ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Fatanmu Mayar Da Nijeriya Wuri Mafi Alheri Ga Kowa – Kwankwaso

by Sulaiman
4 months ago
Kwankwaso

Jigo a jam’iyyar NDC, kuma jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna yiwuwar haɗa tikitin takara da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a babban zaɓen shekarar 2027.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata hira kai tsaye da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV.

Ya ce manufofin magoya bayan Obi, da aka fi sani da ‘Obidients’, da kuma tafiyar Kwankwasiyya suna da kamanceceniya, wanda hakan ya sa ake ƙoƙarin haɗa kai.

ADVERTISEMENT

Da aka tambaye shi ko ‘yan Nijeriya za su iya sa ran tikitin haɗin gwiwa tsakanin Obi da Kwankwaso a ƙarƙashin NDC a 2027, tsohon ɗan takarar shugaban kasar a jam’iyyar NNPP ya ce:“Na yarda haka ne, kuma idan aka duba jam’iyyar, ina ganin haka ne tunaninsu.

“A kwanakin baya mun yi ƙoƙarin fahimtar abin da Obidients ke son yi a siyasa da kuma abin da suke son yi wa Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

“Lokacin da muka kwatanta tafiyar su da ta mu, sai muka fahimci cewa manufofin kusan iri ɗaya ne.

“A taƙaice, muna son mu mayar da Nijeriya wuri mafi alheri ga kowa, musamman matasa maza da mata da suke buƙatar kulawar gwamnati. Ba sa buƙatar abubuwa masu yawa, sai dai muhimman abubuwa kamar ilimi, aikin yi, tsaro da makamantansu.

“Waɗannan su ne matsalolin da ake fuskanta yanzu, kuma mun yarda cewa ƙwararru za su duba tsarinmu da nasu tsarin domin kwatantawa.

“Mun yi nisa sosai a tattaunawar, kuma bisa ga abin da muka tattauna da su, na yi imani muna da buri guda ɗaya ne — ganin Nijeriya ta zama ƙasa mafi alheri ga kowa,” in ji shi.

Kwankwaso
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a
  • Sulaiman
    Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina
  • Sulaiman
    Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

MASU ALAKA

An Ci TikTok Tarar Fam Miliyan £12.7 Kan Karya Dokar Kananan Yara A Burtaniya
Manyan Labarai

Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a

September 17, 2026
Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC
Manyan Labarai

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

September 17, 2026
Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku
Manyan Labarai

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

September 17, 2026
Next Post
Neja

Jihar Neja Ta Kammala Jigilar Alhazai 2,281 Zuwa Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

An Ci TikTok Tarar Fam Miliyan £12.7 Kan Karya Dokar Kananan Yara A Burtaniya

Hisbah Ta Cika Hannu Da Fitaccen Ɗan TikTok A Kano Kan Bidiyoyin Rashin Da’a

September 17, 2026
Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

September 17, 2026
Kawayen amarya

’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina

September 17, 2026
Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

September 17, 2026
Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

September 16, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

September 16, 2026
Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

September 16, 2026
Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas

Sojoji Sun Hallaka Wani Jagoran ’Yan Ta’adda A Katsina

September 16, 2026
Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

September 16, 2026
Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.