ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Rashin Hadin Kan Atiku Da Obi Da Kwankwaso Na Iya Taimaka Wa Tazarcen Tinubu

by Yusuf Shuaibu
4 months ago
Atiku

Lokacin da tsohon Sanata Dino Melaye ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa Peter Obi zai iya aiki ne kawai a karan kansa, nan take ya zama daya daga cikin batutuwan siyasa mafi shahara a makon nan.

Kusan makonni biyu kacal bayan da shugabannin ‘yan adawa sun taru a Ibadan suka yi alkawarin yin hadaka kafin zaben 2027, hadakan ‘yan adawan Nijeriya tuni ya fada cikin rikici.

“Peter Obi ya tusa kansa cikin yanayi mai wuya. Zai iya aiki ne kawai a karan kansa, wanda hakan kuma ya saba wa ka’idar siyasar da muke ciki a yanzu,” Melaye ya rubuta.

ADVERTISEMENT

Rahotonni sun bayyana cewa kwanakin bayan Obi da Rabiu Musa Kwankwaso suka bar jam’iyyar ADC, zuwa NDC, wanda hakan ya jefa sabon rashin tabbas cikin kokarin gina hadaka na manyan jam’iyyun adawa domin yakar APC.

Ga yawancin ‘yan Nijeriya, abubuwan da suka faru sun tuna musu zaben shugaban kasa na 2023, lokacin da rabuwar kawunan ‘yan adawa ta taimaka wajen bude kofar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu duk da fushin mutane game da wahalhalun tattalin arziki da rashin tsaro.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Tsoron da yawancin magoya bayan ‘yan adawa ke yi na cewa tarihi na iya maimaita kansa.

A lokacin zaben 2023, Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da kuri’u kimanin miliyan 8.79, kusan kashi 37 cikin dari na jimillar kuri’un da aka jefa.

Yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya samu kuri’u kusan miliyan 6.98, yayin da Obi ya samu kusan miliyan 6.10. Kwankwaso ya samu kuri’u miliyan 1.5, mafi yawansu daga Kano da wasu sassan yankunan arewa maso yamma. Idan aka hada su, manyan ‘yan takarar adawa sun sami kuri’u fiye da na Tinubu.

Amma tsarin zaben Nijeriya ya ba dan takarar da ke da karfi tsosai wani gwarin gwiwa fiye a kasa da samun hadin kai a fadin yankuna da ke kasar nan. APC kuma ta amfana daga karancin masu jefa kuri’a da kuma rarrabuwar kawunan ‘yan adawa.

Wannan sakamakon ya haifar da rashin jin dadi a tsakanin magoya bayan ‘yan adawa, da dama daga cikinsu har yanzu suna da yakinin cewa hadakar ‘yan adawa zai iya canza sakamakon.

Taron ‘yan adawa na Ibadan da aka gudanar a ranar 25 ga Afrilu, 2026, an yi shi ne don magance wannan matsalar.

‘Yan siyasa daga kungiyoyi daban-daban na hamayya sun hallara don nuna hadin kai da tattauna yiwuwar cimma yarjejeniya kafin zaben 2027.

Haka kuma taron ya samar da wani babban alkawari na yin aiki tare wajen yin adawa da APC da kuma jure abin da masu jawabi suka bayyana a matsayin kokarin mai da Nijeriya tsarin jam’iyya guda.

A wani bangaren kuma, taron ya haifar da kwarin gwiwar cewa ‘yan adawar Nijeriya sun dauki darasi daga kurakuran da suka tabka a shekarar 2023.

A ranar 3 ga Mayu, hadin gwiwar ‘yan adawa ya shiga cikin matsala bayan Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso suka shiga jam’iyyar NDC a hukumance, wanda ya zama sun fice daga ADC, wanda ya rushe tattaunawar Ibadan. Wannan lamari ya sauya lissafin ‘yan adawa kafin shekarar 2027.

Maimakon samun hadin gwiwar adawa guda daya mai karfi, yanayin siyasa yanzu yana bayyana cewa an samu rarrabuwar kawuna, bangaren Atiku na ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar ADC, Obi da Kwankwaso sun hada kai a cikin jam’iyyar NDC, sauran ‘yan siyasa har yanzu suna nazarin yiwuwar hadin kai.

Fadar shugaban kasa za ta yi amfani da rikicin ‘yan adawa don samun nasara.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya zargi Obi da kauce wa fafatawar siyasa masu wuya da kuma canza jam’iyya a duk lokacin da zai fuskanci zaben fitar da gwani.

Rahotanni sun nuna cewa rarrabuwar ‘yan adawa zai iya sake bai wa Tinubu daman sake lashe zabe a 2027.

Lissafin APC yana da sauki, rarrabuwar kawunan ‘yan adawa na rage yiwuwar kalubale mai zafi da zai iya barazanar ga jam’iyyar mai mulki.

A halin yanzu, jam’iyyun adawa suna ta kokarin gamsar da ‘yan Nijeriya cewa sun samar musu ta wata zabi da zai yaki APC kai tsaye.

Mafi yawancin ‘yan Nijeriya da ke fuskantar kunci na tattalin arziki, harkikin siyasa da ake yi a kai a kai yana kara jin kamar ba ya da alaka da abubuwan da ake fuskanta a rayuwar yau da kullum. Don haka, fushin jama’a ba a kan jam’iyyar mai mulki kawai ba ne, amma yana karuwa ga masu fafutukar samun iko ko ta halin kaka.

A yanzu haka, rabewar ‘yan adawa za ta taimaka wa Tinubu. A kowanne mako ana gudanar da sauya sheku, rikice-rikicen cikin gida, da hare-haren jama’a lokaci ne da ake amfani da shi wajen gina kamfen din siyasa.

Atiku
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Atiku

Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Karfafa Bincike A Fannin Kiwon Dabbobi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.