ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Hadakar ‘Yan Adawa Ta Rushe Yayin Da Tikitin Takarar Shugaban Kasa Ya Raba Kan Shugabannin ADC

by Sulaiman and Yusuf Shuaibu
4 months ago
ADC

Gabanin zaben 2027, fatan samun hadin gwiwar ‘yan adawa don yakar jam’iyyar mai mulki ta APC, na fuskantar babbar matsala bayan da manyan shugabanni suka bar hadiakar saboda sabbanin kan tikitin shugaban kasa.

Rahotanni sun nuna cewa hadakar wanda aka kafa karkashin jam’iyyar ADC, mai nufin kalubalantar neman sake zaben Shugaba Bola Tinubu karo na biyu.

A watan Maris na shekara ta 2025, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi da tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu suka yi hadaka da shirin kifar da Shugaba Tinubu a shekarar 2027.

ADVERTISEMENT

A ranar 3 ga Yuli, shugabannin jam’iyyun adawa, ciki har da Peter Obi da sauran manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa da jam’iyya mai mulki, suka karbi ADC a matsayin jam’iyyar adawa don fafatawa a zaben 2027.

Tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami sun kasance cikin manyan ‘yan jam’iyyar hadaka tare da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da masu goyon bayansa suka cikin wannan jam’iyya a ranar 20 ga Maris, 2026 bayan sun bar NNPP.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Sai dai kuma mambobin hadakar sun samu rarrabuwar kai kwanan nan bayan da rikice-rikicen shugabanci da suka dabaibaye jam’iyyar da kuma neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyya.

An ruwaito cewa tattaunawa domin tikitin takarar shugaban kasa kawai ta hadu da cikas tsakanin magoya bayan Atiku da Obi, tare da sauran ‘yan takara da ke fafatawa don samun tikitin takarar shugabancin kasa.

A ranar 2 ga Yuli, Ralph Nwosu, wanda ya kafa jam’iyyar kuma tsohon shugabanta, ya sanar da yin murabus na jagorantar kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, wanda ya bude hanya ga tsarin shugabanci na rikon kwarya da Dabid Mark ke jagoranta.

A wasu watanni bayan da Dabid Mark ya karbi jagorancin jam’iyyar, wani tsagin jam’iyyar da Nafiu Bala, daya daga cikin mataimakan shugaban jam’iyyar ke jagoranta ya kalubalanci tsarin.

Bala ya bayyana cewa bai taba yin murabus daga mukaminsa ba, ya yi ikirarin cewa shi ya kamata ya maye gurbin shugaban jam’iyyar bayan murabus din tsohon shugasaban jam’iyyar, kamar yadda aka bayyana a cikin kundin tsarin jam’iyyar.

Bala ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar ADC tare da shigar da kara a kotu kan kalubalantar shugabancin Mark. A ranar 2 ga Satumba, 2025, Bala ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da shugabancin Mark.

Haka kuma ya nemi umarnin kotu don hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi amfani da sunan Mark a matsayin shugaban jam’iyyar tare da tilasta INEC ta saka sunansa a matsayin shugaban jam’iyyar na wucin gadi.

Har ila yau, ya shigar da bukatun kotu don dakatar da jam’iyyar yin duk wani taro har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin kotu.

An fara sauraron shari’ar a ranar 4 ga Satumba, 2025, kuma alkalin kotun, Emeka Nwite, ya umarci a bai wadanda ake kara ciki har da INEC, sanar da su dalilin da ya sa ake karar.

Ba tare da gamsuwa da hukuncin wucin gadi ba, Dabid Mark ya shigar da koke yana kalubalantar hurumin babban kotun tarayya kan ci gaba da sauraron karar Bala.

Duk da haka, a ranar 12 ga Maris, 2026, kotun daukaka kara ta ki karbar karar Mark gaba daya, ta ce ba ta da hurumin zartar da hukunci ba tare da sanin tushen al’amari ba, wanda ya sa al’amarin ya tafi kotun koli.

Hukumar zabe, daga baya ta dakatar da bangaren Dabid Mark daga jagorancin jam’iyyar.

A ranar 30 ga Afrilu, kotun koli ta mayar da shugabancin Dabid Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC.

Duk da cewa kotun kolin ta soke umarnin kotun daukaka kara wanda ta umarci bangarorin su ci gaba da rike matsayinsu, ta tsaya ba tare da fitar da hukunci na karshe kan rikicin shugabanci da ke kasa ba.

A cikin hukuncin kotun koli mai alkalai biyar karkashin jagorancin Alkali Mohammed Lawal Garba, ta yanke hukunci cewa kotun daukaka kara ta yi aiki fiye da karfin ikonta ta hanyar bayar da umarni bayan ta ki amincewa da karar da aka shigar a gabanta.

Kotun ta amince kawai da wani bangare na daukakar karar Mark kuma ta umarci dukkan bangarorin su koma kotun daukaka kara don ci gaba da sauraron karar.

Masana sun ci gaba da cewa daya daga cikin manyan dalilan rarrabuwar shugabannin ‘yan adawa shi ne, rashin ikon jam’iyyar na tsara shugabancinta bisa yankuna.

Yayin da Atiku da magoya bayansa ke shirin samun tikitin shugaban kasa na ADC daga shugabannin jam’iyya, Obi yana ganin cewa shi ya fi cancanta, yana tabbatar da cewa har yanzu yankin kudanci ya kamata ya fitar da shugaban kasa.

Bangaren Obi ya zargi Atiku da shirin bai wa shugabannin jam’iyya kudi don ba shi damar samun tikiti.

Sakamakon lamarin ya haifar da rashin jituwa, wanda ya sa Obi da Kwankwaso a ranar Lahadi suka dauki matakin komawa jam’iyyar NDC suka bar ADC.

ADC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
ADC
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 32 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Katsina

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 32 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.