Na APC

by Yusuf Shuaibu
4 months ago

Zangon farko na zaɓen 2027, ya nuna cewa ƴan majalisar wakilai guda 50 na majalisa ta 10 ba za su kasance a zauren majalisa ta 11 ba.

A lokacin buga wannan rahoton, aƙalla ƴan majalisar wakilai 48 na jam’iyyar APC sun sha kaye a zaɓen fid da gwani da aka gudanar a faɗin ƙasar a ƙarshen mako. Yayin da ƴan majalisa biyu na Bayelsa ba su shiga takara ba, saboda suna neman manyan muƙaman siyasa.

Ana sa ran adadin zai ƙaru, saboda har yanzu APC ba ta fitar da cikakken sakamakon zaɓukan fid da gwani ba, kuma sauran jam’iyyun adawa kamar jam’iyyar NDC da PDP da LP da ADC da APGA da sauransu ba su gudanar da zaɓukan fitar da gwani ba.

ADVERTISEMENT

Sai dai kuma, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da mataimakinsa, Benjamin Kalu sun jagoranci ƴan majalisar dokoki na APC da suka samu tikitin dawowa.

Manyan ƴan majalisar APC da suka rasa tikiti a zaɓen fitar da gwani sun haɗa da Nicholas Mutu (Bomadi/Patani, Jihar Delta, wanda ya kasance a majalisa tun 1999) da Mike Etaba (Obubra/Etung, Jihar Kuros Ribas), wanda ya rasa tikitin komawa majalisa karo na huɗu.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Haka kuma shi ma, Farfesa Julius Ihonɓbere, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, yana cikin ƴan majalisar da ba za su dawo ba. Shi ma ɗan majaisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Adamu Gagdi, ya rasa tikiti na neman wa’adi na uku.

A Jihar Borno kuwa, Usman Zannah (Gubio/Kaga/Magumeri) da Betara Aliyu (Biu/Shani/Kwaya Kusar/Bayo) da Kadiri Rahis (wakilin Maiduguri da kewaye) da Satomi Ahmed (Jere) da Bukar Talba (Marte/Monguno/Nganzai) da Ahmed Jaha (Gwoza/Chibok/Damboa), duk sun gaza masan tikiti.

A Jihar Bayelsa, mambobi biyu da suka riƙe muƙamansu sun ci gaba da samun tikitin jam’iyya a mazaɓar tarayya ta Yenagoa/Kolokuma-Opukuma da ɗan majalisar Oforji Oboku, ya samu tikitin jam’iyyar. Haka ma a mazaɓar Ijaw ta kudu, Injiniya Rodney Ambaiowei, wanda shi ne ɗan majalisa mai ci, shi ma ya yi nasara.

A mazaɓar Ogbia, Jude Reɗ Ogbuku ya lashe tikitin ɗan majalisar wakilai, yayin da Matema Obodor na PDP, wanda ke riƙe da muƙamin ɗan majalisar, ya ki canja sheƙa tare da Gwamna Douye Diri zuwa APC.

A mazaɓar Nembe/Brass, Jonathan Robinson Obuebite ya sami tikitin APC. Ita ma ƴar majalisa, Marie Ebikake, ita ma ta zaɓi ta ci gaba da zama a PDP domin tsayawa takarar majalisar dattawa a mazaɓar Bayelsa ta yamma.

Yayin da a Jihar Kuros Ribas, ƴan majalisar wakilai guda biyar daga cikin takwas sun sha kashi.

Daga cikin waɗanda suka gaza samun tikiti akwai ƴan majalisa masu wa’adi da dama a majalisar tarayya da suka haɗa da mamba mai wa’adi uku, Mike Etaba, wanda ke wakiltar Obubra/Etung da mamba mai wa’adi biyu, Aleɗ Egbona, wanda ke wakiltar Abi/Yakurr, wanda ya sauya sheƙa zuwa PDP kafin wa’adin ƙarshe da mamba mai wa’adi ɗaya, Godwin Offiono, wanda ke wakiltar mazaɓar Ogoja/Yala da mamba mai wa’adi ɗaya, Emil Inyang, wanda ke wakiltar mazaɓar Akamkpa/Biase da mamba mai wa’adi ɗaya, Bassey Akiba, wanda ke wakiltar Odukpani/ Calabar.

A Akwa Ibom, ko da yake APC ba ta fitar da sakamako a hukumance ba, rahotanni sun nuna cewa shi kaɗai Okpolupum Etteh, wanda yake wakiltar mazaɓar Eket/Esit Eket/Ibeno, ya sha kashi.

A Jihar Ribas, waɗanda suka yi rashin nasara sun haɗa da John Azubuike Opara da Anderson Allison Igbiki, Awaji Imombek Abiante, da Boma Goodhead (a halin yanzu suna wakiltar mazaɓun Andoni/Opobo da Asari-Toru a majalisar wakilai).

A Jihar Delta, waɗanda suka sha kaye a yanzu su ne Nicholas Mutu, Bomadi/Patani da Ngozi Lawrence Okolie, wacce ta sha kaye a zaɓen mazaɓar tarayya ta Aniocha/Oshimili.

A Jihar Ekiti, ƴan majalisa uku da ke kan karagar mulki sun faɗi yayin zaɓen fid da gwanin na jam’iyya APC.

A mazaɓar Ekiti ta tsakiya, Oladapo Karounwi, ya samu ƙuri’u 6,573, wanda yake kan kujerar, Abiodun Omoleye, ya samu ƙuri’u 2,096. A mazaɓar Ekiti ta kudu, Okoro Toyin Zaccheaus ya samu ƙuri’u 9,798, wanda ya doke mai riƙe da muƙamin, Rufus Adeni Ojuawo, wanda ya samu ƙuri’u 1,842. A mazaɓar Ekiti ta arewa II, Ibrahim Olanrewaju ya samu ƙuri’u 6,856 wanda ya doke mai riƙe da muƙamin, wanda ya samu ƙuri’u 2,102.

A Jihar Ogun, biyar daga cikin ƴan majalisa tara da ke kan muƙamansu sun kasa samun tikitin komawa majalisar wakilai. Daga cikin waɗanda suka sha kaye a akwai Ishaƙ Akinlade na mazaɓar Yewa ta arewa /Ipokia da Ibrahim Isiaka, wanda ke wakiltar mazaɓar Ifo/Ewekoro da Tunji Akinosi mai wakiltar mazaɓar Ado-Odo/Ota da Femi Ogunbanwo da ke wakiltar mazaɓar Ijebu Ode/Ijebu North East/Odogbolu.

A Jihar Ondo, akwai tashin hankali a cikin APC bayan kwamitin zaɓen fitar da gwani mai mambobi bakwai ya kasa bayyana sakamakon zaɓen fid da gwani na majalisar wakilai na ranar Asabar da ta gabata.

A Jihar Legas, wani ɗɗan takarar da ke neman kujerar majalisar wakilai a mazaɓar Epe, Mista Ademola Amure, ya yi kira da a soke zaɓen fid da gwani na APC da aka yi ranar Asabar a mazaɓar, yana kwatanta zaɓen a matsayin mara tsari da ke cike da manyan kura-kurai da kuma maguɗi.

Haka nan, a mazaɓar Iwo, Mista Ademola Habeeb ya samu tikiti ta hayar masalaha, yayin da Mista Asalu Daɓid ya samu tikiti ta hayar masalaha a jam’iyyar APC a mazaɓar Ede.

Dakta Obawale Adebisi ya samu tikiti ta hayar masalaha a mazaɓar Ila, yayin da ɗan majalisa mai ci Mista Taofeek Ajilesoro na mazaɓar Ife shi ma ya samu titiki ta hanyar masalaha.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Taron Ministocin Cinikayya Na APEC Ya Yi Kira Da A Samar Da Matsaya Daya Ta Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya

Taron Ministocin Cinikayya Na APEC Ya Yi Kira Da A Samar Da Matsaya Daya Ta Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.