ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Tuhumi Bukola Saraki Da Abdulfatai Ahmed Da Laifin Kisa

by Abubakar Sulaiman
5 months ago

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatai Ahmed, za su gurfana a gaban kotu a ranar 4 ga Yuni, 2026 domin fuskantar sabbin tuhume-tuhume guda 20 da suka haɗa da kisan kai, da haɗa baki da sauran laifuffuka dangane da fashin da aka yi a Offa a shekarar 2018.

An shigar da karar ne a gaban Mai Shari’a Haleemah Salman ta Babbar Kotun Jihar Kwara, inda kuma aka hada da Yusuf Abdulwahab da Alabi Olalekan a matsayin waɗanda ake kara.

Florence-Morenike-Saraki-and-Abubakar-Bukola-Saraki

ADVERTISEMENT

Gidauniyar Saraki Ta Kammala Shirin Rabon Abincin Buda-baki

An ce ƙarar, mai lamba LWS/114C/26, an shigar da ita ne a ranar 9 ga Afrilu, 2026 daga hannun Babban Lauyan Jihar Kwara, Ibrahim Sulyman (SAN), kuma ana sa ran za a miƙa wa waɗanda ake ƙara takardun tuhuma a ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026. Wannan sabuwar shari’ar ta zuwa ne bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa manyan waɗanda suka aikata fashin, ciki har da Ayo Akinnibosun.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Masu gabatar da ƙara sun zargi waɗanda ake ƙara da haɗa baki wajen ɗaukar nauyi da kuma ba da makamai ga wasu da ake alaƙanta su da harin na Afrilu 2018 a Offa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da tayar da hankalin jama’a. An ce Akinnibosun, wanda aka riga aka yankewa hukunci, ya bayyana kansa a matsayin mai aikata kisan kai a ƙarƙashin wata alaƙa ta siyasa da ake dangantawa da waɗanda ake kara.

Haka kuma, ana zargin cewa ya karɓi bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu daga Yusuf Abdulwahab kafin wani taron siyasa, tare da karbar mota kirar Toyota Lexus mai dauke da lambar Saraki da kuma kudi da aka kira “tallafin siyasa”. Ana kuma cewa wasu daga cikin waɗanda aka yankewa hukunci sun raka Saraki yayin ziyarar jaje da ya kai Offa bayan harin, tare da gano wasu motoci da kayayyaki daga ofisoshin gwamnati a jihar Kwara da aka yi amfani da su a matsayin hujja.

Sai dai Saraki ya sha musanta hannu a lamarin, yana mai cewa zarge-zargen siyasa ce kawai da aka ƙirƙira domin ɓata masa suna. Shi ma Abdulfatai Ahmed ya ƙaryata zargin, yana mai cewa ba su da tushe. Ana sa ran shari’ar za ta jawo hankalin ƙasa baki ɗaya, yayin da ake shirin fara sauraron ƙarar a ranar 4 ga Yuni, 2026, kuma ana sa ran Saraki da jam’iyyar PDP a jihar Kwara za su mayar da martani nan ba da jimawa ba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
An Tsinci Gawar Ministan Sadarwa Na Burundi A Cikin Motarsa

An Tsinci Gawar Ministan Sadarwa Na Burundi A Cikin Motarsa

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.