ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Bukatar Zaben Shugabanni Na Gari

by Sulaiman and Ibrahim Bala
4 months ago
Shugabanni

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

Jama’a barkanmu da sake kasancewa tare da ku a wannan fili namu mai albarka, filin da ke kawo muku batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a kwarya.

A wannan lokacin ina so na yi magana a kan wasu abubuwa guda biyu wadanda suke ci mana tuwo a kwarya a wannan rayuwar tamu.

ADVERTISEMENT

Zan yi magana a kan shugabanci, ba mu dauke shi wani abin a zo a gani ba. Alal hakikanin gaskiya Allah subhnahu wa ta’ala ya ce a kangin kaina ma na haramta zalinci. Wato, shugabanni suna zaluntar mabiyansu.

Shugaba dai gabadaya idan aka yi magana akan shugabanci to, ka sani cewar lamari ne ubangiji ya ara maka, kuma ranar gobe alkiyama kowane shugaba zai je da ankwa, adalcin da yayi shi ne zai warware.

LABARAI MASU NASABA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

Shugaba shi ne madubi na tafiyar al’umma bakidaya, idan yayi adalci sai a ga al’ummar ta tafi daidai, kuma shi ma ya ga daidai. Tunda an kai kan wata gaba da lamurarrukan rayuwar ma kashi tamanin sai shugabanci na tafiya zai iya tafiyuwa yadda ya kamata.

Idanuwa suna rufewa wanda ba mu san lokacin da za mu mutu ba, amma da yawa shugabanni Allah yana ara musu rana, yana kuma basu dama.

To, muna fata kuma muna jan kunne ku sani Allah zai tsayar da ku, duk dukiyar da ka tara ko dai tsufa ya riske ka, ko kuma ka mutu ka bar wannan dukiya, kuma baka san me za a yi da ita ba. Daidai da naira daya duk yawan dukiyarka, in ka fi dan karuna arziki, ranar gobe alkiyama sai ka yi bayani “Ya akai ka same ta?, kuma da me ka sarrafata?”.

Sannan kowacce gaba ta jikin dan’adam sai ya fadi abubuwan da ya yi. To, idan ka samu dama mu yi adalci, mu kuma rike amana. Manzon Allah (s.a.w) ya ce, abu guda uku idan ka kauce su a cikin hadisi to, ka zama munafuki. Ka yi zance ka yo karya, a baka amana ka ci, a kuma amince maka ka yi yaudara.

Kuma sannan in na zo ga magoya baya su ma, su sani abubuwan da muke yi ba daidai bane, domin zagin shugabanni fasikanci ne, Annabi (s.a.w) ya fada.

Babu azzalumin shugaba irin wanda zai rika zalintar wadanda yake shugabanci. Haka kuma babu jahili mabiyi, wanda mabiyin da zai rika zagin shubanni. Wa ya fada maka zagi ake yi? ba zagi ake yi ba, saboda idan kana zagin shugabanninka sai ya zamar maka masifa. Ita masifa ko a’ina ba kaunarta ake yi ba, addu’a ake yi ko Allah ya gyara shi ko kuma Allah ya kawo maka madadinsa da zai maka adalci.

Ina fatan za mu yi amfani da koyi da Annabi (s.a.w), mu yi addu’a ga shugabanninmu ya kawo mana wadanda za su cece mu, ya basu dama su cece mu ko Allah ya shirye su. Amma idan muka ci gaba da zaginsu sai su zama lalatattu kuma a kanmu abun zai kare.

Allah ya sa mu dace.

Shugabanni
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Shugabanni
Ibrahim Bala
+ posts Bio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala-2/
    Mene Ne Hukuncin Yin Jam’i Na Biyu A Masallacin Da Ke Da Limami Ratibi 
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala-2/
    Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

MASU ALAKA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
Marurun Zuciya

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

June 20, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Marurun Zuciya

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

May 23, 2026
marayu
Marurun Zuciya

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

May 17, 2026
Next Post
Shugabanni

Sharrin Da Ke Tattare Da Jifan Iyali Da Munanan Kalamai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.