ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Maraba Da Hukuncin Kotu Kan Dakatar Da Jadawalin INEC

by Abubakar Sulaiman
2 months ago
Inec

Jam’iyyun siyasa sun yi maraba da hukuncin babban kotun tarayya wanda ta soke wasu sassa na jadawalin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na zaɓen 2027, sun bayyana hukuncin a matsayin babban sauƙi bayan watanni da suka safe suna ƙorafe-ƙorafe kan lokutan hukumar zaɓe.

Hukuncin na iya sauya yadda ake lissafin siyasa kafin zaɓen 2027, bayan ƙorafe-ƙorafen jam’iyyun siyasa kan cewa jadawalin INEC ya yi kaɗan wajen samun damar gudanar da shirye-shirye na ayyukansu yadda ya kamata.

“Akwai buƙatar a yi a hankali kan muhimman tsarin dimokuraɗiyya. Ina da tabbacin cewa dukkan jam’iyyun siyasa sun yi farin ciki da hukuncin. Hukuncin zai taimaka wa jam’iyyun wajen ƙara tsara kansu yadda ya kamata,” mai magana da yawun kwamitin gudanarwa na ƙasa na PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki da Ini Ememobong.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake magana kan lamarin, sakataren yaɗa labarai na kwamitin gudanarwa na PDP ɓangaren tsakin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da Mohammed Haruna Jungudo, ya ce a ɓangarensu har yanzu suna sake yin Nazari dangane da hukuncin kotun.

Ya ce, “Zan sake dawowa gare ku. Muna nazarin hukuncin a halin yanzu,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Kazalika, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar PRP, Muhammed Bello Ishaƙ, ya ce hukuncin ya bayyana ƙarfin ikon da jam’iyyun siyasa suke da shi da INEC ta karɓe daga garesu.

Ya ce, “A bayyana yake cewa, hukuncin ya sake ingantawa da ci gaban dimokuraɗiyyarmu ta hanyar mayar da ƙarfin ikon jam’iyyun siyasa wanda INEC ta karɓa da kanta.

“Ya faɗaɗa damar yanke shawara a cikin jam’iyyun siyasa kuma ya cire tsarin da ba shi da kyau a cikin ayyukanmu.”

“INEC na iya ɗaukaka ƙara, ko da yake muna fatan cewa manyan masu ruwa da tsaki za su shiga tsakani don dakatar da irin wannan mataki,” in ji shi.

Ishaƙ ya kuma iƙirarin cewa jam’iyyar APC na iya zama ɗaya daga cikin manyan masu amfani da hukuncin duba da rikice-rikicen cikin gida da take fama da shi wajen fitar da ƴan takara.

Ya ce, “Jam’iyyar mai mulki ta APC na iya zama babbar wacce ta fi amfana daga wannan hukunci, bisa la’akari da halin da take ciki a halin yanzu, wajen magance damuwar da ke ƙara tasowa daga ƙoƙarinta na zaɓan ƴan takaranta.

“Wasu jam’iyyun siyasa ma za su kasance cikin tunanin yadda wannan hukunci zai iya taimaka musu wajen faɗaɗa mambobinsu da inganta shugabanninsu,” in ji shi.

Inec
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Inec
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Firaministan Guinea Ya Yabi Kasar Sin Bisa Shawarwarin Da Ta Gabatar

Firaministan Guinea Ya Yabi Kasar Sin Bisa Shawarwarin Da Ta Gabatar

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.