ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 30, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansanda Sun Kama Mutane Tara Kan Rikicin Kasuwar Gujungu A Jigawa

by Sulaiman
3 months ago
Gujungu

Rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa ta kama mutane tara da ake zargi da hannu a wasu laifuka daban-daban bisa kai hari kan ofishin ‘yansanda, da kuma rikicin da ya barke a Kasuwar Gujungu da ke Ƙaramar Hukumar Taura.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, SP Shi’isu Adam, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, kamen na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi na tabbatar da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.

ADVERTISEMENT

Da yake bayani kan rikicin Kasuwar Gujungu, Adam ya ce a ranar 26 ga Yuli, 2026, rundunar ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu a tashin hankalin da ya auku a kasuwar.

Ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan ɗan wani saɓani tsakanin wani soja da wani matashi mai suna Biniya Alhaji Ibrahim, mai shekaru 25, ɗan Ƙaramar Hukumar Miga, a cikin kasuwar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

Kakakin ‘yansandan ya ce rikicin ya rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin sojan ya caka wa Biniya wuka, lamarin da ya yi sanadin raunukan da daga bisani suka yi ajalinsa bayan likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Ya ƙara da cewa bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun matasa sun yi amfani da rikicin wajen kai hari kan ofishin ‘yansanda, inda suka harba kibiyoyi ga jami’an tsaro, tare da ƙona shaguna biyu a cikin kasuwar.

Adam ya ce binciken da aka gudanar bisa bayanan sirri ya kai ga kama mutum biyu da ake zargi da hannu a wannan rikici.

Hakazalika, ya bayyana cewa rundunar ta kuma kama wasu mutum shida da ake zargi da kai hari kan jami’an ‘yan banga.

Sannan ya kara da cewa, ana cigaba da bincike don ganin an kamo duk wanda ke da hannu kan wannan rikici.

Gujungu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    An Kammala Cikakken Zama Na JKS Inda Aka Amince Da Kudurin Ci Gaba Da Bin Cikakken Tsarin Shugabancin Kai Na Jam’iyyar
  • Sulaiman
    An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK
  • Sulaiman
    Ci Gaban Sarrafa Kayayyakin Laturoni Da Na Manyan Fasahohi Ya Ingiza Ribar Da Masanaantun Kasar Sin Suka Samu
  • Sulaiman
    Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

MASU ALAKA

Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto
Manyan Labarai

Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

October 30, 2026
Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace
Manyan Labarai

Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

October 30, 2026
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa

October 30, 2026
Next Post
Alkalin Babbar Kotun Kebbi Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci, Bayan Shafe Mako Guda A Hannun ‘Yan Bindiga

Iyalan Alƙalin Kebbi Sun Ce Sun Biya Naira Miliyan 50 Domin Samun 'Yancinsa

LABARAI MASU NASABA

INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo

INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo

October 30, 2026
Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

October 30, 2026
Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

Mutanen Borno Sun Roƙi Tinubu Da Zulum Su Ceto Ɗalibai 78 Da Aka Sace

October 30, 2026
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa

Ƴan Bindiga Sun Sace Malamar Firamare, Sun Nemi Miliyan 50 Kuɗin Fansa

October 30, 2026
Lakurawa Sun Kashe Insfektan Ƴansanda Da Mutane 11 A Kebbi

Lakurawa Sun Kashe Insfektan Ƴansanda Da Mutane 11 A Kebbi

October 30, 2026
NSCDC Ta Cafke Sojan Gona A Kano

NSCDC Ta Cafke Sojan Gona A Kano

October 30, 2026
Kwamitin Kolin JKS Ya Kira Taron Manema Labarai Game Da Zaman Da Ya Yi

Kwamitin Kolin JKS Ya Kira Taron Manema Labarai Game Da Zaman Da Ya Yi

October 30, 2026
2027: Gwamnonin Kano Da Kaduna Sun Yi Gargaɗi Kan Kalaman Ƙiyayya, Labaran Ƙarya

2027: Gwamnonin Kano Da Kaduna Sun Yi Gargaɗi Kan Kalaman Ƙiyayya, Labaran Ƙarya

October 30, 2026
Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

October 29, 2026
Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

October 29, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.