ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Birtaniya Za Ta Mayar Wa Nijeriya Dala Miliyan $9.5 Na Kudaden Da Aka Sace

by Abubakar Sulaiman
8 months ago
Nijeriya

Gwamnatin Birtaniya ta kammala shirye-shiryen mayar wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Dala miliyan 9.5 na kuɗaɗen da aka gano cewa an same su ne ta hanyar cin hanci da rashawa. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Ofishin Jakadancin Birtaniya a Abuja ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa babban Lauyan Jersey, Mark Temple KC, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) a watan Disambar 2025, domin sauƙaƙa dawo da kuɗaɗen zuwa Nijeriya. An ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen tallafa wa wani muhimmin aikin gine-ginen more rayuwa a ƙasar.

  • Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa
  • Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Tun a ranar 29 ga Nuwamba, 2023, Lauyan ya nemi kotun Royal Court ta Jersey ta kwace kuɗaɗen da ke cikin wani asusun banki, bisa dokar kwace kadarorin da aka samu ta haramtacciyar hanya. A ranar 12 ga Janairu, 2024, kotun ta amince da kwace kuɗaɗen bayan ta tabbatar da cewa kuɗaɗen sakamakon wata badakalar cin hanci ce, inda ’yan kwangila suka karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin amfanin manyan jami’an Nijeriya da abokan hulɗarsu.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ce wannan yarjejeniya ta biyo bayan wasu yarjejeniyoyi biyu da aka kulla a baya tsakanin birnin Jersey da Nijeriya, waɗanda suka haifar da dawo da sama da dala miliyan 300. An yi amfani da kuɗaɗen wajen manyan ayyukan tituna guda uku: hanyar Lagos–Ibadan, gadar Niger ta biyu, da kuma aikin hanyar Abuja–Kano. A halin yanzu, an kammala ayyukan Lagos–Ibadan da Gadar Niger ta biyu, yayin da sabbin kuɗaɗen za su taimaka wajen kammala aikin hanyar Abuja–Kano mai tsawon kilomita 375.

Da yake tsokaci kan batun, Mark Temple KC ya ce dawo da kuɗaɗen na nuna ƙarfin dokokin kwace kadarori wajen yaƙi da cin hanci da rashawa. Shi ma Ministan Shari’a na Nijeriya, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce wannan nasara ta tabbatar da ingancin haɗin gwuiwar Nijeriya da ƙasashen waje, tare da ba da tabbacin cewa za a yi amfani da kuɗaɗen da aka dawo da su yadda ya dace bisa yarjejeniyar da aka cimma.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Nijeriya
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Katsina Ta Sanya Motocin Daukar Marasa Lafiya 15 A Manyan Hanyoyi

Gwamnatin Katsina Ta Sanya Motocin Daukar Marasa Lafiya 15 A Manyan Hanyoyi

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.