ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Nijeriya Miliyan 34.7 Na Fuskantar Barazanar Yunwa Sakamakon Rikice-rikice Da Tsadar Kayayyaki —PWC

by Rabi'u Ali Indabawa
8 months ago
Nijeriya

Rahoton PwC na ‘Nigeria Economic Outlook 2026’ mai taken “Juya daidaiton tattalin arziki zuwa ci gaba mai dorewa,” ya bayyana cewa Nijeriya na fuskantar barazanar tsananin matsalar wadatar abinci a shekarar 2026, inda ake hasashen cewa mutum har miliyan 34.7 za su shiga cikin matsanancin ƙarancin abinci.

Rahoton ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa tare da haɗin gwiwar manufofi ba, matsalolin tsaro da ke ci gaba, hauhawar kuɗin samarwa, da sauyin yanayi za su ci gaba da raunana samarwa, rarrabawa da samun abinci a faɗin ƙasar.

  • Kalaman Takaichi Masu Matukar Ban-Takaici
  • Gwamnati Ta Yaƙi Talauci, Rashin Tsaro,  ’Yancin Jama’a Don A Hana Aukuwar Juyin Mulki A Nijeriya – Falana

PwC ta bayyana cewa, “Rikice-rikice, tsadar kayan noma, da girgizar sauyin yanayi na sa ran za su tura ƴan Najeriya har miliyan 34.7 cikin matsanancin ƙarancin abinci a shekarar 2026.” Rahoton ya nuna Arewa a matsayin yankin da abin ya fi shafa, inda rikice-rikice suka tilasta dubban manoma barin gonakinsu tare da daƙile muhimman ayyukan noma kamar shuka da girbi.

ADVERTISEMENT

Tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2025 kaɗai, kusan mutane 34,000 aka raba da muhallansu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, lamarin da ya rage ƙarfin ma’aikatan noma matuƙa.

Tsadar kayan shigar noma na ƙara tsananta matsalar. Matsakaicin farashin takin NPK a faɗin ƙasa ya tashi da kashi 19.5 cikin 100 a shekarar 2025, inda ya kai kusan Naira 52,000 kan buhun kilo 50. Rahoton ya ce, “farashin samar da kayayyaki ya tashi sosai, inda kuɗin noman masara ya ƙaru da kashi 29.2 cikin 100, yayin da na waken soya ya ƙaru da kashi 36.8 cikin 100.”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Ƙarancin samun tallafin kuɗi ya ƙara taƙaita amfani da kayan noma, inda rahoton ya nuna cewa kashi 62 cikin 100 ne kawai na manoma suka yi amfani da kayan shigar noma a shekarar 2025, ƙasa da kashi 81 cikin 100 da aka samu a shekarar 2024.

Wannan ya haifar da raguwar amfani da kayan shigar noma da kashi 24 cikin 100, tare da raguwar filayen da ake noma da kashi 8 cikin 100.

Sauyin yanayin ruwan sama da rashin tabbas, gami da fari na dogon lokacin a shekarar 2025, sun kuma taimaka wajen samun girbi ƙasa da matsakaici a wasu yankuna, lamarin da ya rage yawan abincin da ake samu gaba ɗaya, tare da ƙara barazanar rashin tsaro a shekarar 2026.

Sakamakon binciken PwC ya yi daidai da gargaɗin manoma da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Rahotanni sun nuna cewa manoma a Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma na tunanin daina noma sakamakon tsadar kuɗin da ake samarwa, matsalar tsaro, da kuma asarar amfanin gona bayan girbi.

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) ma ta yi hasashen cewa kimanin ƴan Nijeriya miliyan 34.7 za su iya fuskantar matsanancin ƙarancin abinci a lokacin daminar yunwa tsakanin watan Yuni zuwa Agusta na shekarar 2026, bisa ga nazarin Cadre Harmonisé na watan Oktoban 2025.

Hauhawar farashin abinci, wanda matsalar tsaro, matsin lambar kuɗin ƙasa, da tsadar makamashi da kayan shigar noma ke haddasawa, tuni ya rage damar samun muhimman kayan aikin noma, musamman ga ƙananan manoma.

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da sauran abokan ci gaba sun sha yin kira da a ɗauki matakan gaggawa domin inganta tsaro, ƙara juriya ga sauyin yanayi, da daidaita samar da abinci.

PwC ta jaddada cewa tinkarar matsalar tsaro, rage tsadar kayan shigar noma, faɗaɗa damar samun kuɗaɗen tallafin noma, da ƙarfafa dabarun daidaitawa da sauyin yanayi za su zama muhimmai matuƙa wajen hana hasashen matsalar ƙarancin abinci rikiɗewa zuwa cikakken bala’in jin ƙai a shekarar 2026.

“Dole ne a ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare samar da abinci, kare hanyoyin samun abin rayuwa, da tabbatar da cewa miliyoyin ƴan Nijeriya ba za su fuskanci yunwa a shekarar gobe ba,” in ji rahoton.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Shin Alonso Ya Cancanci Kora A Real Madrid?

Yadda Kuɗin Hidimar Makarantar Yara Ke Ci Gaba Da Ci Wa Iyaye Tuwo A Ƙwarya

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci