ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yerima Shettima Ya Gudanar Da Aikin Duba Lafiya Kyauta Ga Mutane 500 A Kaduna

by Shehu Yahaya and Sulaiman
8 months ago
Shettima

A kokarinsa na inganta lafiyar al’umma, Ambasada Yerima Shettima, daya daga cikin manyan masu neman kujerar sanata a Kaduna ta tsakiya, ya shirya wani gagarumin aikin duba lafiya kyauta a cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke Unguwar Shaba cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa, inda aka yi wa kimanin mutane 500 aiki.

Ambasada Yerima ya bayyana cewa wannan shiri ya samo asali ne daga akidarsa wadda ta ta’allaka kan cewa rayuwa hidima ce ga Bil’adama. Ya ce wannan aiki wata hanya ce ta ba da gudummawa ga al’umma, alkawarin da ya ce zai ci gaba da karfafa shi a nan gaba.

  • ICPC Za Ta Ci Gaba Da Binciken Tsohon Shugaban NMDPRA Duk Da Janye Ƙarar Dangote
  • Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Yi Jigilarsu a Kasar Sin Ya Zarce Biliyan 4.5 A Shekarar 2025

Ya tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da kuma fadada ayyukan kiwon lafiyar idan har ya samu damar zama sanata. Ya ce a halin yanzu yana gudanar da wannan tallafi ne a matsayinsa na mutum daya, amma idan ya samu madafun iko zai samu karin dama da karfi wajen tabbatar da cewa agajin lafiya ya kai ga kowa.

ADVERTISEMENT

Shirin aikin duba lafiyar zai ci gaba a wasu yankuna, inda tawagar za ta wuce karamar hukumar Chikun a karshen mako mai zuwa.

Aikin duba lafiyar ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman matsalolin lafiya da al’ummar yankin ke fuskanta, ciki har da zazzabin cizon sauro da cutar gyambon ciki da gwaje-gwaje da bayar da magunguna da kuma shirin tsarkake ciki ga yara.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Yerima ya bayyana cewa tuntuba kai tsaye da al’umma na taimaka masa wajen mai da hankali kan bukatunsu da kuma yanke shawara cikin gaggawa domin inganta lafiyar jama’a. Ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su hada kai wajen irin wadannan ayyukan jin kai.

A nasu jawaban, shugabannin Unguwar Shaba sun bayyana shirin a matsayin babban aikin alheri da ni’ima ga mazauna yankin. Sun yi kira ga sauran masu hali da su mara baya ga irin wadannan ayyuka tare da rokon al’umma da su ba da hadin kai da addu’o’i domin cimma burin Yerima na zama sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya.

Shettima
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Shettima
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Birtaniya Za Ta Mayar Wa Nijeriya Dala Miliyan $9.5 Na Kudaden Da Aka Sace

Birtaniya Za Ta Mayar Wa Nijeriya Dala Miliyan $9.5 Na Kudaden Da Aka Sace

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.